Almufid Islamic Foundation

Almufid Islamic Foundation Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Almufid Islamic Foundation, Nonprofit Organization, KLP-001, Plot 2, Block 'K', Mani-Katsina Road, Kano.

15 ga Rabi'u Thaniy, 1448H27 ga Satumba, 2026MTafiyarka zuwa masallaci domin neman ilimi ba tafiya ce ta banza ba. Allah...
27/09/2026

15 ga Rabi'u Thaniy, 1448H
27 ga Satumba, 2026M

Tafiyarka zuwa masallaci domin neman ilimi ba tafiya ce ta banza ba. Allah na iya rubuta maka ladan k**ar na mahajjaci mai cikakkiyar Hajji. Kada ka bar majalisun Alƙur'ani da ilimi.

Manzon Allah ﷺ ya bayyana girman ladan wanda ya tafi masallaci da niyya ta gaskiya, ba don komai ba sai domin ya koyi ilimi mai amfani ko ya koyar da shi. Irin wannan mutum yana samun ladan k**ar na mahajjaci wanda ya cika hajinsa. Wannan yana nuna darajar majalisun ilimi da muhimmancin neman ilimi da koyar da shi.

Manzon Allah (S.A.W):   "Duk wanda wanda ya yalwata ma mai ƙunci, Allah zai yalwata masa duniya da Lahira"(Muslim)
26/09/2026

Manzon Allah (S.A.W):

"Duk wanda wanda ya yalwata ma mai ƙunci, Allah zai yalwata masa duniya da Lahira"

(Muslim)

A Fassara mana Hadisin nan guda biyu zuwa Hausa;
26/09/2026

A Fassara mana Hadisin nan guda biyu zuwa Hausa;

14 ga Rabi'u Thaniy, 1448H26 ga Satumba, 2026MHanyar Aljanna tana farawa da ayyuka masu sauƙi: ka bauta wa Ar Rahman, ka...
26/09/2026

14 ga Rabi'u Thaniy, 1448H
26 ga Satumba, 2026M

Hanyar Aljanna tana farawa da ayyuka masu sauƙi: ka bauta wa Ar Rahman, ka ciyar da abinci, ka yaɗa sallama. Wanda ya yaɗa zaman lafiya a duniya, Allah zai shigar da shi Aljanna cikin aminci.

Manzon Allah ﷺ ya haɗa manyan ayyuka uku masu sauƙin aikatawa amma masu girman lada: bautar Allah Shi Kaɗai, ciyar da abinci, da yaɗa sallama tsakanin mutane. Waɗannan ayyuka suna gyara alaƙar bawa da Ubangijinsa, suna ƙarfafa zumunci, kuma suna zama sanadin shiga Aljanna cikin aminci.

A Lissafin Sultanate Council (Fadar Sarkin Musulmi)

On behalf of the Management, Staff, Friends followers and well wishers of Almufid Islamic Foundation we wish you a fruit...
25/09/2026

On behalf of the Management, Staff, Friends followers and well wishers of Almufid Islamic Foundation we wish you a fruity Juma'a, May all that you prayed for be granted in the best manner.

Dear Muhammad Sani Zayyana,

Thank you and Jazakumullahu Khyr.

25/09/2026

A Special visit by Shaikh Dr. Zakir Naik to Shaikh Mahmoud Alhasanat 🤍.

24/09/2026

Ku sanyaya yinin ku da tattausar tilawa da ga gwani Abdul ganiyy Katsina

13 ga Rabi'u Thaniy, 1448H24 ga Satumba, 2026MBa ado kaɗai ne ke ƙawata mace ba, taƙawa, kunya da kyawawan ɗabi'u su ne ...
24/09/2026

13 ga Rabi'u Thaniy, 1448H
24 ga Satumba, 2026M

Ba ado kaɗai ne ke ƙawata mace ba, taƙawa, kunya da kyawawan ɗabi'u su ne mafi girman ƙawa. Mafi alherin mace ita ce wadda ta haɗa biyayya ga Allah da kyautata wa iyalinta.

Annabi ﷺ ya bayyana siffofin mafi alherin mata da kuma mafi munin mata.
Mafi alherin mata su ne masu ƙaunar mazajensu, masu taimako da jituwa da su a cikin alheri, idan suna tsoron Allah.
Mafi munin mata kuma su ne masu bayyana kwalliyarsu ga waɗanda ba muharramansu ba, da masu girman kai da nuna isa.
Cewa "su munafukai ne" tana nufin suna k**a da munafukai a wannan ɗabi'a, ba lallai tana nufin sun fita daga Musulunci ba.

12 ga Rabi'u Thaniy, 1446H23 ga Satumba, 2026MManzon Allah ﷺ ya ce:“Idan ɗayanku ya ga wani abu a cikin kansa, ko dukiya...
23/09/2026

12 ga Rabi'u Thaniy, 1446H
23 ga Satumba, 2026M

Manzon Allah ﷺ ya ce:
“Idan ɗayanku ya ga wani abu a cikin kansa, ko dukiyarsa, ko a wajen ɗan’uwansa wanda ya burge shi, to ya yi masa addu’ar albarka. Domin lallai idanu (Kambun Baka) gaskiya ne.”

Wato idan ka ga wani abu mai kyau da ya burge ka, kada ka tsaya kawai kana sha’awa, sai ka ce:
“Allah Ya sanya albarka a cikinsa.”
ko “Allah Ya albarkace shi.”

Wannan yana koyar da mu mu haɗa sha’awa da addu’ar albarka, domin kada hassada ko cutarwar ido ta shiga cikin lamarin.

Address

KLP-001, Plot 2, Block 'K', Mani-Katsina Road
Kano
820101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Almufid Islamic Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Almufid Islamic Foundation:

Shortcuts

Share