Sanin Haƙƙinka

Sanin Haƙƙinka Leadership • Governance •Public Awareness

24/06/2026

Abin takaici ne al’umma ta kai matsayin da raba shinkafa da taki ya zama abin da ake ɗauka a matsayin mafita ga matsalolin rayuwa. Ko da yake irin wannan tallafi na iya rage wa wasu radadi na ɗan lokaci, ba shi ne mafita ta dindindin ga talauci da matsin tattalin arziki ba.

A yau, mutane da yawa ba sa iya sayen abinci, taki da sauran buƙatun rayuwa da kuɗinsu. Farashin kaya na ci gaba da tashi, yayin da hanyoyin samun kuɗi ke ƙara wahala. Iyaye suna fama da ciyar da iyalansu, biyan kuɗin makaranta da kula da lafiyarsu.

Abin da ya fi damun rai shi ne yadda ake karkatar da hankalin jama’a daga manyan matsalolin da ke addabar su zuwa ga abubuwan da ba su magance tushen matsalar ba. Alhali kuwa abin da jama’a ke buƙata shi ne ayyukan yi, ingantaccen ilimi, kiwon lafiya mai kyau, hanyoyi masu kyau da bunƙasar tattalin arziki da za su ba su damar dogaro da kansu.

Ba za a iya gina al’umma mai ɗorewa da ci gaba ba idan mutane suna jiran tallafi lokaci zuwa lokaci maimakon samun damar rayuwa cikin mutunci ta hanyar aikinsu da sana’arsu. Kyakkyawan shugabanci yana bayyana ne ta yadda rayuwar jama’a ta inganta, ba wai yawan abubuwan da ake rabawa ba.

Abin takaici kuma, mutane da dama suna ganin abin da ke faruwa, suna fahimtar matsalolin da ake ciki, amma suna yin shiru saboda son rai, anfani na kashin kai ko wata bukata ta daban. Yin shiru a lokacin da ake buƙatar magana ba ya kawo gyara.

Lokaci ya yi da za a fara neman gaskiya, rikon amana da cikakken bayani kan yadda ake tafiyar da al’amuran jama’a. Ya kamata burinmu ya zama gina al’umma inda kowa zai iya samun abin da yake buƙata ta hanyar halal da ƙoƙarinsa, ba wai jira tallafi lokaci zuwa lokaci ba.

Allah Ya gyara mana al’amuranmu, Ya ba mu shugabanni masu adalci da kishin talakawa, Ya kuma ba mu ƙarfin guiwar faɗin gaskiya a kowane lokaci.

Address

Kano
700271

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sanin Haƙƙinka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share