Alliance for Progressive Nigerian Society-APNS

Alliance for Progressive Nigerian Society-APNS An NGO advancing human capital through social, educational, and entrepreneurial development.

YAN NIGERIYA DA S**A KARATU A SUDAN ZA SU GABATAR DA GAGARUMIN TARON A JIHAR KANOKwamitin Shirya Taron Ƙungiyar ’Yan Naj...
15/02/2026

YAN NIGERIYA DA S**A KARATU A SUDAN ZA SU GABATAR DA GAGARUMIN TARON A JIHAR KANO

Kwamitin Shirya Taron Ƙungiyar ’Yan Najeriya da s**a yi karatu a Sudan (Nigerian Sudan Alumni) ya sanar da shirin gudanar da taron sada zumunci na mambobinsa, domin ƙarfafa haɗin kai, bunƙasa zumunci, da sake haɗa tsofaffin abokan karatu da abokai.

An shirya gudanar da taron kamar haka:

Rana: Asabar, 28 ga Maris, 2026
Lokaci: 11:00 na safe
Wuri: Dakin Taro na Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Jihar Kano.

Manufar wannan taro ita ce haɗa ’yan Najeriya da s**a yi karatu a Sudan domin sad zumunci, da tattauna muradun gama-gari, da kuma lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen ci gaban ƙasa da jin daɗin mambobin ƙungiyar.

Taron zai kasance dandali na musayar ra’ayi, sake gina alaƙa, da tsara makomar haɗin kai ga al’ummar "Nigerian Sudan Alumni'

Saboda haka, ana ƙarfafa dukkan mambobin ƙungiyar "Nigerian Sudan Alumni" da su halarta tare da bayar da gudummawa, domin ana sa ran taron zai kasance mai matuƙar muhimmanci da tasiri.

Don ƙarin bayani, mambobi na iya tuntuɓar Kwamitin Shirya Taro.

Mun gode.

15/02/2026
02/02/2026

This NGO dedicated to advancing human capital through inclusive social, educational, and entrepreneurial development. The organization empowers individuals with knowledge, skills, and opportunities to improve livelihoods, foster innovation, and drive sustainable community growth.

Address

Plot JA, 23, Kakaki Street, Kinkinau, GRA
Kaduna
800221

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alliance for Progressive Nigerian Society-APNS posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share