16/06/2026
Rahama Sidi Ali fitacciyar jarumar masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood ce wadda aka haifa a ranar 22 ga Yuli, 1989 a Jihar Kaduna, Najeriya.
Ta taso a Kaduna inda ta yi karatun firamare da sakandare kafin ta ci gaba da karatu a Kaduna Polytechnic.
Ta fara harkar fim tun tana matashiya, inda fim ɗinta na farko ya kasance Far Mace, sannan ta fito a wasu fina-finai da shirye-shiryen talabijin da s**a haɗa da Matar Abokina, Kwana Casa'in, da sauran ayyukan Kannywood.
Sai dai ta samu gagarumar ɗaukaka ne a shekarar 2019 bayan ta taka rawar Umma (Mahaifiyar Maryam) a cikin shahararren shirin talabijin na Labarina
Wanda ya sanya ta zama sananniya a faɗin Arewacin Najeriya saboda kwarewarta wajen nuna halayen uwa mai tausayi, tarbiyya da hikima duk da cewa shekarunta ba su kai na irin rawar da take takawa ba.
A hirarraki daban-daban da ta yi, Rahama ta bayyana cewa mutane da yawa sun riƙa ɗaukarta a matsayin tsohuwa saboda yadda take fitowa a matsayin uwa a cikin Labarina.
Dangane da rayuwarta ta kashin kai, ta bayyana cewa har yanzu ba ta yi aure ba, amma tana fatan yin aure a nan gaba, sannan ta taɓa cewa ba za ta iya auren ɗan fim ba saboda tana da tsananin kishi.
Baya ga nasarar da ta samu a fina-finai, Rahama Sidi Ali ta shahara saboda sauƙin kai, mutunta masoyanta da kuma hulɗa da su ta kafafen sada zumunta, lamarin da ya ƙara mata farin jini.
A yau, ana kallonta a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jaruman Kannywood masu taka rawar uwa.
Kuma tana ci gaba da ba da gudummawa wajen haɓaka masana'antar fina-finan Hausa tare da kasancewa abin koyi ga matasa masu sha'awar harkar fim