Kawo Community Development Association - KCDA Youth Forum

Kawo Community Development Association - KCDA Youth Forum this is a forum for the helping hand and uniting the people of kawo ward

KCDA is a community Association that urges for promoting Unity, improving quality of life, enhancing the quality of education, facilitating rapid development in the community, youth empowerment.

12/05/2026
Yabon Gwani Ya Zama Dole.. Allah ya taya ka riko Sir
11/05/2026

Yabon Gwani Ya Zama Dole..

Allah ya taya ka riko Sir

Congratulations once again Sir our new Board Chairman Kaduna Market Development and Management Company
09/05/2026

Congratulations once again Sir our new Board Chairman Kaduna Market Development and Management Company

Congratulations, Sir, on your well-deserved appointment by the Kaduna State Government. May this position be of benefit ...
09/05/2026

Congratulations, Sir, on your well-deserved appointment by the Kaduna State Government. May this position be of benefit to the good people of Kaduna State. Once again, please accept our congratulations.

Civilian JTF KAWO....
01/05/2026

Civilian JTF KAWO....

Assalamualaikum warahmatullahi wabaratuhu*Matsayar wadannan kungiyoyi masu albarka dangane da fitar da dan takara da a k...
10/04/2026

Assalamualaikum warahmatullahi wabaratuhu

*Matsayar wadannan kungiyoyi masu albarka dangane da fitar da dan takara da a kayi a kawo ba bisa ka'ida ba*

* Kawo Community Development Association (KCDA)
* Kawo Muslim Association of Nigeria ( KAMAN)
* Jama'atu Izalatil bidi'ah wa'ikamatis Sunnah kawo (Jibwis)

*
Wadannan kungiyoyi masu albarka, suna Kira da babban murya ga dukkan masu ruwa da tsaki a kawo, dasu Sani cewa wannan zabi da a kayi na fitar da dan takaran Dan majalisar gundumar kawo anyi shi ne bada yawun su ba.

Mun gode.

Ana gayyatar kowa da kowa
04/04/2026

Ana gayyatar kowa da kowa

03/04/2026

*GAYYATAR TARO NA AL'UMMAR KAWO KADUNA*
**************************
_*Ana gayyatar Dukkanin Al'ummar Kawo Taro da za ayi Ranar Lahadi 5th April, 2026 da Karfe 9:30 A.M a Makarantar Dalet Girls Secondary School Kawo Kaduna (DAY KAWO) Insha Allah*_

*Agenda:*
_*1- Batun Tsaro (Security)*_
_*2- Batun Makarantar Dalet Girls Secondary School Kawo Kaduna (Day Kawo)*_
_*3- Batun Babban Asibitin Kawo (Kawo General Hospital)*_

_Allah Bada ikon Zuwa_

Signed,
_*Engr. Shehu Usman Dantudu (Chairman Kawo Community Development) Association KCDA) & Sheikh Shehu Uthman Gambo (Chairman Kawo Muslim Association of Nigeria KAMAN)*_

3rd April, 2026

ZUWA GA GWAMNATIN JIHAR KADUNAAssalamu alaikum,Bisa girmamawa da jinjina, mu al’ummar Kawo Ward dake Karamar Hukumar Kad...
31/03/2026

ZUWA GA GWAMNATIN JIHAR KADUNA

Assalamu alaikum,

Bisa girmamawa da jinjina, mu al’ummar Kawo Ward dake Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa, muna son isar da wannan kiran ga Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani.

Muna kira ga Maigirma Gwamna da ya gaggauta shiga tsakani game da batun wasu mutane da ke son mamaye Makarantar Sakandare ta Yanmata ta Day Kawo.

Akwai rahotanni da ke cewa wasu mutane suna ikirarin an siyar da quarters na malaman makarantar ga wasu, wanda hakan ke iya kawo cikas ga amfanin yara talakawa da makarantar ke bayarwa.

Muna mai jaddada cewa wannan batu ba wai abin wasa ba ne, domin yana shafar makomar yara da kuma amincin al’umma.

Haka kuma, mun fahimci cewa wannan lamari na iya zama wani yunkuri na bata suna ko zagon kasa ga Maigirma Gwamna a lokacin da zaben 2017 ke karatowa, wanda ke nuna aniyar wasu su ga faduwar gwamnatin jihar a ido.

Muna roƙon Maigirma Gwamna da hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike, su tabbatar da gaskiya, sannan a kare martabar makarantar da hakkin yaran al’umma.

Muna godiya da kulawarku,
Al’ummar Kawo Ward, Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa

29/03/2026

BAƘON JIYA NA IYA DAWOWA A KAWO – LOKACI YA YI NA ƊAUKAR MATAKI!

A kwanakin baya, al’ummar Kawo sun fuskanci wani mummunan lamari na rashin tsaro wanda ya tayar da hankalin kowa. An kashe wani jami’in tsaro a kan babban titin mota, kusa da tashar mota, sakamakon harin wasu masu kwacen waya. Wannan al’amari ba ƙaramin firgici ya haifar ba, ya kuma sa jama’a shiga damuwa tare da jefa yankin cikin yanayi na fargaba.

Bayan wannan iftila’i, an ga ƙoƙari da haɗin gwiwar jami’an tsaro wajen dawo da zaman lafiya, wanda ya kawo ɗan sauƙi na wani lokaci. Amma abin takaici, wannan ƙoƙari ya dusashe, komai ya yi shiru tamkar an manta da abin da ya faru.

Yanzu haka, alamu na nuna cewa irin wannan ta’asa na ƙoƙarin dawowa, musamman a ƙarƙashin gadar mota a Kawo — wani muhimmin wuri da ke zama mahadar matafiya daga kudanci zuwa arewacin ƙasa da kuma akasin haka. Wannan lamari barazana ce ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

Tambayoyi masu muhimmanci sun taso:
Shin jami’an tsaro sun ja da baya ne?
Ko kuwa suna fuskantar ƙarancin kayan aiki da rashin isasshen tallafi ne?

A zahiri, lokaci ya yi da za a ɗauki matakai masu ƙarfi da gaggawa:

A dawo da sintiri na haɗin gwiwa (joint patrol) kamar yadda aka yi a baya

A ƙara yawan jami’an tsaro a wuraren da ake yawan aikata laifuka

Gwamnati ta samar da ingantattun kayan aiki da isasshen tallafi ga jami’an tsaro

Al’umma su ƙara ba da haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanan sirri cikin gaggawa

Dole ne mu fahimci cewa tsaro alhakin kowa ne. Idan aka yi sakaci ko aka yi shiru, wannan matsala za ta iya ƙara tsananta, har ta kai ga rasa rayuka da dukiyoyi da dama.

A ƙarshe, muna Allah wadai da wannan mummunan kisan gillar da aka yi wa wannan bawan Allah ba tare da wani laifi ba. Muna roƙon Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa, Ya kuma bai wa iyalansa haƙuri da juriya.

Tsaron Kawo, Tsaronmu ne gaba ɗaya. Mu tashi tsaye kafin lokaci ya kure.

Daga Masu Hasashen Alheri ga Kawo

16/03/2026

Address

Kakuri Road
Kaduna

Telephone

+2347063470034

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kawo Community Development Association - KCDA Youth Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share