AL-Itqan Charity Foundation

Call Website Contact the organization

AL-Itqan Charity Foundation The Association aims is to assist Orphans and the less privileged.

"Giving is the best way to show gratitude 🌟. Let's spread kindness and support our orphans, as the Prophet (PBUH) said, ...
09/02/2026

"Giving is the best way to show gratitude 🌟. Let's spread kindness and support our orphans, as the Prophet (PBUH) said, 'I and the one who sponsors an orphan will be in Paradise like this,' showing his fingers. (Bukhari 6005)

Your support can change a life. Donate, volunteer, or share this post.

"

AL-ITQAN CHARITY FOUNDATION, muna ci gaba da aikin alheri na tallafa wa marayu, gajiyayyu ta hanyar ba su tufafi, abinci...
07/02/2026

AL-ITQAN CHARITY FOUNDATION,

muna ci gaba da aikin alheri na tallafa wa marayu, gajiyayyu ta hanyar ba su tufafi, abinci, da kulawa ta musamman.
Yayin da muke shirin shiga watan Ramadan, muna kuma shirya rabon abinci domin taimaka wa marayu da mabukata su samu sauʙi a wannan wata mai albarka.
Muna kira ga masu hali da masu son aikata alheri su kasance tare da mu wajen yada farin ciki da bege.
Taimako kaɗan daga gare ka na iya zama babbar ni’ima ga wani.
ā€œDuk wanda ya tallafa wa maraya, Allah zai ninka masa lada.ā€

🤲 Mu haɗa hannu domin alheri.

Hotuna daga Wajan walimar Auren Malama Nasiba Abdullahi P.R.O na AL-ITQAN CHARITY FOUNDATION
08/01/2026

Hotuna daga Wajan walimar Auren Malama Nasiba Abdullahi P.R.O na AL-ITQAN CHARITY FOUNDATION

08/01/2026

daga wajan walimar Auren Malama Nasiba Abdullahi P.R.O na AL-ITQAN CHARITY FOUNDATION.

SAKON TA’AZIYYAInnā lillāhi wa innā ilaihi rāji’ūn.Al-Itqan Charity Foundation na mika sakon ta’aziyya mai cike da alhin...
27/11/2025

SAKON TA’AZIYYA

Innā lillāhi wa innā ilaihi rāji’ūn.

Al-Itqan Charity Foundation na mika sakon ta’aziyya mai cike da alhini ga iyalai, ā€˜yan uwa, almajirai, mabiya, da daukacin al’ummar Musulmi bisa rasuwar fitaccen malami, tauraron ilimi, jagoran al’ummah, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya rayu rayuwar kyautatawa, ilimantarwa, da raya addinin musulunci. Ya kasance madogara ga mabukata, ginshiʙi ga almajirai, jagora ga malamai, kuma haske ga al’ummar da ya shafe rayuwarsa yana yi wa hidima.

Allah Ya karɓi rayuwarsa cikin rahama, Ya yafe masa, Ya raya darajarsa, Ya sanya kabarinsa ya kasance daga cikin gidajen Aljanna.
Allah Ya ba iyalansa, ɗalibansa, da al’ummar Musulmi hakuri da juriyar jure wannan babban rashi.

Wannan rashi ba na iyali ba ne kaɗai — rashi ne na al’umma gaba ɗaya.

Allah Ya jikansa da rahama.
Amin.

— Al-Itqan Charity Foundation

JARRABAWA TA ALLAH — LABARIN ANNABI AYYUB (AS) Daga cikin annabawa, Annabi Ayyub (Alaihissalam) ne ya fi fuskantar jarra...
24/10/2025

JARRABAWA TA ALLAH — LABARIN ANNABI AYYUB (AS)

Daga cikin annabawa, Annabi Ayyub (Alaihissalam) ne ya fi fuskantar jarrabawa mai tsanani. Allah Ya gwada shi da rashin dukiya, rashin lafiya, da rashin ’ya’ya, har jikinsa ya cika da ciwo, kuma mutane s**a guje shi — sai matarsa kaɗai ta rage tana kula da shi.

Duk da haka, bai taɓa gunaguni ba. Sai ya ce:

"Anni massaniyaįø-įøurru wa anta arįø„amur-rāḄimÄ«n."
ā€œYa Ubangijina, an shafe ni da ciwo, kuma Kai ne mafi jin ʙai daga masu jin ʙai.ā€
Suratul Anbiyaa – Aya ta 83

Allah ya yabe shi saboda haʙuri da tawali’u, sannan ya mayar masa da lafiya, iyali, da dukiya fiye da yadda ya rasa.

Wannan yana koya mana cewa:

Duk jarrabawar da muke ciki, mu kasance masu haʙuri da dogaro ga Allah.
Lalle bayan ʙunci akwai sauʙi.

Al-Itqan Charity Foundation
ā€œServing humanity with sincerity and faith.ā€

šŸ’ššŸ’™šŸ’œšŸ¤ŽšŸ–¤šŸ¤
24/10/2025

šŸ’ššŸ’™šŸ’œšŸ¤ŽšŸ–¤šŸ¤

šŸ’” Innā lillāhi wa innā ilayhi rājiā€˜Å«nMun rasa ’yar’uwa Maryam 😢.Hakika mutuwa gargaɗi ce ga rayayyu. Maryam ta bar duniy...
12/10/2025

šŸ’” Innā lillāhi wa innā ilayhi rājiā€˜Å«n

Mun rasa ’yar’uwa Maryam 😢.
Hakika mutuwa gargaɗi ce ga rayayyu. Maryam ta bar duniya, amma kyawawan halayenta ba za su taɓa gogewa a zukatanmu ba.

Allah ya jikanta, ya gafarta mata, ya sanya kabarinta dausayin aljanna.
Ya kuma ba iyalanta da da Yan uwa haʙuri da juriyan rashin ta amin.

AL-ITQAN CHARITY FOUNDATION Tana farin cikin gayyatar mambobin ta gagarumin taro (Meeting) wanda zai gudana kamar haka I...
04/10/2025

AL-ITQAN CHARITY FOUNDATION

Tana farin cikin gayyatar mambobin ta gagarumin taro (Meeting) wanda zai gudana kamar haka Insha Allah:

Rana:~ Lahadi 5/10/2025

Wuri:~ Masallacin anglo Jos

Lokaci:~ 4:00pm

*NASIBA ABDULLAHI* šŸŽ¤
P.R.O

Innā lillāhi wa innā ilaihi rāji’ūnWani gini ya rushe daren yau da misalin ʙarfe 11:30 na dare a Dogon Agogo, Jos.Ginin ...
10/09/2025

Innā lillāhi wa innā ilaihi rāji’ūn

Wani gini ya rushe daren yau da misalin ʙarfe 11:30 na dare a Dogon Agogo, Jos.
Ginin ya rufta da yara huɗu (4) tare da iyayensu.

šŸ˜” Yara biyu daga cikinsu sun rasu.
Yanzu haka sauran iyalin suna kwance a OLA Hospital Jos Babban Masallacin Juma’a

🩸 Ɗaya daga cikin ’yan matan ta sami mummunan rauni a kashin baya (spinal cord injury).

Suna cikin tsananin buʙatar taimakon kuɗi. Don Allah a taimaka wa wannan iyali, musamman ʙaramin yarinyar da take cikin hali mai tsanani.

Allah ya saka da alheri. 🤲

Address

Mai Adiko Rayfield Jos
Jos

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AL-Itqan Charity Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to AL-Itqan Charity Foundation:

Shortcuts

Share