AA Qurami Orphans Support Organisation

AA Qurami Orphans Support Organisation Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AA Qurami Orphans Support Organisation, Nonprofit Organization, FF 19 Zangon Afaka Rigasa Kaduna, Kaduna South.

27/02/2026

3003082279
KUDA MFB
AA Qurami Connection Ventures

Wannan shine account number din na Gidauniyar AA Qurami Orphans Support Organisation

Ga wanda Allah ya h**e muwa kuma yake da niyya sai a bada abunda Allah ya h**e

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Da farko muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, wanda Ya h**e mana zuciya da...
02/02/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Da farko muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, wanda Ya h**e mana zuciya da tausayi, Ya kuma umarce mu da taimakon marayu da marasa galihu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaban halitta Annabi Muhammad (SAW), wanda ya kasance mafi tausayi ga marayu, har ya ce: “Ni da mai kula da maraya muna tare a Aljanna kamar haka” sai ya nuna yatsunsa guda biyu.

Yan uwa maza da mata,

Maraya ba wai kawai yaro ne da ya rasa mahaifi ko mahaifiya ba; maraya yaro ne da ya rasa garkuwar rayuwa, ya rasa jagora, ya rasa wanda zai tsaya masa a lokacin bukata. Amma duk da haka, maraya yana da mafarki, yana da buri, yana da basira da hazaka kamar kowane yaro a cikin al’umma.

Babbar matsalar da marayu ke fuskanta a yau ita ce rashin damar samun ingantaccen ilimi. Yaro maraya na iya zama likita, malami, lauya ko shugaba, amma talauci da rashin tallafi na iya katse wannan tafiya tun daga tushe. Idan aka hana yaro ilimi, an hana shi makoma; idan aka taimaka masa da ilimi, an gina al’umma baki daya.

A nan ne rawar AA Qurami Orphans Support Organisation take bayyana. Wannan gidauniya ba wai tana ciyar da marayu kadai ba, tana tufatar da su ko kula da lafiyar su kawai ba; tana gina rayuwa ne ta hanyar ilimi. Tana biyan kudin makaranta, tana samar da kayan karatu, tana karfafa zuciyar marayu su ji suna da daraja kuma suna da makoma mai kyau...

Ya jama’a,
Duk littafin da aka saka a hannun maraya sadaka ce, duk kudin makarantar da aka biya masa ibada ce, duk murmushin da muka janyo masa lada ne a wurin Allah. Taimakon ilimin maraya ba ya lalacewa, domin ilimi gadon rayuwa ne da yake bin mutum har kabari.

Mu tuna cewa, wata rana mu ma za mu tsaya gaban Allah, za a tambaye mu: me muka yi da damar da aka ba mu? Shin mun taimaki marayu, ko mun juya baya? Shin mun gina rayuka, ko mun yi shiru muna kallo?

Saboda haka, muna kira ga masu hannu da shuni, ‘yan kasuwa, malamai, da duk mai zuciyar tausayi: ku tallafa wa AA Qurami Orphans Support Organisation. Ku bayar da duk abin da kuka iya kudi, lokaci, shawara ko addu’a, domin ceto makomar marayu ta hanyar ilimi.

A karshe, muna rokon Allah Ya saka wa duk wanda ya taimaka wa marayu da alheri, Ya yalwata masa arziki, Ya kare shi da iyalansa, Ya kuma haɗa mu tare da Annabi (SAW) a Aljannatul Firdaus.

Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Assalamualaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Kamar dai yadda mukayi muku alkawarin cewar duk karshen wata zamu dunga tunat...
30/01/2026

Assalamualaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Kamar dai yadda mukayi muku alkawarin cewar duk karshen wata zamu dunga tunatar da Yan uwa bisa neman tallafin ku domin taimakawa wajen biya musu kudin makaranta tareda sauran abubuwan da s**a shafi karatun.

Muna roqon Allah ya bada ikon bayarwa ya h**e abun bayarwa.

26/12/2025
TUNATARWA TA MUSAMMAN 🤍Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh.Da wannan sakon, muna tunatar da ’yan’uwa masu albark...
25/12/2025

TUNATARWA TA MUSAMMAN 🤍

Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh.

Da wannan sakon, muna tunatar da ’yan’uwa masu albarka game da alkawarin gudunmawar da s**a dauka domin tallafawa rayuwar marayu da masu bukata ta hannun wannan gidauniya.

Karshen wata ya zo, kuma kamar yadda kuka sani, gudunmawar ku ita ce ginshikin farin cikin wadannan yara, iliminsu, lafiyarsu da makomarsu.

Ko da gudunmawa kadan ce, tana da matukar girma a wajen Allah ﷻ da kuma a zukatan marayu.

“Duk wanda ya ciyar da maraya, Allah zai ciyar da shi alkhairi fiye da yadda yake zato.”

Muna rokon ku da ku cika alkawarin da kuka dauka, domin alkawari amana ce, kuma marayu na jiran taimakon ku.

Allah Ya saka da alheri, Ya ninka lada, Ya sanya a ma’aunin ayyukan alkhairin ku.
Ameen.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Lpwv8xG9UeRJSNhe7xco2N

23/12/2025

Don Allah ku tausaya mu marayu...

Short Reminder!!!*1️⃣“Kada ka zalunci maraya.”📖 Al-Duha 93:9👉 Taimakon marayu ibada ce.2️⃣“Ni da mai kula da maraya zamu...
15/12/2025

Short Reminder!!!*

1️⃣

“Kada ka zalunci maraya.”
📖 Al-Duha 93:9

👉 Taimakon marayu ibada ce.

2️⃣

“Ni da mai kula da maraya zamu kasance tare a Aljanna.” ﷺ
📚 Bukhari

👉 Tazararmu kaɗan ce kamar yatsu biyu.

3️⃣

“Suna ciyar da miskini da maraya saboda Allah.”
📖 Al-Insan 76:8

👉 Rahama alamar imani ce.

4️⃣

“Gida mafi alkhairi shi ne wanda ake kyautatawa maraya.” ﷺ
📚 Ibn Mājah

👉 Ka sanya gidanka cikin alheri.

5️⃣

“Ku girmama marayu.”
📖 Al-Fajr 89:17

👉 Girmamawa ita ce ginshikin tausayi.

6️⃣

“Duk wanda ya shafa kan maraya saboda Allah, yana da lada a kan kowace gashi.” ﷺ
📚 Ahmad

👉 Ƙaramin aiki, babbar lada.

7️⃣

Murmusin maraya sadaka ne.
👉 Ka zama dalilin farin cikinsu.

8️⃣

Kada ka jira ka zama mai kudi kafin ka taimaka maraya.
📖 Al-Baqarah 2:215

👉 Allah yana duba zuciya.

9️⃣

Annabi ﷺ ya kasance maraya.
👉 Taimakon marayu Sunnah ce.

🔟

Duk alherin da ka yi, Allah Ya sanshi.
📖 Al-Baqarah 2:197

Address

FF 19 Zangon Afaka Rigasa Kaduna
Kaduna South
FF19

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AA Qurami Orphans Support Organisation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share