Sheikh Zakzaky Foundation

  • Home
  • Sheikh Zakzaky Foundation

Sheikh Zakzaky Foundation Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sheikh Zakzaky Foundation, Community Organization, .

KHATAMA NA ZAMAN JUYAYIN SHAHADAR IMAM ALI (AS) A GARIN KANOYau talata 21 ga watan ramadan 'yan uwa almajiran sayyid Ibr...
10/03/2026

KHATAMA NA ZAMAN JUYAYIN SHAHADAR IMAM ALI (AS) A GARIN KANO

Yau talata 21 ga watan ramadan 'yan uwa almajiran sayyid Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky na garin kano sun ci gaba da Zaman juyayin shahadar Imam Ali (AS) a rana ta karshe, wanda zaman ke gudana yanzu haka a muhallin hussainiyar Imam Ridha Kofar waika kano.

JAMI’AN TSARO NA SHIRIN ZUBAR DA JININ AL’UMMAR MUSULMI A JIHAR KATSINA–Taron Manema Labarai Al’umma na sane da yaƙin da...
10/03/2026

JAMI’AN TSARO NA SHIRIN ZUBAR DA JININ AL’UMMAR MUSULMI A JIHAR KATSINA

–Taron Manema Labarai

Al’umma na sane da yaƙin da ke gudana yanzun haka tsakanin Ƙasar Amerika da Isra’el tare da haɗin bakin wasu daga cikin Ƙasashen Larabawa irin su Saudiyya, Qatar, Bahrain, Jodan da Dubai. Waɗannan Ƙasashe sun haɗa kai suna ta yaƙar Jamhuriyyar Musulumci ta Iran.

Wannan yaƙin ya sanya Duniya ta rabe zuwa gida biyu, Muminai a ƙarƙashin Jagorancin Ƙasar Iran, sai kuma masu goyama Azzalumai baya a ƙarƙashin Jagorancin Ƙasar America da Isra’el da munafikan shugabannin Ƙasashen Larabawa.

Akan hakane Gwamnatin tarayyar Nigeria take taka rawar zama Ƴar amshin Shata ga Ƙasar America da Isra’el, daman ta gayyato waɗannan Ƙasashe zuwa wannan Ƙasar wai da sunan samar da tsaro.
Wannan alaƙa dake tsakanin Gwamnatin Nigeria da ta Isra’el ta baiwa Jakadan Isra’el dake a Nigeria damar zargin Harkar Musulumci a Nigeria ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) da cewa wai tana horas da yara Ƴan Ta’ada.

Sai ga shugaban Ƴan sanda na Ƙasa (IG) ya baiwa Police ummarni akan cewa su sanya idanu da ɗaukar mataki ga duk waɗanda s**a fito s**a nuna goyon baya ga Jamhuriyyar Musulumci ta Iran. Sai muke ganin gamayyar Jami’an tsaron Sojoji da Police sunyi comber ta fiye da motoci Ashirin (20) ɗauke da muggan makamai da motocin yaƙi masu sulke suna ta sunturi a garin Katsina tun tsawon mako ɗaya a wannan Jihar ta Katsina mai fama da rashin tsaro na Bandits, ɓangaren da yafi kamata gwamnati ta maida hankali, Jami’an tsaro ya kamata su kai ɗauki don samar da tsaro, sai s**a ɓuge a cikin gari suna tada hankalin Jama’a suna neman afka ma mutanen da basu da tarihin tada hankali.

Fitowa a nuna goyon baya kuwa ga waɗanda ake zalunta amsa kiran Manzo (S.A.W.W) ne da yake faɗa a Hadisin sa cewa; “Idan Mumini yai yekuwa daga bangon gabas to wajibin Muminin dake a bangon yamma ne ya karɓa masa”. Wannan goyon baya da Addu’o’i shine abinda zamu iya nunawa ga Ƴan' uwanmu Musulmi da ake zalunta.

Kuma Ƙasashen Duniya anata yin Muzaharori sai anan Nigeria ake take wannan ƴancin da Constitution ya rigaya ya bada damar ayi. Don haka mu Ƴan'uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na Jihar Katsina muna kira da babbar murya ga Gwamnatin Jihar Katsina da duk wasu masu faɗa aji da sauran Jama’a cewa, duk wani abu da s**a ga ya faru a cikin al’umma to su tuhumi da zargi Jami’an tsaron da s**a zaƙu don su shekar da jinin al’umma.

Mun saba gudanar da jerin gwanon Muzaharori daban-daban, muyi mu tashi lafiya sama da shekara Talatin (30) batare da an kashe koda kiyashiba, ko an ɓannata dukiyar kowa ba, Al’ummar Katsina su shedane akan haka.

Don haka, idan anga wani abu yafaru a yanzu daga Jami’an tsaro ne.

Amincin Allah ya tabbata ga masu neman zaman Lafiya.

Daga: Ƴan'uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H), na Yankin Katsina.

(Talata 21-09-1447/10-03-2026)

💥
05/03/2026

💥

A Muslunci shi Jagora ne, a Shi'anci kuma Marji'i ne, a duniya kuma Jarumi ne, a wajen mutane kuma shi abun koyi ne.!
03/03/2026

A Muslunci shi Jagora ne, a Shi'anci kuma Marji'i ne, a duniya kuma Jarumi ne, a wajen mutane kuma shi abun koyi ne.!

02/03/2026

Har yanzu babu tabbataci Natanyahu yana raye. Bayan hari da aka kaiwa ofishinsa. Babu wani sabon Bidiyo da zai tabbatar yana raye

Munkarɓa muna masu godewa Allah😥
01/03/2026

Munkarɓa muna masu godewa Allah😥

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Zakzaky Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Sheikh Zakzaky Foundation:

  • Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization?

Share