Dangada Youth Awareness Forum - DAYAF

Dangada Youth Awareness Forum - DAYAF Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dangada Youth Awareness Forum - DAYAF, Community Organization, Dangada Cikin Gari, Bagwai Local Government Area, Kano.

29/09/2022

Assalamu alaikhum warahmatullah dafatan kuna lafiya, kamar kowanne sati wannan satinma muna da taro kamar haka.

Rana: Juma'a.
Lokaci: 08:30pm
Wurin Taro: Manhajar WhatsApp.

A mutunta lokaci, ma'ana a tabbatar an halarta akan lokaci hakarta ku tana da matukar muhimmanci "yan kungiya.

Assalamu alaikhum warahmatullah dafatan al'umar mazabar dangada kuna lafiya, bayan nazari an nada jajirtattun matasan da...
24/09/2022

Assalamu alaikhum warahmatullah dafatan al'umar mazabar dangada kuna lafiya, bayan nazari an nada jajirtattun matasan da zasu jagoranci wannan tafiya duba da yadda suke bada gudummawa wajen cigaban wannan mazaba mai albarka.

Duba da cewa nadin na rikon kwarya ne a yanzu an zabi mutane hudu da zasu kula da ofis din da aka tura kowanne kafin lokacin da za'a kara nada wasu domin kulawa da sauran ofis din, ga su kamar haka.

1. Sani Saidu Dangada — Shugaba.
2. Usman Rabi'u Jibaga — Mataimakin Shugaba.
3. Ya'u Hassan Rugar Isau — Maga Takadda.
4. Musbahu Abdullahadi Rabi'u — Jami'in Hulda Da Juma'a.

Muna addu'ar Allah ya basu ikon sauke nauyin da Allah ya dora masu, a shirye shubancin kungiya yake domin karbar shawara ko gyara domin cigaban wannan tafiya.

Bayan kammala wannan nadi na iyayen kungiya da kakan kungiya domin tallafawa wannan tafiya da kuma karfafa mana gwuiwa.K...
24/09/2022

Bayan kammala wannan nadi na iyayen kungiya da kakan kungiya domin tallafawa wannan tafiya da kuma karfafa mana gwuiwa.

Kungiya ta raba wadannan takaddu ga mutanen da aka zaba karkashin jagorancin PRO na wannan kungiya, tabbas yayi kokari shi da "Yan kwamitinsa Kuma sun kammala aikinsu.

Mun samu tarba daga kowanne uban kungiya da muka ziyarta domin bashi takaddar nadin sa da kuma gabatar masa da wannan kungiya, sun bamu shawarwari masu'ana.

Kuma sun shaida mana cewa zasuyi aiki kafada da kafada damu domin kawo cigaba a mazabar dangada gabaki dayanta, sannan sun bamu tabbacin bamu kudummawa dari bisa dari domin kafuwar wannan tafiya.

Muna addu'ar Allah ya yayi riko da hannayenmu a wannan tafiya dama sauran ayyuka da muka sa a gaba na alkhairi.

23/09/2022

Bayan doguwar mahawara a tsananin membobin wannan kungiya mun amince da nada mutane goma sha daya a matsayin patrons da grand patron, domin bamu gudummawa da kuma karfafa wannan tafiya.

Kasancewar aikin da muka dauko ba aiki ne mai sauki ba, muna bukatar mutane masu kishi domin bamu gudummawa ta shawarwari,lokaci da sauran abubuwan da s**a kamata.

Allah ya basu ikon sauke wannan nauyi, mutanen sune kamar haka.

1.Alhaji Haruna Musa Dangada — Grand Patron.
2. Alhaji Aminu Rabi'u Turaki — Patron.
3. Alhaji Alkasim Nuhu — Patron.
4. Alhaji Haruna Mato — Patron.
5. Alhaji Muttaka Habibu — Patron.
6. Malam Salisu Iliyasu (Mai Kudi) — Patron.
7. Alhaji Tafida Aminu — Patron.
8. Doctor Sagiru Rabo Dahiru — Patron.
9. Malam Sh*tu Abdullahi —Patron.
10. Malam Shu'aibu Salisu — Patron.
11. — Patron.

23/09/2022

Assalamu alaikhum warahmatullah dafatan "yan'uwana kuna lafiya, wannan shine sahihin shafin wannan kungiya, kuma an kafatane domin wayar da kan matasan mazabar dangada gabaki daya.

Muna neman goyan bayanku da shawarwari domin baza mu iya mu kadai ba.

Allah muke roko ya Sanya mana hannu akan wannan tafiya.

Address

Dangada Cikin Gari, Bagwai Local Government Area
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dangada Youth Awareness Forum - DAYAF posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Dangada Youth Awareness Forum - DAYAF:

Share