Al-Ihsan Youth Development Asso. Bichi

Al-Ihsan Youth Development Asso. Bichi AL-IHSAN YOUTH COMMUNITY DEVELOPMENT ASSOCIATION BICHI.

01/01/2026
22/12/2025

Asslamu Alaikum
Idan Allah ya kaimu gobe Talata, za'a tantance masu yanar Ido domin yi musu aiki kyauta, a Hagagawa community clinic, Hagagawa Bichi da misalin karfe 10:00 na safe. Allah ya bamu sa'a Ameen

Representing the Association at 2026 Kano State Appropriation bill our submission was:1. Lasting solution to Bichi Tsoho...
14/12/2025

Representing the Association at 2026 Kano State Appropriation bill our submission was:
1. Lasting solution to Bichi Tsohon Gari Water supply.
2. Connecting Girawa Community with Electricity Supply
3. Erosion Control in Darul Fairah Area
4. Provision of more toilets structures and connecting them with water supply for better use and maintenance
Insha Allah the Committee promised to look into it and ask the Association to also forward the document to Honorable Lawan Shehu Bichi for further inclusion.
Thank you God Bless Al-ihsan Family.

Sunday
14-12-2025

Alhamdulillah.....Kungiyar AL-IHSAN YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION BICHI, ta halarci taron karrama mai girma Baturen "Yan...
09/11/2025

Alhamdulillah.....

Kungiyar AL-IHSAN YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION BICHI, ta halarci taron karrama mai girma Baturen "Yan Sanda na KH Bichi wato CSP Murtala Muhammad Fagam, wanda aka gabatar a jiya Asabar 08-11-2025.

A yayin Taron kungiyar ta bashi lambar yabo (Award Certificate) saboda irin kokarinsa da kuma cigaban da ya kawo a fannin ingataccen tsaro a wanann KH tamu ta Bichi mai albarka.

Amadadin dukkan Shugabanni da Mambobi muna sake jaddada murna da fatan alkhairi agareshi da addu'ar Allah ya karo dubun nasarori Ameeen.

Mustapha Tijjani Shehu
Sakatare
09-11-2025

Alhamdulillahi.Wannan kungiya ta Karkare shirinta na rabon Sanitary pad ga yan uwa mata a makarantar Ihya'u Ulumiddin Is...
07/10/2025

Alhamdulillahi.
Wannan kungiya ta Karkare shirinta na rabon Sanitary pad ga yan uwa mata a makarantar Ihya'u Ulumiddin Islamiyya yarkasuwa Bichi.
Dalibai 35 ne s**a amfana da Sanitary Pad Pieces 185.
Yazuwa yanzu da muka karkare wannan shiri, kungiyar ta Raba Sanitary Pad pieces 1,085 ga dalubai 235 da s**a fito daga Makarantun kamar haka.
1. GGSS BICHI
2. GGASS BICHI
3. GGSS CHIRANCI da kuma
4. IHYA'U ULUMIDDIN ISLAMIYYA.
Shugaban kungiyar yayi kira da Al'umma musamman masu Hali wajen kula irin waddannan abubuwa da ake musu kallon Kanana, haka kuma ya ja hankalin Dalibai da su cire kunya a cikin dukkan abinda ya shafi tsarki da Mas'alolin addini inda yai kira ga daluban da su rika tambayar Malamai musamman mata.
Haka kuma, yayi godiya ga yan Kungiyar Bisa wannan kokari da s**ai.
Shuwagabannin makarantun suma sunyi Godiya ga wannan kungiya bisa wannan tallafi.

Al'Ihsan Youth Development Association Bichi.

Innalillahi wainna ilaihi Raji'un.Allah yayi wa malam Shazali mai wankin Hula Rasuwa.Kafin Rasuwarsa, ya sha fama da jin...
05/10/2025

Innalillahi wainna ilaihi Raji'un.
Allah yayi wa malam Shazali mai wankin Hula Rasuwa.
Kafin Rasuwarsa, ya sha fama da jinya wanda har ta kai kun nemi Yan uwa su taimaka domin a kula dashi.
Mutane 8 ne s**a taimaka da kudi naira Dubu sha Uku, wanda a karshe muka mika kudin ga iyalansa ta hannun Yaronsa.
Za'ai Jana'izarsa a gobe da misalin Karfe 7 na safe, a gidansa dake Layin gidan Abdullahi dan zago, Bayan Gidan Malam Hussaini Musa.

Allah Ubangiji ya gafartawa

SAKON GODIYA...!!!Amadadin Kafatanin yan wannan Kungiya mai albarka musamman yan kwamitin lafiya, muna mika sakon godiya...
02/10/2025

SAKON GODIYA...!!!
Amadadin Kafatanin yan wannan Kungiya mai albarka musamman yan kwamitin lafiya, muna mika sakon godiyarmu ga wani Bawan Allah da ya Bawa wannan kungiya mai albarka gudummawa ta Sanitary Pad Pieces 120 (Leda 12).
Bawan Allahn da ya nemi a sakaya sunansa ya Bayyana jin dadinsa Bisa wannan taimako na Sanitary Pad guda 1,000 da kungiyar Al'Ihsan ta bawa Daliban Manyan makarantun Sakandare na Mata.
Muna Addu'ar Allah Ubangiji ya Saka masa da Alkhairi Ya Biya masa Bukatunsa.

RANA TA UKU.Kungiyar Matasa ta Al'Ihsan Youth Development Association Bichi ta gudanar da Lecture ta Musamman tare da Ra...
02/10/2025

RANA TA UKU.
Kungiyar Matasa ta Al'Ihsan Youth Development Association Bichi ta gudanar da Lecture ta Musamman tare da Rabon Sanitary Pad ga yan uwa mata dake makarantar GGSS CHIRANCHI.
Makarantar ta kasanche ta uku a cikin gerin da Makarantun da kungiyar ta Ziyarta.
shugaban kwamitin lafiya, Mustapha Tijjani Shehu ya yabawa Shugabar makarantar (Malama Amina) Bisa cancantar Daliban da ta Bayar domin cin moriyar Shirin.

Haka kuma, Sakataren kwamitin na lafiya Aminu Rabi'u Na'iya ya bayyana cewa, nan da bada dadewa ba kungiyar zata Sanar da makaranta ta gaba wadda anan ne ake sa ran karkare Shirin.
Shugaban kungiyar, Engr. Abubakar Abdurrazaq Abdullahi ya yabawa 'Yan kungiyar da kuma yan kwamitin na lafiya Bisa cimma wannan Nasara.

PRO AL'IHSAN
Umar Rabi'u Shu'aibu.

RANA TA BIYU.....!!!KUNGIYAR AL'IHSAN YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION BICHI TA GUDANAR DA RABON SANITARY PAD  KASHI NA BIY...
30/09/2025

RANA TA BIYU.....!!!
KUNGIYAR AL'IHSAN YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION BICHI TA GUDANAR DA RABON SANITARY PAD KASHI NA BIYU,GA DALIBAI MATA DA KE MANYAN MAKARANTUN SECONDARY NA BICHI.

A yau Talata 30-09-2025 Kungiyar Al'Ihsan Youth Development Association Bichi ta gudanar da Rabon Sanitary Pad ga daluban makarantar mata ta GGASS BICHI.

Kungiyar ta Gabatar da Lecture akan Tsaftar Kai da kai (Personal Hygiene) tare kuma kuma raba Sanitary pad ga Dalibai 65 da s**a amfana.

Zuwa yanzu, Kungiyar ta raba Sanitary Pad guda 650 ga dalubai 130 na Makarantun GGSS BICHI da kuma na GGASS Bichi.
Idan Allah ya kaimu Ranar Alhamis 2/10/2025, kungiyar zata kare shirinta a makarantar mata ta GGSS CHIRANCI a inda ake sa ran Dalubai 70 zasu amfana.

Mustapha Tijjani Shehu
Sakataren AL'IHSAN
Shugaban Kwamitin Lafiya

KUNGIYAR AL'IHSAN YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION BICHI TA KADDAMAR DA RABON SANITARY PAD GA DALIBAI MATA DAKE KARAMAR HUK...
29/09/2025

KUNGIYAR AL'IHSAN YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION BICHI TA KADDAMAR DA RABON SANITARY PAD GA DALIBAI MATA DAKE KARAMAR HUKUMAR BICHI.

A yau Litinin 29-09-2025 Kungiyar Al'Ihsan Youth Development Association Bichi ta kaddamar da shirinta na rabon Audugar Mata (Sanitary Pad) Guda Dubu daya (1,000).

Inda aka fara da Makarantar Mata ta GGSS Bichi. Kungiyar ta Gabatar da Lecture akan Tsaftar Kai da kai (Personal Hygiene) tare kuma kuma raba Sanitary pad ga Daliban Makarantar Mata ta GGSS Bichi a inda Dalibai 65 S**a amfana.

Idan Allah yakaimu gobe Za'a gabatar da irin wannanan shirin a Makarantar Mata ta GGASS Bichi, sannan ranar Alhamis kuma a Makarantar Mata ta GGSS Chiranchi.

Mustapha Tijjani Shehu
Sakataren AL'IHSAN
Shugaban Kwamitin Lafiya

Assalamu Alaikum....A Sakamakon Posting da akayi jiya na neman taimakawa wani mara lafiya (mai fama da cancer a mafitsar...
27/09/2025

Assalamu Alaikum....
A Sakamakon Posting da akayi jiya na neman taimakawa wani mara lafiya (mai fama da cancer a mafitsara) a jiya, yazuwa ynx an samu naira 8,000 daga wajen mutane 4, kari akan naira 5,000 da nayi posting da safe cewa an samu daga wajen mutane hudu.
Jimilla:- Naira 13,000 da aka samu daga wajen mutane 8.
Allah ya saka da alkhairi
Allah kuma ya bada ikon taimakwa.

Account Number:- 6993880190
Bank:- Moniepoint
Account Name:- AL-IHSAN YDA BICHI

Address

Buden-Gari Quarters Bichi LG
Kano
12345

Telephone

08105306738

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-Ihsan Youth Development Asso. Bichi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share