Mu Koma Karatun Zaure

Mu Koma Karatun Zaure Ta wannan hanya zamu san wasu daga cikin malaman zaure🙏

17/04/2026

Yadda ɗalibin zaure kullum yake cikin rungumar littattafai, yana zuwa gaban malami ya karanta, a ƙara masa sabo, sannan ayi karatun 'yan bayansa tare dashi, matsayin maimaici a gurin sa😍

Kada a haɗa shi da wanda ke zuwa lecture hannu babu komai, a yi darasi kawai ya tashi ya tafi gida.

Banbancin ba ƙarami ba ne.

A ƙarshe kuma Ɗan lecture ne zai futo yana nuna cewa shi malami ne_ Subhanallahi.

Allah ya ganar da mu🤲

✍️ Abubakar Tukur Usman

10/04/2026
10/04/2026

Assalamu Alaikum
Barkan mu da wannan rana ta Juma'a ✨️

Karatun zaure tsari ne na karatu inda dalibi ke dauko littafin da yake son karantawa, ya zo gaban malami ana karantawa t...
08/04/2026

Karatun zaure tsari ne na karatu inda dalibi ke dauko littafin da yake son karantawa, ya zo gaban malami ana karantawa tare da fassara.

Kowane zaure na da nasa tsarin karatu; ana sanya wasu littattafai da dole dalibi ya karanta, sannan kuma kowa na iya zuwa da wanda yake so.

Za mu rika kawo muku tarihin manyan malaman zaure-na baya da na yanzu- tare da sanar da ku inda ake samun karatunsu idan suna samuwa.

Muna fatan za ku yi follow, like, comment da sharing na wannan page. Haka kuma muna rokon ku da ku rika yi mana tag na malaman zaure da kuke bi, musamman na yankinku🙏

07/04/2026

Kuyi mana Tag na malaman zauren da kuke bibiya🙏

07/04/2026

بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على رسول الله صلى الله عليه وسلم

'Yan uwa mun bude wannan page ne domin tuno da yaɗa karatuttukan malaman zaure🙏

Sannan duk malamin da muka samu zamu sanar muku a inda zaku sami karatuttukan sa insha Allah🙏

Allah ya taimake mu ya bada nasara 🙏
Ya sakawa malaman mu da alkhairi🤲

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mu Koma Karatun Zaure posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share