22/12/2025
IRM Foundation Ta Saka Manyan Jigo-Jigon APC na Kaduna ta Arewa Cikin Shirin Kiwon Lafiya na KADCHMA
Gidauniyar IRM Foundation, ƙarƙashin jagorancin wanda ya kafa ta kuma mai ba Gwamnan Jihar Kaduna shawara na musamman kan harkokin jin kai, Alhaji Ibrahim Rilwan Muhammad, ta ɗauki nauyin saka manyan jigo-jigon jam’iyyar APC na Kaduna ta Arewa cikin shirin kiwon lafiyar jihar Kaduna, KADCHMA
Wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin tallafawa manufofin Gwamnatin Jihar Kaduna wajen rage wa jama’a nauyin kuɗin kula da lafiya, tare da tabbatar da cewa al’umma, musamman ma mambobin jam’iyyar APC na Kaduna ta Arewa, suna samun ingantacciyar kulawa a asibitoci.
Yayin jawabin sa a wajen taron kaddamar da shirin, Alhaji Ibrahim ya jaddada muhimmancin haɗin kai da ɗaukar alhakin juna wajen samar da lafiyar al’umma. Ya ce:
“Lafiya dukiya ce, kuma gwamnati kaɗai ba za ta iya ɗaukar nauyin biyan bukatun kowa ba. Don haka akwai buƙatar masu hali su tashi tsaye wajen tallafawa kokarin gwamnati.”
Ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen jin kai da dama da IRM Foundation ke aiwatarwa, domin rage raɗaɗin matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar. Haka kuma ya yi kira ga mambobin jam’iyya da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki ɗaya, tare da jajircewa wajen ci gaban jam’iyyar da kuma goyon bayan sake zaɓar Gwamnan Jihar Kaduna Senator Uba Sani a lokacin da ya dace.
A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa, Hon. Muhammad Gambo Zion, ya jinjinawa Alhaji Ibrahim bisa wannan gagarumin tallafi, tare da kira ga sauran manyan jami’an jam’iyyar da su ƙara ƙaimi da tsare-tsaren da za su inganta walwala da jin daɗin mambobin jam’iyya.
Wasu daga cikin waɗanda s**a amfana da shirin sun bayyana godiyarsu ga IRM Foundation, tare da yin alkawarin ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen shekara ta 2027.