07/10/2024
TALLAFAWA ILIMI TUN DAGA TUSHE A AREWACIN NAJERIYA..
Daga Gidauniyar You vs You Foundation
A kokarin ta na tallafawa ilimi, Gidauniyar You vs You ta kaddamar da soma rabon littafai ga daliban Makarantun primary a Arewacin Najeriya.
Ma'assasi kuma Jagoran wannan Kungiya Ahmed Mohammed tare da rakiyar chairman na Kungiyar Mubarak Musa da sauran membobin kungiyar sun fara da ziyartar Makarantar Hotoro South Special Primary School Wadda take karkashin Karamar hukumar Nasarawa a Jihar Kano, karkashin Shirin Gidauniyar Mai suna ASPIRE PROJECT Wanda Insha'Allahu zamu kewaya Makarantu da nufin ba da tallafin Littafi, pencils, chalkboard, Uniform da ma ababan zaman dalibai (Benches).
Muna farawa da Sunan Allah, domin yayi mana Jagoranci bisa wannan aiki da muka fara.
A madadin wannan Kungiya Muna jinjina ga shi Shugaban wannan gidauniya El-ahmed Moh'd bisa jajircewa da kuma tsayawa tsayin daka don ganin wannan project ya samu nasara. Ba zamu gushe ba sai mun yabawa members na wannan Kungiya a karkashin Jagoranci Chairman Ustazu Mubarak Musa bisa sadaukarwar su Babu dare Babu rana.... Allah Ubangiji Ya sanyawa kowa cikin ayyukan sa na alkhairi.
Allah Ya taimaki wannan Kungiya Ya daga darajarta da Mutanen cikinta.
Signed by
Mubarak Musa
Chairman You vs You Foundation