15/05/2026
A madadin al'ummar unguwar Warure, da daliban wannan unguwa suna miƙo sakon godiya ga jagora Baba Habu, kuma uba ga wannan ƙungiya ta Warure Students' Association (WASA) bisa ɗaukar nauyin dalibai da marayu da kuma tallafawa matasa da aka yi alƙawarin aiwatar nan ba da jimawa ba.
Babu shakka, al'ummar wannan unguwa sunyi farin ciki da irin wannan karamchi da taimako da aka ƙaddamar da ɗambarsa musamman a a abinda ya shafi harkar Ilimin yara Maza da Mata.
Wannan ƙungiya ta WASA tana mai addu'ar Allah ta'ala ya bawa jagora nasara acikin rayuwar sa ya cika masa burin sa ya ƙara yalwata arzikinsa.
Warure Students' Association
Media Center.