04/09/2025
MATSALAR BARIN YARA SUNA GARARAMBA BABU KARATU BABU TAIMAKO
A yau muna ganin yara da yawa suna yawo a tituna, kasuwanni da unguwanni ba tare da makaranta ba, babu ilimi,
babu kulawa. Wannan lamari ya zama babban barazana ga iyaye, alโumma, da kuma gaba ษaya ฦasar nan.
Idan yaro ya tashi ba tare da ilimi da tarbiyya ba, yawanci yana fadawa cikin miyagun dabiโu
faษa da ษaba,
sace-sace,
shaye-shaye, da shiga ฦungiyoyin barna. Wannan yana lalata rayuwarsu, yana kuma kawo tashin hankali da zaman ษar-dar a cikin alโumma.
Ilimi kuwa shi ne haske da makamin rayuwa. Idan aka bar yaro ba tare da shi ba, makomar ฦasa gaba ษaya tana cikin haษari, domin ba za mu samu shugabanni nagari, malamai, likitoci, injiniyoyi ko masu aikin yi ba. Sai dai mu samu matasa marasa amfani, waษanda za su iya zama barazana ga kowa.
ALLAH Subhanahu wata'ala yana cewa
> ููุง ุฃููููููุง ุงูููุฐูููู ุขู
ููููุง ูููุง ุฃููููุณูููู
ู ููุฃููููููููู
ู ููุงุฑูุง
โYa ku waษanda kuka yi imani, ku tsare kanku da iyalanku daga wuta.โ
(Suratut-Tahrim: 6)
ANNABI MUHAMMAD ๏ทบ Yana cewa
> ูููููููู
ู ุฑูุงุนู ูููููููููู
ู ู
ูุณูุฆูููู ุนููู ุฑูุนููููุชููู
โDukanku makiyaya ne, kuma dukanku za a tambaye ku game da abin da kuka kiyayye.โ
(Bukhari da Muslim)
Wannan yana nuni da cewa iyaye suna da nauyin kula da tarbiyyar โyaโyansu, domin kada su tashi a barauniyar hanya.
Imam Ali (AS) ya ce:
> โููููุจู ุงููุญูุฏูุซู ููุงููุฃูุฑูุถู ุงููุฎูุงููููุฉูุ ู
ูุง ุฃููููููู ูููููุง ู
ููู ุดูููุกู ููุจูููุชูููโ
โZuciyar yaro kamar ฦasa ce marar tsiro, duk abin da aka shuka a cikinta za ta karษa.โ
Wannan yana nuna muhimmancin a shuka ilimi da tarbiyya mai kyau a cikin zuciyar yara tun suna ฦanana.
Abin da ya kamata mu yi
Iyaye su ja โyaโyansu jikin su, su nuna musu ฦauna da kulawa, su tura su makaranta ko sanaโa mai amfani.
Gwamnati ta samar da makarantun zamani da tallafin kayan karatu ga marasa ฦarfi.
Malamai, shugabanni da masu hannu da shuni su tallafa wa marayu da talakawa wajen samun karatu.
A ฦarfafa tarbiyya ta addini da ta zamantakewa domin