26/02/2026
Kira ga Al’ummar Jihar Filato da su Yi Watsi da Siyasar Zubar da Jini
Al’ummar Hausawa na Jos ta Arewa sun yi imani da gaske cewa Jihar Filato ta wuce wancan mummunan zamani mai cike da radadi na tantance mutane da kashe fararen hula marasa laifi a kan manyan hanyoyinmu. Abin takaici, a ranar Litinin, 23 ga Fabrairu, 2026, tsakanin Dorowan Babuje da Mangu Hale, wasu abubuwa sun faru da s**a sake tuna mana cewa har yanzu inuwa ta wancan lokaci na nan.
Wasu matasa ‘yan kasuwa Hausawa guda hudu daga Jos ta Arewa, suna cikin tafiya cikin lumana zuwa Kasuwar Litinin ta Pankshin domin gudanar da halastaccen kasuwanci, an kashe su cikin rashin imani. Sa’o’i kadan kafin haka kuma, an ruwaito cewa mutane tara an kashe su a wani hari da aka kai a wani otel a cikin wannan al’umma. Kwanaki kadan kafin wannan, wasu makiyaya Fulani uku da aka sanar da bacewarsu tun da fari, daga bisani an same su an kashe su tare da yi musu yankan rago. Wadannan al’amura ba su kadai ba ne. Abin da muke gani a yanzu shi ne wani mummunan zagayen tashin hankali da aikata laifuka da ke kara kamari.
Mu bayyana a fili ba tare da wata shakka ba: Kai hari ga matafiya marasa laifi saboda suna da alaka ta kabila ko addini da wadanda ake zargi da aikata laifi, abu ne na rashin tausayi, laifi ne, kuma ba za a amince da shi ba.
Hukunta al’umma baki daya ba adalci ba ne. Daukar fansa ba ya samar da tsaro. A maimakon haka, yana nuna rugujewar kyawawan dabi’u da doka.
Tarihi ya nuna mana cewa duk wata daukar fansa tana dasa irin wata sabuwar daukar fansar a gaba.
Kowane matakin ramuwar gayya yana kara zurfafa zargi, yana fadada rarrabuwar kai, tare da barazana ga zaman tare cikin lumana da ke hada mu a matsayin al’ummar Filato.
Mun fahimci cewa al’ummomin da tashin hankali ya shafa na iya jin tsoro da takaici. Amma hakkin kare rayuka da dukiyoyi yana karkashin gwamnati da hukumomin tsaro ne kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Muna kira ga hukumomin tsaro da su zakulo wadanda ke da hannu a wadannan