Mu'assasatu Darul Qur'an Wa Sunnah

Mu'assasatu Darul Qur'an Wa Sunnah Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mu'assasatu Darul Qur'an Wa Sunnah, Charitable organisation, Sheka Gidan Leda, Kano.

Tarjama Prof Sani umar rijiyar lemo HafizahullahSuratul Ali-Imran ita ce Sura ta Uku3 daga Sama 14. An kawata wa mutane ...
05/10/2024

Tarjama Prof Sani umar rijiyar lemo Hafizahullah

Suratul Ali-Imran ita ce Sura ta Uku3 daga Sama

14. An kawata wa mutane son sha'awace-sha'awace na mata da 'ya'ya da dukiya mai yawa abar tarawa ta zinariya da azurfa da kuma kiwatattun dawaki da dabbobi na gida da amfanin gona. Wadannan duk morewa ce ta rayuwar duniya; Allah kuwa a wurinsa ne kyakkyawar makoma take.

15. Ka ce: "Shin in ba ku labarin da abin da ya fi wadancan alheri? Wadanda s**a yi takawa, suna da wasu aljannatai wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu, a wurin Ubangijinsu, suna masu zama a cikinsu dindindin da mata na aure tsarkaka da kuma yarda daga Allah. Kuma Allah Yana ganin bayinsa.

Tafseer

Bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) a baya ya nuna cewa, dukiya da 'ya'ya ba za su amfani wadanda s**a kafirce masa ba, sai kuma a wadannan ayoyin yake gargadi ga wadanda kyale-kyalin rayuwar duniya za su shagaltar da su, har su manta da lahira.

Allah ya bayyana cewa, ya sanya wa mutane son wasu abubuwa na sha'awa, kamar mata da 'ya'ya maza da tara nau'ukan dukiyoyi iri-iri, kamar zinare da azurfa, da kiwatattun dawaki da rakuma da shanu da kananan dabbobi da gona kin noma.

Allah ya bayyana duk wadannan abubuwan na more dadin duniya ne, daga karshe su tafi su barsu, kuma a wurin Allah kadai ake samun kyakkyawar makoma da sakamako mai yawa marar yankewa.

Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana wa Annabinsa S A W cewa, akwai abin da ya fi wadannan kyale-kyali kayan sha'awar na duniya a wurin Allah, wadanda su ne aljannatai na ni'ima, da abin da yake cikinsu na gidaje manya-manya, wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu, ga kuma tsarkakan mata a cikinsu. Kuma wannan ni'imar ta har abada ce, ba mai yankewa ba, za su yi ta zama a cikinta har abada. Tare da wadannan ni'imomi kuma akwai wata babbar ni'ima, wadda ta zarce kowace ni'ima girma, ita ce samun yardar Allah (Mai tsarki da daukaka

An karbo daga Abu Sa'id Alkhudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah S.A.W ya ce "Allah Ta'ala zai ce wa 'yan Aljanna "Ya ku 'Yan Aljanna.

Sai su ce "Mun amsa maka, ya Ubangijinmu Sai ya ce "Shin kun yarda? Sai su ce: "Me zai sa ba za mu yarda ba, alhalin ka ba mu abin da babu wanda ka taba ba shi irinsa a cikin halittarka? Sai Allah ya ce To zan ba ku abin da ya fi wannan da na ba ku. Sai su ce Ya Ubangiji, mene ne kuma ya fi wannan da ka ba mu? Sai ya ce "Zan halatta muku yardata, daga yanzu ba zan yi fushi da ku ba har abada."Bukhari 6549, da Muslim 2829

za mu fahimci abubuwa kamar haka

1. Rage nuna damuwa ga kyale-kyalin duniya, mai gushewa nan da nan da himmatuwa wajen neman lahira, mai dawwama har abada.

2. Duk yawan abin duniyar da bawa zai samu; to jin dadi ne na wucin-gadi, zai mutu ya bar shi. Ni'ima ta har abada ita ce ni'imar lahira.

3. Wadannan ni'imomi da aka ambata a nan, ya kamata bawa ya kalle su ta fuskar da za su amfane shi, ba kallo irin na sha'awa ba. Idan ya yi haka to za su fi karfin zuciyarsa, har su karkatar da shi daga kan hanyar gaskiya.

Allah Ta'ala Ya datar damu Yasa mu wanye lafiya.

✍️ Ahmad Tijjani AL-Shekaweey

MONDAY 23/SEPTEMBER/2024Tunatarwa! Tunatarwa!! Tunatarwa!!!" Babu Wanda Yasan Muhimmancin Ibada Sai mamaci. "Ahmad Tijja...
23/09/2024

MONDAY 23/SEPTEMBER/2024

Tunatarwa! Tunatarwa!! Tunatarwa!!!

" Babu Wanda Yasan Muhimmancin Ibada Sai mamaci. "

Ahmad Tijjani AL-Shekaweey
Mu'assasatu Darul Qur'an Wa Sunnah

Address

Sheka Gidan Leda
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mu'assasatu Darul Qur'an Wa Sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share