27/12/2025
Ko dai Æmurka ta Sayi Arewa?
Wani ɗan Majalisar Amurka, Riley Moore, ya fito ya ce wai harin da Amurka ta kai a Najeriya ya hana kai farmaki kan Kiristoci a lokacin Kirsimeti. A lokaci guda kuma, shugaban Najeriya ya tabbatar da cewa an kai harin ne da amincewar gwamnatinsa.
Abubuwan Lura:
• Meye haɗin Sokoto garin Musulmi da Kirismeti, ko dai suna son su isar da saƙon cewa Musulmin Arewa na kæshë Kiristocin Najeriya?
• Meye haɗin ƙaramar hukumar Jabo a Sokoto da yaƙar ta'addanci, ko dai suna nufin nan ne cibiyar ’yan ta'addan Najeriya?
• Meye haɗin ISIS da ta'addancin da ake fama da shi a Arewa, ko dai bandits (su Bello Turji) suke nema aka samu kuskure?
Idan da gaske manufar ita ce yakar ’yan ta’adda, me ya sa ba a mayar da hankali kan sanannun wuraren da suke fakewa ba, kamar: Dajin Sambisa, Dajin Rugu, Dajin Kamuku, Dajin Kuyan Bana (Sububu), Dajin Birnin Gwari, Dajin Mandara, da Dazuzzukan Lake Chad Basin?
Wannan makirci ne ake shirya wa Arewa, kuma ba ’yan ta'adda suke yaƙa ba; Musulmi suke yaƙa, domin inda suke hari ba cibiyar ta'addanci bane, kuma ba cibiyar Kiristoci bane b***e a ce suna ƙoƙarin kare su, daman suna da agenda ta ganin bayan Musulunci, kuma da yardar Allah ba za su yi nasara ba.
Shugabannin cikin gida da na waje kowa da akwai manufar da yake son cimma wa, kuma har ’yan uwansu Kiristoci ba kaunarsu suke ba; kawai suna wasa da hankalinsu ne, daga ƙarshe wawayen dake jin daɗi da Kirista ma ji daɗinsu; kowa zai gane kurensa in dai ba a gyara ba.
Shin kun taɓa ganin ƙasar da Æmurkæ ta shiga da nufin gyara s**a zauna lafiya?