07/07/2026
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) Ta Yi Allah-Wadai Da Ware AREWA MASO YAMMA Daga Aikin Gina Hanyoyi Na Naira TIRILIYAN 3.9 Da Gwamnatin Tinubu Ta Yi.
Ƙungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) ta yi Allah-wadai da matakin Gwamnatin Tarayya na amincewa da ayyukan gina hanyoyin tarayya guda 27 da s**a kai darajar sama da Naira tiriliyan 3.9 a jihohi 15, yayin da aka bar dukkan jihohi bakwai na Arewa maso Yamma ba tare da ko aikin hanya guda ba.
Ƙungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin nuna wariya da cin amanar yankin da ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023, inda ta ce Arewa maso Yamma ce ta ba shugaban ƙasa mafi yawan ƙuri'u tare da ba APC cikakken goyon baya.
CNG ta nuna damuwa cewa duk da kasancewar yankin na da manyan hanyoyin da ke da matuƙar muhimmanci ga noma, kasuwanci, masana'antu da tsaron ƙasa, babu ɗaya daga cikinsu da aka haɗa cikin sabbin ayyukan. Ta kuma yi nuni da cewa har yanzu ba a kammala aikin hanyar Abuja–Kaduna–Kano ba, duk da yawan haɗurra, sace-sacen mutane, hare-haren 'yan bindiga da kuma asarar tattalin arziki da matafiya ke ci gaba da fuskanta a wannan hanya.
Ƙungiyar ta ɗora alhakin wannan rashin daidaito kai tsaye a kan Shugaba Tinubu, tana mai cewa shugabanci na gaskiya ya k**ata ya kasance bisa adalci da daidaito, ba fifita wasu yankuna tare da watsi da wasu ba.
Haka kuma, CNG ta soki shirun manyan shugabannin siyasa daga Arewa maso Yamma, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati daga yankin, tana mai cewa suna bin al'ummarsu bashin bayani kan dalilin wannan rashin adalci.
A ƙarshe, CNG ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta sake duba rabon ayyukan hanyoyin domin haɗa jihohin Arewa maso Yamma, tare da gaggauta kammala aikin hanyar Abuja–Kaduna–Kano da kuma fara sabbin ayyukan manyan hanyoyin yankin. Ƙungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da yaƙi da duk wani nau'in nuna wariya tare da kare muradun al'ummar Arewa bisa adalci da daidaito.
Sa Hannu
Comr Jamilu Aliyu Charanci
National Coordinator
Coalition of Northern Groups (CNG)