30/03/2026
Sunayen Tituna a Kafanchan: Tarihin Hadin Kan Najeriya a Zuciyar Masarautar Jama’a
Ko kun taba lura cewa sunayen tituna da hanyoyin cikin garin Kafanchan suna dauke da babban tarihi da darasi kan hadin kan kasa?
A cikin garin, akwai tituna masu sunaye daga sassa daban-daban na Najeriya, abin da ke nuna yadda Kafanchan ta dade da zama cibiyar kasuwanci, sufuri da cudanyar al’adu.
A bangaren Arewa, akwai tituna irin su Kano, Kaduna, Katsina, Sokoto, Borno, Bauchi, Bida, Zariya, Funtua, Soba, Bebeji, Jama’a, Jos, Hadeja, Adamawa, Jagindi da Wamba. Wadannan sunaye na nuna alakar tarihi da zamantakewa tsakanin Kafanchan da sauran yankunan Arewa.
A bangaren Yamma, tituna kamar Ibadan, Ogbomosho da Legas na tuna mana da tsohuwar alakar kasuwanci da harkokin jirgin kasa da s**a hada yankunan kasar nan.
Haka kuma, a bangaren Kudu, akwai Calabar, Warri da Bayelsa, wadanda ke kara fito da matsayin Kafanchan a matsayin gari mai karbar baki daga kowane sashe na Najeriya.
Baya ga haka, akwai tituna masu nuna asalin Jama’a Emirate da rayuwar al’umma kamar Danhaya, Kindaza, Isa Muh’d Close, Church Street, Masallaci Street, Hospital Road, Titin Mai Martaba (Emir’s Road), Kaninkon Street da Cross Road. Wadannan sunaye na dauke da tarihi, addini, sarauta da kuma rayuwar yau da kullum.
Haka zalika, sunayen unguwanni kamar Unguwar Rumada, Cikin Gari, Unguwar Jama’a, Hayin Gada da Unguwar Bala suna ba da haske kan yadda Kafanchan ta bunkasa daga tsofaffin matsugunai zuwa babban gari mai yalwar jama’a.
A takaice, sunayen titunan Kafanchan ba wai hanya kawai suke nuna wa ba, suna kuma ba da labarin tarihi, asali da hadin kan kasa.
Wace t**i ko unguwa ce a Kafanchan kuke ganin tana da tarihi mai ban sha’awa?
Idan kai dan asalin Kafanchan ne, daga wanne layi kake?
Yaya sunan mai unguwarku?
Idan daga nesa kake, me ka sani a kan Kafanchan? Me yake zuwa kwakwalwar ka da zarar an ambaci Kafanchan?
Ku rubuta mana a comment section domin mu taskace tarihin garinmu.
North
1. Kano Street
2. Kaduna Street
3. Katsina Street
4. Sokoto Street
5. Borno Street
6. Bauchi Street
7. Bida Street
8. Zaria Street
9. Funtua Street
10. Soba Street
11. Bebeji Street
12. Jama’a Street
13. Jos Street
14. Hadeja Street
15. Adamawa Street
16. Jagindi Street
17. Wamba Street
18. Abuja Street
West
19. Ibadan Street
20. Ogbomosho Street
21. Lagos Street
22. Ilorin Street
South
23. Calabar Street
24. Warri Street
25. Bayelsa Street
Others
26. Danhaya Street
27. Kindaza Street
28. Isa Muh'd Close
29. Church Street
30. Masallaci Street
31. Hospital Road
32. Emir’s Road
33. Albarka Street
34. Magajiya Street
35. Kaninkon Street
36. Cross Road
37. Gurara Street
38. Ung. Rimi Road
39. GSS Road
40. Railway Road
Unguwanni
Ung. Rumada
Cikin Gari
Ung. Jama’a
Hayin Gada
Ung. Bala
Ung. Makafi
Sabon Sarki
Ung. Shanu
Gangare
Wace t**i ko unguwa ce a Kafanchan kuke ganin tana da tarihi mai ban sha’awa?
Idan kai dan asalin Kafanchan ne, daga wanne layi kake?
Yaya sunan mai unguwarku?
Idan daga nesa kake, me ka sani a kan Kafanchan? Me yake zuwa kwakwalwar ka da zarar an ambaci Kafanchan?
Idan Akwai Inda Bamu Ambata Ba a Tuna Mana.
Ku rubuta mana a comment section domin mu taskace tarihin garinmu.