29/05/2026
ƘUNGIYAR DHARUSSA’ADAH ISLAMIC ORPHANS ASSOCIATION TA RABA NAMAN SALLAH GA MARAYU 100 A KANO
Ƙungiyar Dharussa’adah Islamic Orphans Association da ke Sabuwar Mandawari, Kwanar Jega a Jihar Kano, ta gudanar da rabon naman Sallah ga marayu akalla 100 domin sanya farin ciki a zukatansu yayin bikin Eid-el-Kabir.
An gudanar da rabon naman Sallah ne a yammacin ranar Alhamis, 28 ga Mayu, 2026, a unguwar Sabuwar Mandawari da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, inda marayu daga gidaje daban-daban s**a amfana da tallafin rabon naman.
Da yake jawabi yayin taron, shugaban ƙungiyar, Musa Nasiru Musa, ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa nasarar gudanar da aikin yankawa marayu bijimi sa da akuya guda ɗaya, inda kimar su ta kai kusan naira miliyan 1.6.
Ya ce manufar shirin ita ce tallafa wa marayu domin su ma su ji daɗin walwala irin ta sauran al’umma a lokacin Sallah.
Haka kuma ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su ci gaba da tallafa wa ƙungiyoyin marayu domin gina al’umma ta gari mai ɗorewa tare da samun lada a ranar Lahira.
An gudanar da shirin rabon naman ne ƙarƙashin jagoranci da tallafawar mataimakin shugaban ƙungiyar, Umar Lawan Muhammad, tare da shugaban makarantar Nailussa’adah Islamiyya, Abdul’aziz Nasiru Musa, da sauran jagorori da mambobin ƙungiyar ciki har da Suleman Abbas, Alhajin Baba, Mannazi, Lawal Ahmad, Pillars, Hamisu Babba da sauransu.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar ya ƙara da yabawa gudummawar da masu hannu da shuni daga ciki da wajen Jihar Kano s**a bayar wajen ganin an tallafa wa marayun.
Ya ce: “Za mu ci gaba da ƙoƙari wajen tallafa wa marayu ta fannoni daban-daban domin inganta rayuwarsu da rage musu wahalhalu.”
A ƙarshe, an yi addu’ar Allah ya ƙara wa al’umma buɗi domin ci gaba da tallafa wa marayu da irin waɗannan ƙungiyoyi.
Allah ya saka wa kowa
da alkhairi.
COV: BYMN