07/04/2026
HADISIN MU NA YAU
Manzon Allah {ﷺ} ya ce: “Abubuwa uku, (3) idan mutum ya yi su da gaske gaskiya ne; kuma idan ya yi su da wasa gaskiya ne: Aure, saki, da dawo da mace (bayan saki).
[ƘARIN HASKE]
1. Ma’anar “جدُّهنّ جدٌّ، وهزلهنّ جدٌّ”:Wato, waɗannan abubuwa ba wasa ake yi da su ba, domin suna da hukunci na shari’a mai tsanani. Idan mutum ya faɗi su da wasa, to hukuncin shari’a zai tabbata.
2. (1) An-nikāḥ (Aure): Idan mutum ya kasance ya yi maganar aure tare da sharuddan shari’ah (waliyyi, shaidu, amincewa), ko da fa wasa ne, to aure ya tabbata. Ba a cewa “ina wasa kawai nake” bayan ya yi lafazin aure.
3. (2) At-ṭalāq (Saki): Idan mutum ya ce wa matarsa “na sake ki”, ko da wasa yake yi, saki ya tabbata.
4. (3) Ar-raj‘ah (Dawo da mace bayan saki):Idan mutum ya saki matarsa saki ɗaya ko biyu, Kuma sannan a lokacin iddarta ya ce “na dawo da ke”, ko da wasa yake, dawowa ta tabbata.
5. Manufar hadith ɗin:Musulmi ya kasance mai natsuwa da hankali wajen amfani da kalmomi da s**a shafi auratayya da saki, domin su na da matuƙar muhimmanci a shari’a. Wasanni, barkwanci, ko motsin rai ba su canza hukunci a cikin waɗannan abubuwa ba.
Ga darasin da za a ɗauka daga hadith ɗin biyu:
(1): Addu’ar farkon salla tana koyar da tsarkake kai da tawali‘u gaban Allah. (2): Aure, saki da dawo da mace ba wasa ake yi da su ba, domin suna da sakamako mai girma a shari’a. (3): Annabi 💓{ﷺ}💓 ya koyar da cewa kalma tana da nauyi, don haka fa musulmi ya kiyaye harshensa.
ALLAH YA DATAR DA MU DA FALALARSA
Yar Hajiya ✍️✍️