Maitama Charitable and Educational Foundation

  • Home
  • Maitama Charitable and Educational Foundation

Maitama Charitable and Educational Foundation This is the official page of Ibadurrahman Foundation For Da'awah & Human Development.
(1)

Khudbah Mai Taken:  Kiyaye  HarshePROF. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo OON.Daga Masallacin Al Muntada Dorayi kanoDomin ...
29/05/2026

Khudbah Mai Taken: Kiyaye Harshe
PROF. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo OON.
Daga Masallacin Al Muntada Dorayi kano
Domin samun wannan hudubar sai ya bibiyi link din shafi malam a comment section 👇

Yana da kyau Al'ummar su son ciwon kansu saboda ba zaka taba ganin yan kudu suna s**an pastor kawai dan shi pastor ne ba...
28/05/2026

Yana da kyau Al'ummar su son ciwon kansu saboda ba zaka taba ganin yan kudu suna s**an pastor kawai dan shi pastor ne ba. Wallahi ire Irene su sheik pantami Ko da suna da kuskure sun fi yan siyasarmu da muke dasu. Allah ganar da Al'ummarmu ta san ciwon kanta

Professor Pantami shi kansa jam’iyya ne mai zaman kansa.Kuma duk inda ya tsaya takara, darajar jam’iyyar ne zai ƙaru, ku...
25/05/2026

Professor Pantami shi kansa jam’iyya ne mai zaman kansa.

Kuma duk inda ya tsaya takara, darajar jam’iyyar ne zai ƙaru, kuma za'a samu nasara da izinin Allah, domin tabbas za'a samu shugabanci na gaskiya, riƙon amana, da aiki tukuru, In Sha Allah.

Pantami ya kasance ɗaya daga cikin fitattun mutanen da s**a taimaka wajen sauya Najeriya daga dogaro da man fetur kaɗai zuwa bunƙasa tattalin arzikin zamani. Mutum ne mai ƙwarewa da babu jihar da za ta so ta rasa shi.

Na kalli wani bidiyon ɗan takarar da gwamnan gombe ya tsayar yana cewa Pantami mutum ne da ya yi aiki matuƙa a lokacin da yake Minista, kuma ƙwararre ne.

Haka abin yake. Duk adawarka da shi, ka san mutum ne da yasan aiki, mutum ne mai ilimi, mutum ne da In Sha Allah idan ya hau kujera a Najeriya, zai bar legacy.

Waɗanda ma ba ’yan Gombe ba, suna son Professor ya zama gwamnan Gombe saboda sun san zai zama fitilar da zata haskaka sauran jihohi.

Muna sonka, muna alfahari da kai Professor. Allah Ya ba ka nasara.🥰❤️

Copied.

24/05/2026
Faydha in Focus: A Scrutiny of Inya's BeliefBabban Malaminmu Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo (Hafizahullah) ya rubuta littaf...
08/05/2026

Faydha in Focus: A Scrutiny of Inya's Belief

Babban Malaminmu Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo (Hafizahullah) ya rubuta littafinsa mai suna:

هذه هي الفيضة: إنياس وآراؤه في الميزان

Mohammad Qaddam Sidq Isa ya fassara shi zuwa Turanci, bayan bibiya tare da dubawa daga Malam, sannan bisa sahhalewa daga gare shi, an buga wannan Littafi domin amfanuwar al'umma musamman ƴan boko masu karsashin yin karatu cikin harshen Turanci da kuma su kansu asalin turawan. Allah Ya saka wa Malam da alheri mai girma Allah Ya ƙara masa lafiya Ya tsare shi.

Ga masu buƙatar wannan littafi, su yi gaggawar tuntuɓar wannan lamba: (+2348166176663).

NB: Don Allah a yi hakuri, iya lambar can da aka bayar ta sama za a tuntuɓa a kan wannan littafi zuwa yanzu. Idan da wata sabuwar sanarwar za a gani zuwa gaba.

Musa Muhammad Dankwano.
Sakataren Kwamitin Ilimi na Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo.
08-05-2026.

Khudbah Mai Taken:Sako Zuwa ga ‘Yan SiyasaPROF. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo.Daga Masallacin Almuntada Dorayi Kano.
08/05/2026

Khudbah Mai Taken:
Sako Zuwa ga ‘Yan Siyasa
PROF. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo.
Daga Masallacin Almuntada Dorayi Kano.

30/04/2026

Ban taba ganin gida irin wannan ba.

Shaik abubakar umar rijiyar lemo
Shaik prof sani umar rijiyar lemo
Shaik Dr rabiu umar rijiyar lemo
Shaik mahamud umar rijiyar lemo

Yam gida daya duk malamai. Kuma uwa daya uba daya, yayin ziyarar sallah a gidan su na family, Allah ya kara musu lapia da imani.

AURAN GATA ANGO DA AMARYA (3000)Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf za ta gudanar da wani s...
29/04/2026

AURAN GATA
ANGO DA AMARYA (3000)

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf za ta gudanar da wani shiri na musamman na aurar da zawarawa da ’yan mata dubu uku (3,000), wato maza 1,500 da mata 1,500.

Wannan shiri ya fi karkata ne ga marayu da kuma ’ya’yan talakawa domin tallafa musu su samu rayuwa mai inganci ta hanyar aure.

Abubuwan da aka tanada ga ma’auratan sun haɗa da:
1. Kayan ɗaki: gado, sif, madubi, katifa, filo da zanin gado.
2. Kayan abinci: shinkafa, taliya, da man girki.
3. Kayan sawa ga mata: atamfa da hijabi.
4. Kayan sawa ga maza: shadda da hula.
5. Sadaki: Naira dubu ɗari (₦100,000).
6. Jari ga mata: Naira dubu ɗari (₦100,000) domin fara sana’a.

Haka kuma, za a gudanar da gwajin lafiya tare da cike takardun (forms) guda uku domin tabbatar da cewa duk wanda zai shiga shirin ya cika dukkan sharudda.

Ƙarin bayani
(Duk wanda zai shiga wannan shiri sai yana da sanaa.)

Allah ya saka wa gwamna da alkhairi, ya sanya wannan aiki ya zama alheri mai ɗorewa ga al’umma, ya kuma sa ya zama sanadin rage talauci da inganta zaman lafiya a jihar Kano.

Yi Ƙokari ka Mallaki na ka a Kan Lokaci!Wannan Littafi mai albarka na babban Malaminmu Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo (Hafi...
28/04/2026

Yi Ƙokari ka Mallaki na ka a Kan Lokaci!

Wannan Littafi mai albarka na babban Malaminmu Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo (Hafizahullah) yanzu haka ya iso zuwa ga al'umma daga birnin Misra. Domin mallakar naka, sai ka tuntuɓi: Kamfanin buga littattafai na Darul Hikma, Kurmi, Kano. Ga lambobin wayar shugaban kamfanin 08028400757- 08034324485.

Allah Ya saka wa Malam da alkhairi Ya ƙara masa lafiya da imani. Haƙiƙa yana da matukar kyau malamai da masu da'awa da ɗaliban ilimi su yi gaggawar mallakar wannan littafi mai matuƙar muhimmanci. Sannan a karantar da shi ga sauran al'ummar musulmai.

Musa Muhammad Dankwano.
Sakataren Kwamitin Ilimi na Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo (Hafizahullah)
28-04-2026.

26/04/2026

Duk masoyinAnnabi S A. ya rubuta ko ya fadi S. A W.

Address

Salanta

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Maitama Charitable and Educational Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Maitama Charitable and Educational Foundation:

  • Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization?

Share