01/04/2026
AURE YA WUCE YADDA KUKA DAUKA:
Matasa da yawa suna tunanin idan sun samu 500k na Sadaki, s**a hada Lefe, s**a k**a haya inda zasu zauna shikenan lissafin Aure ya kare. To ba haka bane, Akwai abubuwan da ake boye muku wanda duk abubuwan da na lissafa ba su bane masu wahala in dai Aure ake magana...
Kafin ka sanya kafar wando daya da rayuwar aure, dole ne ka hadiye wadannan danyen gaskiyar guda 6:
1. ZABIN MACE: Babban tashin hankalin shine idan ka tashi auren, shin wace irin mace zaka aura? Daga ranar da kayi Aure, kashi 80% na rayuwarka, natsuwarka, da lafiyar kwakwalwarka yana hannun matar da ka aura. Shin wacce irin ka aura? Mai gina rayuwa ko wacce zata rushe rayuwarka, ta asirta asirinka a waje, kuma ta mayar da kai ba komai ba?
2. LISSASAFIN KUDI A BOYE: : Kafin ka yi Aure kasan san unexpected ko hidden bills kuwa? Abinci, cefane, kudin asibiti (musamman idan ciki ya shiga), kudin madara, kudin pampers, kudin makarantar yara, kudaden da ake kashewa a gudanar da gida... Wannan ba lissafin albashin N30,000 ba ne wanda zaka ci ka watsar. Injin kawo kudi kake bukata, ba jiran wata ba.
3. HAKURI DA IYON JURE FUSHI: Mace zata bata maka rai dari-bisa-dari har ka ji k**ar ka hadiye ta. Idan kai irin namijin nan ne mai saurin fushi, mai duka, ko mai yawan zagi... wallahi aurenka ba zai wuce wata shida ba. Asalin kwarjinin Namiji shine ikon yin shiru a lokacin da yake da ikon yin ihu. Wannan wata jarabawa ce ta daban.
4. KARE IYAKOKIN GIDA: Daga ranar da ka daura aure, dole ne ka koyi cewa "A'A" ga danginka da kawayenta masu son tsoma baki a cikin gidanka. Idan baka da tsaurin zuciyar kare sirrin matarka da hana waje gudanar da gidanka, aurenka zai ruguje a idonka kana kallo.
5. JAGORANCIN ADDINI: Kai ne Limamin gidan, Allah ba zai tambaye ka iya shinkafar da ka ciyar da su ba kawai, Zai tambaye ka tarbiyyarsu. Idan baka san yadda zaka koya wa matarka da 'ya'yanka sallah da tsoron Allah ba, kiyamar zango zaku tashi. Gidan da babu Allah, asibitin mahauta ne.
6. HAKKIN KWANCIYA DA NATSUWAR RUHI: Aure ba zallar cin abinci ba ne. Matarka tana bukatar lokacinka, sauraron kuka da korafinta, da kuma kulawa ta jiki wato Hakkinta na kwanciya. Idan baka da lafiyar jiki ko baka da lokacin sauraronta, zata tsane ka koda kana raba mata miliyoyi a kullum.
Aure Ibada ne, amma idan baka bi a hankali ba zai iya zama sanadiyar rugujewar rayuwarka. Sannan idan baka sauke hakki ba, Allah zai k**a ka da laifi a gobe kiyama.
Dan Allah matasa mu daina gaggawar cika daki babu tsari. Mu gyara kanmu kafin mu dauko diyar mutane.
Allah yasa mudace.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️