05/08/2022
DALILIN DA YASA AKE ZABAR BIYOWA TA LAYIN ADDINI DOMIN CIMMA MURADUN SIYASA..?
Akwai abinda Malamai masana ilmin dabi'ar dan adam (Psychologist) suke kira da "Gaslighting", hakan na nufin "Hanyar da wani zai amfani da kwarewar iya zance da yakar tunani, wajen jefa shakku ko kwankwanto ga wani ko wasu, akan abinda ya faru dasu kuma suke da yakini akansa".
Duk wanda yake Nigeria, yasan me ya kasance a jiya, kuma yasan abinda yake wakana a yanzu, kowa yasan irin halin da ake ciki na tashin farashin kayayyaki, linkuwar tsadar rayuwa, asarar rayuka da kuma barnata dukiyooyin al'umma da bata gari keyi a kullum da sauransu.
Amma idan 'Yan Siyasa s**a shigowa al'umma ta rigar Addini, ta hanyar siye imanin Malamai, idan Malami ya shirya zantuka na zallar yakar tunani da jefa shakku da kwankwanto a zukatan mabiya ta hanyar zayyano wasu dalilai da misalai na zamba, saboda raunin mabiyansu na makauniyar biyayya da soyayya, sai ka samu su mabiyan sun shiga hali na shakku da konkonto akan wai anya da gaskene ma akwai laifin masu mulki cikin halin da ake ciki..? Karshe dai sai tantama ya wanzu a zukatansu sai ya zamto yan siyasa sun samu damar da zasu sake baje hajarsu akansu.
Duk da ni da kai mun sani cewa babu wata maslaha da addini ke samu, ko mabiya addinai a mulkin masu mulkin Nigeria, amma akan zabi amfani da addini a yayin kakar siyasa domin cimma wannan kuduri ta hanyar amfani da salo na "GASLIGHTING".
ALLAH YA 'YANTO MABIYA DAGA KOMAR MALAMAI MASU CI DA ADDINI.
ALHAMDULILLAH