25/01/2025
Alamomi 10 da za ku gane idan Æ´aÆ´anku sun fara shaye-shaye
Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi matsala ce da ta jima tana ci wa al'umma tuwo a ƙwarya, musamman a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Gwamnatoci a matakai daban-daban sun sha ɓullo da matakan yaƙi da ɗabi'ar, ciki har da kafa hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya ta NDLEA.
Galibi dai matasa ne s**a fi faÉ—awa tarkon É—abi'ar ta shaye-shaye.
Kuma a lokuta da dama shaye-shayen kan haifar da wasu munanan É—abi'u, k**ar sace-cace, da dabanci da sauran laifuka.
Hukumar NDLEA dai ta ce matasa ne rukunin al'umma da ke kan gaba wajen ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.
Yadda za a gane mai shaye-shaye
Abdullahi Sardauna, babban mataimakin kwamandan hukumar NDLEA mai kula da k**a masu laifi da horas da ma'aikatan hukumar reshen jihar Borno, kuma tsohon jami'i mai kula da fadakarwa da gyaran halin masu ta'ammali da ƙwaya na hukumar ya shaida wa BBC wasu alamomi guda 10 da iyaye za su lura da su domin gane yaransu sun fara shaye-shaye, k**ar haka:
1 - Sauyawar É—abi'a
Abu na farko da iyaye za su lura da shi, shi ne sauyawar halayyar Æ´aÆ´ansu, k**ar yadda jami'in ya bayyana.
''Idan a baya yaronka yana da ladabi da biyayya, sai kuma daga baya ka fahimci ya daina, ya kuma koma wasu É—abi'u marasa kyau to ya k**ata ka zurfafa bincike a kansa'', in ji shi.
2 - Sauya abokai ko ƙawaye
Wata alamar da za ka iya gane yaronka ya fara ta'ammali da ƙwaya, ita ce ka ga ya sauya abokansa na arziki - da a baya ka san shi da su.
Ko kuma idan mace ce ta sauya ƙawayenta na arziki da ka santa da su, ta koma wasu, ba tare da wata hujja mai ƙarfi ba
''Yau ka ganshi da wannan, gobe ka gan shi da wannan, waÉ—anda kuma ba ka aminta da halayensu ba'', in ji shi.
3) Chanjin tsarin rayuwa
Idan yaro ko yarinya s**a fara shaye-shaye za su sauya yadda s**a saba gudanar da rayuwarsu a cewar jami'in hukumar ta NDLEA.
''Alal misali da 'yarka ko É—anka sun saba yin barci da wuri, sai ka ga yanzu sun dawo ba sa barci da wuri sai lokaci ya ja, ko a baya sun saba ba sa barci da wuri, sai kuma daga baya s**a koma da wuri suke barci, ko kuma sun koma yin barcin a lokacin da ba su saba yi ba''.
''Ko kuma a baya suna tashi barci da wuri, amma sai ka ga yanzu ba su tashi sai lokaci ya ja, to ya k**ata ka zurfafa bincike'', in ji shi.
4) Chanji a cin abinci
Idan yaro ya fara shaye-shaye, cin abinsa ma kan sauya a cewar jami'in na NDLEA.
''Idan a baya ka san ɗanka ko 'yarka ba mai yawan cin abinci ba ce, sai kuma daga baya ka fahimci sun ƙara yawan abincin da suke ci, ko kuma baya suna da yawan ci, amma daga baya s**a rage ci, to nan ma ya k**ata ka bincika''.
5) Yawan ɓatan abubuwa a gida
Yawan ɓatan abubuwa a gida na daga cikin alamun da za ka iya zargin ɗanka ko 'yarka sun fara shaye-shaye, musamman idan ba shi da sana'ar.
"Yau an ajiye naira 50 ko 100 ta ɓata ba a ganta ba a cikin gida, gobe ma haka, to yana da kyau ka binciki 'yayanta'', in ji Abdullahi Sardauna.
Jami'in na NDLEA ya ce abubuwan da yara s**a fi sata a gida domin samun na shaye-shaye sun haɗa da abubuwan amfani, ko sutura ko k**ar sarƙar gwal ko awarwaro masu tsada.
6) Ƙarya
Ƙarya na daga cikin alamomin da za ka gane ɗanka ko 'yarka sun fara shaye-shaye.
''Zai riƙa yin abubuwan da bai saba ba, kuma idan ka tambaye shi zai riƙa yi maka ƙarya, to daga nan ya k**ata ka gane akwai abin da yake ɓoye maka'', a cewar Abdullahi Sardauna.
7) Saurin fushi
Wannan alama ce da za ka iya gane ɗanka ko 'yarka sun fara shaye-sayen miyagun ƙwayoyi.
''Abu kaÉ—an sai ka ga yaro ya fusata yana faÉ—a da abokansa ko da 'yan'uwansa ko da mutanen gari'', in ji Abdullahi Sardauna.
8) Jin haushin jami'an tsaro
Wannan ma wata alama ce da ke nuna cewa ɗanka ko 'yarka sun fara shaye-shaye a cewar jami'in hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyin.
''Za ka ga ko a talbijin ya ga jami'in tsaro, É—an sanda ko wani jami'in, sai ka ga yana fushi da shi, yana yawan zaginsa''.
9) Chanjin k**anni
Idan yaro ya fara shaye-shaye wasu da dama daga cikin k**anninsa za su sauya ba yadda aka san shi ba.
''Idan yaro fari ne , za ka ga ya fara rinewa yana komawa baƙi, fararen haƙoransa za su fara komawa baƙaƙe, fatarsa za ta fara tsagewa, musamman ƙafarsa, hannayensa za su koma baƙaƙe''.
10) Dawowa gida a makare
Na daga cikin alamomin yaro ya fara shaye-shaye ya riƙa dawowa gida a makare ba k**ar yadda ya saba a baya ba.
''Da ya saba da wuri yake dawowa gida, amma yanzu sai ka lura ba ya dawowa sai dare ya fara yi, to ya k**ata ka bincika''.