29/09/2025
*SANARWAR AIKA WASIƘA ZUWA GA HON. BELLO EL-RUFA’I*
*Assalamu’alaikum,*
Muna farin cikin sanar da ƴan uwa cewa ƙungiyar cigaban al'ummar Sabon Garin Malalin Gabas - *Sabon Garin Malalin Gabas Community Development Association*, ta rubutawa *Hon. Mohammed Bello El-Rufa’i,* ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa wasiƙa, don buƙatar tattauna batutuwan ci gaban da s**a shafi al’ummar wannan yanki ta Sabon Garin Malalin Gabas da shi. Musamman, kan batutuwan ƴan asalin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa wanda su ka ƙunshi kusan kashi 60% na gidaje a Sabon Garin Malalin Gabas, kuma suke kaɗa ƙuri'ar su a can.
Wakilin kungiyar *Mal. Yasir Ishaq,* ya miƙa wasiƙar cikin nasara a yau 29 ga Satumba, 2025, kuma ɗaya daga cikin Ma'aikatan haɗin gwiwar *Hon. Bello El-Rufa’i* ya amsa wasiƙar domin miƙata ga shi Hon. ɗin.
Muna jiran amsa dangane da kwanan wata da lokacin taron, daga *Hon. Bello El-Rufa’i,* wanda za a sanar da membobin da zarar an tabbatar da su.
Allah ya bamu sa’a… Aamiin
*Bisallam.*
Comr. Muhammad Ziya’ulhaq Ashafa
*(Chairman, Muryar Matasan Sabon Garin Malalin Gabas)*
29th September, 2025.