19/02/2026
SANARWAR MANEMA LABARAI
KABARA COMMUNITY SECURITY, EDUCATION & DEVELOPMENT ASSOCIATION (KCSEDA)
Kungiyar Kabara Community Security, Education & Development Association (KCSEDA)
ta gabatar da korafi a hukumance ga
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano,
Cp Ibrahim bakuri
tana mai kira da a gaggauta gudanar da cikakken bincike kan kisan daya daga cikin ’yan kwamitin Kabara tare da jikkata wasu mutane biyu,
sak**akon rikicin fadan daba da ya barke tsakanin Kabara da Magashi.
Tun bayan faruwar wannan lamari, kungiyar ta dauki alkawarin bibiyar lamarin domin tabbatar da an gano wadanda s**a aikata wannan danyen aiki
tare da gurfanar da su a gaban kuliya domin a yi musu hukunci bisa doka.
A ranar 18 ga Fabrairu, 2026, kungiyar ta shigar da korafi a hukumance ta hannun lauyan kungiyar kuma lauya daga ƙungiyar kare hakkin dan Adam ta
Global Community for Human Rights Network,
tare da shugaban kungiyar, Kabara community da sakataren kungiyar da pro
inda s**a mika takardar karar ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano domin neman adalci da kare hakkin wadanda abin ya shafa.
KIRAN GAGGAWA GA HUKUMOMIN TSARO DA GWAMNATIN JIHAR KANO
Kungiyar na kira cikin gaggawa ga
hukumomin tsaro da gwamnatin Jihar Kano da su fito da gaskiya
ba tare da jinkiri ba kan waɗan da ake zargi sun shiga Kabara,
s**a aikata kisan gilla ga yara marasa laifi — yara da ba su aikata wani laifi ba.
Wadanda aka kashe sun hada da:
Halifa Churi — ɗan kwamitin Kabara, mara laifi.
Ɗan Malam — malamin makarantar allo, mai tarbiyyar yara.
Akilu — matashi mai neman halal domin rayuwarsa.
Wadannan ba ’yan daba ba ne, ba masu tada fitina ba ne — ’ya’yan talakawa ne masu neman na kansu da gina makomarsu.
Kungiyar ta jaddada cewa ba za a lamunci amfani da kakin gwamnati wajen cutar da al’umma ba, tare da bayyana wannan lamari a matsayin zalunci da kisan gilla, ba aikin tsaro ba.
BUKATUN KUNGIYAR
Kungiyar na neman:
A fito da cikakkiyar gaskiya kan abin da ya faru
A gano wadanda s**a aikata ake zargi da aikata laifin
A hukunta su bisa tanadin doka
A ba iyalan wadanda aka kashe adalci da diyya
Rayuwar talaka ba abin wulakanci ba ce.
Adalci dole ne ya tabbata.
An fitar da wannan sanarwa ne daga:
Kabara Community Security, Education & Development Association (KCSEDA)