Aikawa charity foundation

Aikawa charity foundation gidauniyar tallafawa raunana da marayu, ginin masAllatai da makarantu da sauransu

KUN TUNA WANNAN YARINYAR 😭😭😭Itace wacce naje gidansu na tarar tanacin tsakin gari saboda, rashin Abinci. Su 9 ne mata aw...
17/05/2026

KUN TUNA WANNAN YARINYAR 😭😭😭

Itace wacce naje gidansu na tarar tanacin tsakin gari saboda, rashin Abinci.

Su 9 ne mata awurin mahaifiyarsu.

Akwai daya, acikin yaran shekarar ta daya tana kwance zaayi mata Operation akan ₦680k an rasa kudin.

Sannan an tashesu daga gidan da suke haya basusan inda zasu nufaba.

Mun kai musu tallafin abimci da kudi da safe.

Yanzuma mun kai wani abincin da dare.

Sannan mun biya, kudin aikin,

Likitan ya amince zai karvi ₦550k, mun biyashi kudinsa.

Yanzu dai gidan haya muke nema.

Idan kuma mun samii yadda mukeso Allah yasa mu siya, musu gida.

WAllahi munji dadi yaran sai murna suke.

Allah ya, hadamu a ladan.

✍️✍️✍️✍️
Sani Rogo Aikawa

CEO Aikawa charity foundation

08082744019

SAURA KADAN AFASA AUREN😭😭😭.NA AURAR DA "YA TA 63🤣🤣🤣🤣.kusan watanni biyu wata mata wacce ban saniba take kirana cikin kuk...
16/05/2026

SAURA KADAN AFASA AUREN😭😭😭.

NA AURAR DA "YA TA 63🤣🤣🤣🤣.

kusan watanni biyu wata mata wacce ban saniba take kirana cikin kuka tana cewa in ceto RAYUWARTA sau shida ana Saka ranar auren kanwarta ana fasawa saboda su marayune Babu uwa babu uba Kuma basuda KOMAI SABODA kuncin rayuwa.

Dangin mijin sunce daga wannan karon sai dai AFASA AUREN.

Duk sanda mukayi Kuka take itada kanwarta marainiya wato amarya.

HAR ASABAR daga gabata bamuda komai kuma LAHADI daurin Aure.

Tun safe na futa inyi Nan inyi chan inata fafutuka.

Saboda sauri rigar barcice a jikina 🤣🤣

Katifa nafara siye nakira Wani yabada labulaye Wani kayan kitchen Wani gado Wani kwaba da haka da haka dai muka tattara mata kayanda ko amarya wacce mahaifata ke raye wata bata samuba.

Ni dasu mukayita yawon NEMAN mafita ko yawon biki baayiba.

Shago shago muka dinga shiga dasu s**a zabi kayan da kansu.

Aradun ALLAH JIKINA YA GAYAMUN🤣🤣🤣🤸🤸🤸.

Allah SARKI amarya da yayarta sai kukan MURNA.

AMARYA TA DURKUSA HAR KASA TACE NAGODE BABA🤸🤸🤣🤣🤣🤣.

Ashe har nazama BABA.

ALLah yabada zaman lafiya.

Insha Allah zamu bita da kayan Sanaa har gida Nan da kwanaki.

NAJI DADI WALLAHI.

🙏🙏.
DON ALLAH MU DINGA Agazawa MARAYUN amare wallahi akwai matsala.

ALLAH YA DAFA MANA SABODA MATSAYIN ANNABI MUHAMMADU SAW.

SANI ROGO AIKAWA
AIKAWA CHARITY FOUNDATION.
08082744019

11/05/2026

MASHA ALLAHU😭😭😭.

mun kirawo uwar marayunnan wacce suke kwana da, yunwa suna kuka itada yaranta.

Basa zuwa makaranta, ga rayuwar tayi musu zafi.

Itace mai marayun da sun kasa samun mai agazawa, rayuwarsu.

Wallahi a office dinmu s**a karya, bayan sun shafe tsawon lokaci suna tafiyar kasa, saboda rashin kudin mota.

Mun fara bata agajin ₦60k.

Ga wanda, keda agajin kayan Abinci, ko siya mata, keken dinki, ko kuma daukar dawainiyar karatun yaran to zai iya tuntubata.

👇👇👇

08082744019.

Kira ko wathasp.

ALHAMDULILLAH. wannan itace fatima katsina, wacce keda, larurar idanu. Wacce bata gani da rana, idanunta suke shirin mak...
09/05/2026

ALHAMDULILLAH.

wannan itace fatima katsina, wacce keda, larurar idanu.

Wacce bata gani da rana, idanunta suke shirin makancewa.

Itace wacce aka nemi kudin aiki ₦427,000. Kusan shekara daya baa samuba.

Cikin ikon Allah anyi aikin idon farko, saura guda dayan.

Har ganinta ya dawo na guda dayan.

Saura dayan shima ana shirin shiga da ita aikinsa.

Allah ya sakawa dukkan wadanda s**a tallafa da Alheri.

Allah ya hadamu a, ladan.

✍️✍️✍️
AIKAWA CHARITY FOUNDATION.

08082744019.

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN. Allah yayiwa baiwar Allahn nan mai famada ciwon mama rasuwa. Wacce aka nemi kudin All...
09/05/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN.

Allah yayiwa baiwar Allahn nan mai famada ciwon mama rasuwa.

Wacce aka nemi kudin Allurai kusan naira miliyan goma sha biyu domin ceto rayuwarta..

Har mun fara siyen Allurai sai jikinta yayi tsanani, Allah ya, karbi abinsa.

Ta, rasu tabar yara mata guda biyar.

Munje mun kai tallafin kudi naira dubu dari da Abin sanaa dakuma kayan Abinci.

Allah ya gafarta mata ya, kyautata, makwancinta.

Allah ya sakawa dukkan wadanda s**a taimaka da Alheri.

✍️✍️✍️
AIKAWA CHARITY FOUNDATION

08082744019.

mASHA ALLAH. Wannan itace rijiya ta 700 da muka kammala fisabilillahi don Amfanin bayin Allah. Allah ya sakawa masu taim...
08/05/2026

mASHA ALLAH.

Wannan itace rijiya ta 700 da muka kammala fisabilillahi don Amfanin bayin Allah.

Allah ya sakawa masu taimakawa da Alheri.

Allah ya hadamu a ladan baki daya.

✍️✍️✍️
Aikawa charity foundation .

08082744019.

AI SHIKENAN😭😭😭😭😭DUkkanninsu iyayen marayune, kowacce cikin kuka take kirana tana neman a taimaki rauuwarta itada marayun...
05/05/2026

AI SHIKENAN😭😭😭😭😭

DUkkanninsu iyayen marayune, kowacce cikin kuka take kirana tana neman a taimaki rauuwarta itada marayunta.

Bamuda kudi a foundation, wallahi takai kadaminda har rance muke domin ceto rayuwar iyayen marayu dakuma marayunsu.

Dukkansu so suke suyi ƙaramar sanaaa domin dogaro da, kansu.

Wallahi muji tsoron Allah, saboda makota fs yawa sun kauda, kansu ga taimakon marayunsu.

Allah ya bamu juriya.

✍️✍️✍️✍️
Sani Rogo Aikawa

CEO Aikawa charity foundation

08082744019.

ALLAH SARKI RAYUWA.Yaronnan da ya ƙone, ake rasa kuɗin aikinsa da dawainiya da  kayan diresin da abinci.Anyi aiki cikin ...
27/04/2026

ALLAH SARKI RAYUWA.

Yaronnan da ya ƙone, ake rasa kuɗin aikinsa da dawainiya da kayan diresin da abinci.

Anyi aiki cikin nasara.

Mun kirasu har office, an siyo dukkan magunguna sun sami kulawa ta musamman.

Mun danƙa musu naira dubu ɗari a hannu, sai yakama murna da farin ciki yana cewa, umma kuɗi, umma kuɗi.

Munji daɗi kwarai da gaske.

Ubangiji kaci gaba da farantawarmu saboda Alfarmar Annabi muhammadu saw.

✍️✍️
SANI ROGO AIKAWA.

CEO AIKAWA CHARITY FOUNDATION.

08082744019.

WAYE ZAI CECI RAYUWAR AMINA? 😭😭😭😭. Amina budurwace mai shekaru 17, yau kusan shekara daya wasu ciwuka s**a fito ajikin n...
25/04/2026

WAYE ZAI CECI RAYUWAR AMINA? 😭😭😭😭.

Amina budurwace mai shekaru 17, yau kusan shekara daya wasu ciwuka s**a fito ajikin nononta. Tsawon shekara daya an rasa kudin da zaa cire mata wannan kari dake jikinta.

Yanzu haka jikinta yayi zafi, domin kwana take tana kuka saboda azabar ciwo.

Kullum haka takesa mahaifiyarta gaba tana kuka tareda zubarda hawaye saboda ciwon yaci karfin jikinta.

Yau mun kaita asibiti likitoci sun tabbatar abin yana neman ya zama dancer mama idan baayi aikin da wuriba.

Zaayi mata aikin akan ₦150,000, sannan akwai gwajin karin da zaayi akan ₦17k.

Don Allah indai da ikon agaxa mata to ga Aikin Allah a daure a tausayawa rayuwarta.

Zaayi mata operation ranar litinin 27/4/2026.

Idan akwai wanda keson ganinta da idonsa, ko kuma yakeson a hadashi da likitin da zai mata aikin, ko kuma wani karin bayani akira 08082744019 kira ko wathasp.

Zaa iya zuwa office dinmu dake unguwar goron dutse, no 15 Aminu kano way.

Domin ganinta ido da ido.

Ga masu niyyar agaxawa ko tausayawa, ga inda zamu agaxa don aje ayi aikin ranar litinin insha Allahu.

👇👇👇

*00-12---95--09---08---
J""""""A******I********Z
AIKAWA CHARITY FOUNDATION.

DON ALLAH A DUBI RAYUWAR AMINATU.

A TAIMAKEMU DA SHARE.

✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Aikawa charity foundation.
08082744019.

INNALILLAHI😭😭😭😭😭LAmarin ya girgizamin zuciya. Wata baiwar Allah ce ke famada matsalar koda. Tazo asibiti babu kudin wank...
24/04/2026

INNALILLAHI😭😭😭😭😭

LAmarin ya girgizamin zuciya.

Wata baiwar Allah ce ke famada matsalar koda.

Tazo asibiti babu kudin wankin kodar, sai ta juya zata koma gida ta siyarda tsohuwar katifarta da take jinya😭😭😭😭

Wata yayata dake aikin asibitin ce ke sanar dani.

Dana tambayi nawane kudin wankin sai akace ₦20k.

Abinda yabani tausayi da mamaki shine, shin da bansaniba sai dai ta koma gida kenan a kafa? 😭😭😭😭.

Baa gama ba, fa akwai ragowa masu yawa?

Shin yaya zatayi da na gaba😭😭😭

Idan akwai wanda zai dauki ɗawainiyarta ya tuntubeni in hadashi da ita.

✍️✍️✍️✍️✍️
Sani Rogo Aikawa

CEO Aikawa charity foundation

08082744019..

MASHA ALLAH. Mun biya, kusan naira dubu dari uku da talatin kudin gwaje gwajen Hawau, wacce s**ayi accident da mahaifiya...
21/04/2026

MASHA ALLAH.

Mun biya, kusan naira dubu dari uku da talatin kudin gwaje gwajen Hawau, wacce s**ayi accident da mahaifiyarrta tasami matsalar laka.

Insha Allah muna jiran fitowar kudin aiki, wanda zai iya haura naira miliyan biyu.

Allah ya, kawo mafta, ya sakawa masu taimakawa da alheri.
✍️✍️✍️✍️

08082744019.

Address

No 15 Aminu Kano Way Goron Dutse Kano. Opposite Sheikh Ishaka Rabiu Mosque
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aikawa charity foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share