Bello Sharada Support Organisation

Bello Sharada Support Organisation Wannan Tafiyace ta masu kishin al umma matasa da mata iyayenmu

Hon.Ibrahim Garba Dansiyane da yake da kishin al umma da kishin jaharsa Da kuma yankinsa dake kano Ibrahim garba yazo da manufofi managarta hakan yasa muke gayyatar dukkan maison ceton halin da muka tsinci kanmu a siyasance

SHIRI NA MUSAMMAN A KAN RAYUWAR BELLO MUHAMMAD SHARAƊA Ku kasance tare da gidan Radio Rahma 97.3FM a gobe Alhamis 3-9-20...
02/09/2026

SHIRI NA MUSAMMAN A KAN RAYUWAR BELLO MUHAMMAD SHARAƊA

Ku kasance tare da gidan Radio Rahma 97.3FM a gobe Alhamis 3-9-2026 da misalin ƙarfe 10:00 na safe, domin jinmu ɗauke da shiri na musamman a kan rayuwar Marigayi Malam Bello Muhammad Sharada da irin gudunmawar da ya ba wa al'umma.

A cikin shirin za mu kasance tare da wasu daga cikin makusatan Malam Bello domin su yi mana bayani kan yadda ya gudanar da rayuwarsa. Kuna da damar bugo waya tare da turo saƙonninku na Ta'aziyya a kan lambar waya 07077952939 a lokacin gabatar da shirin.

Marigayi Mallam Bello Muhammad Sharada : Ingantaccen Misali Abun Kwaikwayo a Wajen Matasan Wannan Zamanin.Daga Dr Umar M...
02/09/2026

Marigayi Mallam Bello Muhammad Sharada : Ingantaccen Misali Abun Kwaikwayo a Wajen Matasan Wannan Zamanin.

Daga Dr Umar Musa Mustapha,
DG na H.E Senator Mallam Ibrahim Shekarau Kuma Shugaban Majalisar Shekarau Shura ta jihar kano.

Tare da cikakkiyar sallamawa ga ikon Allah, muke bayyana alhinin mu na rashin Mallam Bello Muhammad Sharada wanda Allah ta'ala ya amshi rayuwarsa a yammacin ranar Asabar, 29 ga watan Agusta ta shekarar 2026, bayan yar gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 56. An gabatar da sallar jana'izarsa a safiyar ranar Lahadi, 30 ga watan Agusta ta shekarar 2026 da misalin karfe 8:00 na safe a babban masallacin juma'a na unguwar Sharada. An binne gawar Mallam Bello a makabartar Musulmi ta Fadama dake unguwar Sharada. Dandazon al'ummar da s**ai masa Sallah kuma s**ayi masa rakiya zuwa makwancinsa na karshe shaidace ta irin kyakkyawar rayuwar da ya gabatar a tsakanin al'umma.

Marigayi Mallam Bello Sharada cikakken magidanci ne, duk da bai kasance mai tarin dukiya ba, amma ya rayu da kana'a da kuma wadatar zuciya. A wasu lokutan da kaina na sha bashi hayar gona wadda yake noma abinci domin ciyar da iyalansa. Wannan shaidace mai kyau domin tana bayyana mamacin a wanda ya rayu a matsayin cikakken dan gwagwarmaya, sannan kuma hakan shaida ce akan Mallam Bello ya rayu a matsayin mutum mai cikakken dogaro ga Allah (Tawakkali).

Ya kasance malamin addini mai basira, malamin da koyarwarsa bata gajiyarwa, sannan cikkakken dan Da'awah ne a kungiyoyi mabanbanta. Yana da hakuri sosai. Sannan Allah ya bashi saukin fahimtar al'amura. Mutane da yawa na zuwa gareshi domin neman shawara.

A bangaren aikin yada labarai kuwa ya ciri tura. Mallam Bello yayi aiki a matsayin Babban Edita a jaridar Tajdid da sauran kafefen yada labarai. Ya kasance yana gudanar da shirye shiryen Fashin baki da wayar da kan al'umma a gidajen rediyoyi da dama a jihar Kano. Bayanan sa cike suke da tarin hujjoji masu tsananin ilimantarwa da kuma gamsarwa ga duk wani mai sauraronsa.

Assalamu Alaikum Warahmatullah'Yan Uwa muna godiya da irin addu'o'inku ga Malam Bello Muhammad Sharada, Alhamdulillah.Ka...
31/08/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullah

'Yan Uwa muna godiya da irin addu'o'inku ga Malam Bello Muhammad Sharada, Alhamdulillah.

Kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) yace: "Nafsul-mu'mini mu'allaqun bi-daynihi hattaa yuqdaa 'anh".

Ma'ana : "Ruhin mumini yana Makale da bashi har sai an biya masa"

Kuma kamar yadda shi marigayi ya rubuta a wannan shafin a watannin da s**a gabata cewa :

"A Karshe ina addu'a Allah kayi mana tsari da jinya mai nauyi da talauci mai tozartarwa da bashi Mai kunyatarwa da tsufa mai rikitarwa. Allah Ka lamunce min na sauke duk nauyin dake kaina na duk wani hakkin jama'a"

Mu iyalansa muna rokon duk wani ko wata da s**ai mu'amala wadda akwai nauyi akansa, su taimakeshi su fadamana ta wannan lambar--0909 924 700 94.Kira ko WhatsApp!

Wadanda S**a sarayar masa kuma suma su sanar mana.

A Karshe muna rokon 'yan Uwa da sakashi a cikin addu'o'inku domin nema masa gafara da sabati a wajen Allah (SWT).

Sanarwa
Mubarak Bello Muhammad
Amadadin 'Yan Uwa Da Iyalan Marigayi Mallam Bello Muhammad Sharada

ALLAHU AKHBAR 😭Da Safiyar Lahadi, 30/08/2026Aka gudanar da jana’izar marigayi Malam Bello Muhammad Sharada  Kamar Yadda ...
30/08/2026

ALLAHU AKHBAR 😭

Da Safiyar Lahadi, 30/08/2026

Aka gudanar da jana’izar marigayi Malam Bello Muhammad Sharada Kamar Yadda Addininmu Ya Tsara a Babban Masallacin Juma’a na Sharada.

Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa da rahama, Ya sa Aljannar Firdausi ce makomarsa Allah Ya Albarkaci Bayansa Amin.🤲

😭🤲🏼
29/08/2026

😭🤲🏼

29/08/2026

Innalillahi Wa’innah ilaihi raji’un.😭

Address

Sharada Phase One Kano
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bello Sharada Support Organisation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share