Ballah DAWO DAWO media

Ballah DAWO DAWO media Introduction
The Ballah Dawo-Dawo 2027 Movement was established to highlight the work, contributions,

🇳🇬 HAPPY INDEPENDENCE DAY, NIGERIA 🇳🇬A yau, 1 ga Oktoba 2026, muna taya al’ummar Najeriya murnar cika shekaru 66 da samu...
01/10/2026

🇳🇬 HAPPY INDEPENDENCE DAY, NIGERIA 🇳🇬

A yau, 1 ga Oktoba 2026, muna taya al’ummar Najeriya murnar cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai.

Muna addu’ar Allah Ya ƙara wa Najeriya zaman lafiya, haɗin kai, ci gaba da wadata. Mu ci gaba da kasancewa masu kishin ƙasa tare da gina Najeriya mafi inganci domin al’umma da tsararraki masu zuwa.

Allah Ya albarkaci Najeriya 🇳🇬🤲🏾
Happy 66th Independence Anniversary!

— Hon. Ibrahim Umar Ballah
Dan Takarar Majalisar Tarayya, Kumbotso
NDC

BALLAH DAWO-DAWO MEDIA – Muryar Kumbotso

29/09/2026

Nasara dai

29/09/2026

Yaron guduwa yayi kafin akara zaman

Daga ChiranciA yau, Lahadi 13/09/2026, ɗan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Ibrahim...
13/09/2026

Daga Chiranci

A yau, Lahadi 13/09/2026, ɗan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Ibrahim Umar Ballah, tare da ɗan takarar Majalisar Jiha, Hon. Nafi’u Garba Aliyu, na jam’iyyar NDC, sun ziyarci mazabar Chiranci domin halartar ɗaurin aure da aka gudanar a wannan mazaba.

Muna roƙon Allah Ya sanya albarka a wannan aure, Ya ba ma’auratan zaman lafiya da haƙurin zama juna.

Bukhari Ashafa

-dawoMedia

🤝 ZAMA NA MUSAMMANHon. Ibrahim Umar Ballah ya gana da Alh. Ado Rodi, inda s**a tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi ...
13/09/2026

🤝 ZAMA NA MUSAMMAN

Hon. Ibrahim Umar Ballah ya gana da Alh. Ado Rodi, inda s**a tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi siyasa, ƙarfafa alaƙa da haɗin kai, da kuma hanyoyin da za su taimaka wajen ƙara tabbatar da nasarar Jam’iyyar NDC da tsarin Kwankwasiyya a Mazabar Dan Miliki, Karamar Hukumar Kumbotso da Jihar Kano baki ɗaya.

Allah Ya tabbatar mana da nasara, Ya ba mu rabo mai amfani ga al’ummar Kumbotso. 🤲🏾

Source: Bukhari Ashafa





SAƘON GOYON BAYAN ‘YAN APC A KUMBOTSOA kafafen sada zumunta, ana ci gaba da ganin wasu daga cikin mabiya jam’iyyar APC a...
03/09/2026

SAƘON GOYON BAYAN ‘YAN APC A KUMBOTSO

A kafafen sada zumunta, ana ci gaba da ganin wasu daga cikin mabiya jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Kumbotso suna bayyana goyon bayansu ga ‘yan takarar jam’iyyar NDC na Majalisar Tarayya da Majalisar Jiha a zaɓe mai zuwa.

Abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda comments da martanin jama’a ke ƙara nuna sha’awa, goyon baya da ƙwarin gwiwa ga wannan tafiya.

Lokaci ne na haɗin kai, fahimtar juna da sabon fata. 🤝🏾

Allah Ya tabbatar da alheri, Ya ba mu nasara mai amfani ga al’ummar Kumbotso. 🤲🏾

magoya baya karuwa suke naboye Dana fili zamuyi nasara da yardar Allah BALLAH DAWO-DAWO
02/09/2026

magoya baya karuwa suke naboye Dana fili
zamuyi nasara da yardar Allah

BALLAH DAWO-DAWO

01/09/2026

hon. Ibrahim Umar ballah

MUHIMMIN ZAMA A ABUJA 🇳🇬A ranar 31/08/2026, His Excellency Peter Obi, ɗan takarar Shugabancin Ƙasa na NDC, da His Excell...
01/09/2026

MUHIMMIN ZAMA A ABUJA 🇳🇬

A ranar 31/08/2026, His Excellency Peter Obi, ɗan takarar Shugabancin Ƙasa na NDC, da His Excellency Sen. Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa a gidansa da ke Maitama, Abuja, domin tattauna shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe mai zuwa.

Ganawar ta samu halartar Hon. Ibrahim Umar Ballah, ɗan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Kumbotso Federal Constituency, tare da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

Allah Ya tabbatar da alheri da nasara. 🤲🏾

🟢 TARON BALLAH SUPPORT GROUP (BSG)30 ga Agusta, 2026BALLAH SUPPORT GROUP (BSG) ta gudanar da wani muhimmin taro da ya ha...
31/08/2026

🟢 TARON BALLAH SUPPORT GROUP (BSG)

30 ga Agusta, 2026

BALLAH SUPPORT GROUP (BSG) ta gudanar da wani muhimmin taro da ya haɗa jagorori da wakilan ƙungiyar, domin ƙarfafa haɗin kai, tsari da dabarun tafiyar siyasa gabanin zaɓe mai zuwa.

An jaddada muhimmancin sadaukarwa, biyayya, aiki tare da wayar da kan al’umma cikin lumana, tare da inganta sadarwa tsakanin shugabanni da wakilan ƙungiyar.

BSG na ci gaba da gina ƙarfi bisa haɗin kai da aiki tukuru. Nasara da haɗin kai ne! 🤝🏾💪🏾




Address

Kumbotso Near Microfinance Bank
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ballah DAWO DAWO media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share