06/05/2026
SHIN OFISHIN 'YAN SANDA NA DRAGON SQUAD DAKE KURNA TASHI ZAI YI KO YAYA?
A safiyar yau Laraba muka samun labarin cewa, ofishin 'yan sanda na "Dragon 🐉 Squads" dake unguwar Kurna Asabe za'a tashe su daga nan a maida su garin Dangwauro dake hanyar Zaria.
Haƙika wannan labari ya matuƙar ɗagawa al'ummar wannan yanki namu hankali, duba da irin amfani, da ƙoƙari, da gudummawar da wannan jami'ai suke bayarwa a wannan yanki da kewaye, ta wurin ɗakile ayyukan ɓata gari, shaye-shaye, faɗan daba, ɓarayi da sauransu. Amma sai dai wani hanzari ba gudu ba wanda mutane basu sani ba shine:-
A bisa tuntuɓa da muka yi, mun samu labarin cewa wannan ofishi ba tashi zai yi ba, illaa, sai dai tsarin aikin da kuma ma'aikatan ne za'a chanza, amma ofishi yana nan a inda yake, hasalima waɗansu jami'an yan sandan da ake yiwa laƙabi da "Anti Kidnapping" za'a kawo nan ofishin, domin suma su bada tasu gudummawar wurin ɗakile ayyukan ɓata gari kamar ko sama da na baya.
Kuma daman mun sani, wannan ba sabon abu bane a tsarin aikin gwamnati, domin a koda yaushe idan aka yi la'akari da waɗansu abubuwa akan iya samun chanji, domin kafin a kawo Dragon ma wasu ne a wajen, amma basu yi kwana biyu ba aka sauya su aka kawo Dragon.
Mun samu labarin cewa waɗanda za'a kawo ɗin har sun zo sun duba wurin, kuma ana sa ran a koda wane lokaci zasu iya fara aiki.
Muna fatan duk waɗanda zasu zo, Allah Ya basu ƙarfin gwiwa wurin yin abinda yafi wanda na baya s**a yi. Allah Ya sa wannan canjin ya zama alkhairi. Aamiin ya Rabbal Aalameen.
Ibrahim Salihu Kurna.
Dan gwagwarmaya.
SHIN OFISHIN 'YAN SANDA NA DRAGON SQUAD DAKE KURNA TASHI ZAI YI KO YAYA?
A safiyar yau Laraba muka samun labarin cewa, ofishin 'yan sanda na "Dragon Operational 🐉 Squads" dake unguwar Kurna Asabe za'a tashe su daga nan a maida su garin Dangwauro dake hanyar Zaria.
Haƙika wannan labari ya matuƙar ɗagawa al'ummar wannan yanki namu hankali, duba da irin amfani, da ƙoƙari, da gudummawar da wannan jami'ai suke bayarwa a wannan yanki da kewaye, ta wurin ɗakile ayyukan ɓata gari, shaye-shaye, faɗan daba, ɓarayi da sauransu. Amma sai dai wani hanzari ba gudu ba wanda mutane basu sani ba shine:-
A bisa tuntuɓa da muka yi, mun samu labarin cewa wannan ofishi ba tashi zai yi ba, illaa, sai dai tsarin aikin da kuma ma'aikatan ne za'a chanza, amma ofishi yana nan a inda yake, hasalima waɗansu jami'an yan sandan da ake yiwa laƙabi da "Anti Kidnapping" za'a kawo nan ofishin, domin suma su bada tasu gudummawar wurin ɗakile ayyukan ɓata gari kamar ko sama da na baya.
Kuma daman mun sani, wannan ba sabon abu bane a tsarin aikin gwamnati, domin a koda yaushe idan aka yi la'akari da waɗansu abubuwa akan iya samun chanji, domin kafin a kawo Dragon ma wasu ne a wajen, amma basu yi kwana biyu ba aka sauya su aka kawo Dragon.
Mun samu labarin cewa waɗanda za'a kawo ɗin har sun zo sun duba wurin, kuma ana sa ran a koda wane lokaci zasu iya fara aiki.
Muna fatan duk waɗanda zasu zo, Allah Ya basu ƙarfin gwiwa wurin yin abinda yafi wanda na baya s**a yi. Allah Ya sa wannan canjin ya zama alkhairi. Aamiin ya Rabbal Aalameen.
Ibrahim Salihu Kurna.
Dan gwagwarmaya