12/05/2026
12/05/2026
Shugaban Gammayyar Kungiyar Cigaban Kasuwar Singa da kewayenta (SIMDA), Barr. Junaidu Muhammad Zakari, Ya Karɓi Bakoncin Sabon Sakataren Zartarwa na Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye na Jihar Kano, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, a Ofishinsa.
Mai Girma Shugaban Kasuwar Singer (SIMDA), Alh. Junaidu Muhammad Zakari Esq., ya karɓi bakuncin Sakataren Zartarwa na Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye na Jihar Kano, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, a yau yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai ofishin shugaban da ke Kasuwar Singer a jihar Kano.
A yayin ziyarar, Barrister Junaidu Muhammad Zakari ya taya Dr. Ibrahim Garba Muhammad murnar naɗin da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano ya yi masa. Ya bayyana sabon Sakataren Zartarwan a matsayin mutum mai ƙwazo, jajircewa da sadaukarwa wajen aiki, wanda shugabancinsa zai kawo ci gaba mai amfani ga kare haƙƙin masu saye da bunƙasa harkokin kasuwanci a faɗin jihar.
A nasa jawabin, Dr. Ibrahim Garba Muhammad ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce samar da haɗin kai da kyakkyawar alaƙa tsakanin Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye na Jihar Kano da Ƙungiyar SIMDA. Ya jaddada muhimmancin yin aiki tare domin dakile matsaloli tare da hana yaduwar kayayyakin da ba su dace da amfanin ɗan Adam ba a kasuwannin jihar Kano.
Ya kuma bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen wayar da kan ‘yan kasuwa da masu sana’o’i kan ingantattun hanyoyin gudanar da kasuwanci tare da kare muradun masu saye da masu sayarwa baki ɗaya.
A cewarsa, manufar wannan yunƙuri shine tsaftacewa da kare martabar kasuwancin Jihar Kano tare da samar da ingantaccen muhalli mai lafiya ga harkokin kasuwanci.
Haka kuma,Dr. Ibrahim Garba Muhammad ya tabbatar wa ‘yan kasuwa cewa Gwamnatin Jihar Kano a shirye take domin tallafa wa harkokin kasuwanni da inganta yanayin kasuwanci. Ya buƙaci shugabannin Kasuwar Singer da su yi aiki kafada da kafada da Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye domin cimma manufofin da aka sa gaba don amfanin ‘yan kasuwa da masu saye baki ɗaya.
Sakataren Zartarwan, wanda ya k**a aiki a hukumance a yau, ya bayyana cewa ziyarar da ya kawo ofishin Shugaban SIMDA shine aiki na farko da ya fara yi tun bayan k**a aikinsa.
Taron ya gudana cikin nasara tare da tattaunawa mai amfani tsakanin ɓangarorin biyu. Mambobin tawagar Sakataren Zartarwan sun samu kyakkyawar tarba daga shugabannin SIMDA da s**a haɗa da Alh. Aminu Umar Dogara Mataimakin Shugaba na daya, Amb. Abubakar Usman Ali Sakatare, Barr. Abdullahi Usman Mashawarci kan harkokin Shari’a, Alh. Nasiru Idris Nanu Ma’aji II, da Mal. Bashir Umar Bello PRO II, waɗanda suma s**a bayar da gudummawa mai amfani tare da kalaman ƙarfafawa domin samun nasarar Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye ƙarƙashin sabon jagoranci.
Barrister Junaidu Muhammad Zakari ya kuma miƙa takardar shawarwari a rubuce ga Sakataren Zartarwan.
An kammala taron cikin fahimtar juna da tabbatar da haɗin kai da jajircewa wajen samar da kasuwanni masu aminci, kare haƙƙin masu saye, da bunƙasa harkokin kasuwanci mai ɗorewa a Jihar Kano.
Sa Hannu:
Amb. Abubakar Usman Ali, Sakatare
A Madadin: Alh Junaidu Muhammad Zakari Esq
Shugaban Kasuwar Singa (SIMDA)