17/03/2022
MUHIMMANCI_____LOKACI
Da yawanmu ba mu san mahimmancin lokaci ba, inda za ka lura da masu wasan tseren ɗauka-sauke za ka ga kowa nasara yake son ya ci, amma dole ya san me zai yi, kuma cikin minti nawa? Dole ya yi ƙoƙarin kammala duk zagayen nan a cikin 'yan mintocin da yake da su, in ba haka ba komai ƙoƙarinsa a banza ne yake yi, ma'ana ya riga ya saki hanyan nasara kenan, a addini ma za ka ji ana cewa yi kaza kafin kaza ya same ka, shi ya sa a darussan baya muka ce 'yan siyasammu da za su yi shekaru ƙasa da huɗu su sauka, me s**a iya yi wa jama'a wanda zai lamunta musu dawowarsu?
In kuma waɗanda dawowar da ma da wahala kamar kansiloli, me s**a yi wanda zai lamunta musu damar shiga takarar shugaban ƙaramar hukuma? In kuma mai koyon sana'ar hannu ne shekara nawa kake zaton za ka yi? Shin waɗannan shekarun sun isheka ka gwanance? Ka fara samun waɗanda in ka bar wannan wurin za su biyo ka duk inda kake saboda jin daɗin aikinka? In ba haka ba ne to ka sake lissafi, kai za ka ƙiyasta lokacin da kake son ka yi, sai in asali dama yanayin sana'ar a ƙiyasce lokacinta yake, ko kuma sai maigidanka ya sallame ka.
Duk da haka, kana da damar da za ka ɗiba wa kanka shekarun da kake buƙatar ka zama wani abu a fagen, yadda wasu masu buƙatar aikin da kuke yi ba sa iya sakewa da kowa sai kai, mutumin da nasara ke gabansa zancen hutu kowani lokaci ba nasa ba ne gaskiya, shi ma yana cikin tsarin da ya ɗiba wa kansa, lokacin aiki daga kaza zuwa kaza, zumunta lokaci kaza, abokai lokaci kaza, in bai yi aure ba ƙila yana da lokaci kaza don wace zai aura, in kuma ya yi to iyalin nasa na buƙatar lokaci kaza, sai an haɗa da haka don zomo ba ya kamuwa daga zaune, in dai ba za ka shigar da hutu lokacin aiki ba, to bai dace aiki ya riƙa shiga lokacin hutu ba, tsari yana da amfani.
Mukan ce wane ɗan boko ne, amma za ka taras ya fi kowa jin daɗin rayuwarsa saboda irin tsarin da ya yi, kasuwanci ko aikin ofis ko na masana'anta ko ma'aikata ko wata sana'ar hannu duk suna buƙatar lokaci, in