Shuwarin Development Association-SHUDA

Shuwarin Development Association-SHUDA SHUDA is a community development association, meant for human and societal development

28/03/2026

DOMIN SANAR DA AL'UMMAR GARI!

A cikin 'yan watannin da s**a gabata, bayan samun sahihan bayanai game da zargin niyyar raba filin lambun Shuwarin na dab da Gidan Tsika (kadarar alumma ta ƙarshe da ta rage a cikin garin Shuwarin) ga wasu mutane, wannan Ƙungiya ta dauki matakin gaggawa ta hanyar tuntuɓar duk masu ruwa da tsaki. Daga baya, Ƙungiyar ta nemi ganawa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Kiyawa domin gabatar da damuwarta da kuma tattauna al'amarin cikin manufar ƙubutar da wannan wuri da ya rage a cikin kewayen garin.

Shugaban Ƙaramar Hukuma a wancan lokacin ya tabbatar mana da cewa shi da kansa bai amince da wannan shirin ba, kuma cewa wannan ƙoƙari na wasu mutane ne masu son rai da neman amfanar da kansu kadai. Har ila yau, ya tabbatar wa Ƙungiyar da cewa zai jajirce wajen farfaɗo da lambun, wanda ya haɗa da gina shinge a kewaye shi, shuka ƙarin itatuwan da suke da amfani wajen tattalin arziki, samar da borehole don bayin ruwa, da kuma ɗaukar ma’aikatan wucin gadi don kula da lambun a kowace rana.

Abin takaici, a cikin 'yan kwanakin da s**a gabata, mun lura da ja da baya daga wannan alkawari. Sahihan bayanai sun nuna cewa an sake farfado da yunkurin yanka lambun kuma yanzu ana ƙoƙarin aiwatar da shi, wanda wani wakilin Ƙaramar Hukumar ke jagoranta. Wannan yunkurin ya kasance abin bakin ciki da takaice, duba da la’akari da alkawarin da akayi na farfado da shi amfanin dukkanin alummar garin Shuwarin da ma ita kanta karamar hukumar. Ƙungiyar SHUDA, shugabanninta, da sauran masu muradin alkairi ga Shuwarin sun kasance kan rashin amincewa da wannan yunkurin.
Wannan sanarwa an fitar da ita ne don sanar da alumma halin da ake ciki tare da kuma jan hankalin duk wani mai ruwa da tsaki.

Muhammad Sunusi Hussain
Sakatare

13/11/2025

SANARWA SANARWA,
KIYAWA LGA.

Gobe Juma'a 13-11-2025, za'a tantance mata masu sha'awar shiga Shirin Foundation Year Program (FYP).
Ma'ana Karatun JINYA da Kuma UNGOZOMA na Jihar Jigawa, karamar Hukuma KIYAWA.
Da Misalin 9:00am. Insha Allah.
A cikin sakateriyar mulki dake karamar Hukuma ta Kiyawa.

WAJIBABBUN ABUBUWAN DA AKE BUKATA SUNE:-
- SSCE daga 7-9 credit a bangaran kimiya (SCIENCE), Wanda ya hada da English, Maths, Physics, Chemistry, da Kuma Biology.

-Takardar shedar karamar Hukuma (INDIGINE).

-Takardar shedar katin Dan kasa (NIN).

-Original copy da Kuma Photocopy na takardun.

Allah ya bada sa'a.

Domin karin bayani a tuntubi.

Mushaffau Aliyu
Coordinator Danmodi Student care Kiyawa local Government.
08132112961.

10/10/2025

SANARWA!

Ina Masu bukatar gyaran jarabawar su ta SSCE (Takardar kammala karatun Sakandare) ga dama ta samu karkashin OFISHIN SSA Students zaa Biya Masu gyaran NECO(November/December).

Duk Mai bukatar sai ya tuntubi Alesau Musa akan wannan lambar 09038274214 Dan Karin bayani.

Allah Ya bada saa.

SHUDA OFFICIAL! Wakilan SHUDA sun gana da Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa. Wakilan sun tattauna batun Samar da Batiran S...
07/09/2025

SHUDA OFFICIAL!

Wakilan SHUDA sun gana da Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa.

Wakilan sun tattauna batun Samar da Batiran Solar da aka sace a asibitin Shuwarin inda maigirma Shugaban Karamar Hukuma Hon. Abdulhamid yayi alkawarin Samar da Batiran a cikin kankanin lokaci duba da tasirin da Solar ke dashi wajen gudanar da aiyukan asibitin.

Tun da farko Wakilan karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa Hon. Adamu Muhammad Adamu sun mika wa Shugaban Karamar Hukumar takarda Mai dauke da kira ga Shugaban Karamar Hukumar da ya sahale tare da bada gudunmowa wajen farfado da Lambun Gwamnati (Orchard) da yake Unguwar Gidan Tsika.

Shugaban ya Nuna Jin Dadin sa da wannan yunkurin tare da yin alkawarin turo kwamiti daga Karamar Hukuma Dan yin aiki tare da kungiya Dan rayar da wannan Lambu.

Muna adduar Allah Ya tabbatar mana da wadannan aiyukan tare da sauran ayyukan alheri da muke nema ga Al'ummar mu da Garinmu.

05/09/2025

SHUDA OFFICIAL!

A Madadin shugabanci da Al'ummar garin Shuwarin muna mika sakon godiya da yabo ga kungiyar Care International bisa Sanya wasu Unguwanni a garin Shuwarin cikin wadanda s**a amfana da tallafin kayan abinci ga Iyaye mata karkashin Shirin su na yakar Yunwa da Fatara a arewacin Najeriya Wanda ya gudana a karshen satin da ya gabata.

Kungiyar SHUDA na mika godiya da jinjina ga Al'ummar gari da s**a bada hadin Kai wajen gudanar da wannan rabon kayan abinci cikin aminci ba tare da an samu hatsaniya ba.

Godiya ta musamman ga wakilan SHUDA da s**a tsaya s**a hada Kai da jami'ai Dan ganin aikin ya tafi dai dai Musamman Shugaban SHUDA Dr. Sulaiman Badayi da Daraktan kwamitin Amintattu Mal. Ibrahim Babawuro da s**a bada kudi daga aljihun su Dan bada kudin shan ruwa ga jami'an KAGLOS security da s**a tsaya s**a bada gudunmawar tsaro Dan tabbatar da wannan aikin cikin Nasara.

Muna qara godiya ga Mai girma Hakimin Shuwarin, Sarkin Gabas din Dutse da wakilan sa da s**a bada muhimmiyar gudunmowa dan ganin wannan tallafi yaje ga wadanda aka tsara Dan su cikin sauki.

A karshe kungiyar SHUDA na kira ga Al'umma da su cigaba da ba bada hadin Kai akan duk Wani Shirin da zaa gudanar wajen kawo Cigaba zuwa garin Shuwarin da sauran garuruwan mu da suke kewaye da Shuwarin. Tare da adduar Allah Ya cigaba da daga darajar Garinmu da Al'ummar mu Amin.

Information Officer
for: Chairman

28/08/2025

SHUDA!

Kungiyar Shuwarin Development Association SHUDA ta Kai ziyarar aiki ga sabon BATUREN Yan sanda (DPO) na SHUWARIN DIVISION.

Ziyarar da wakilan kungiyar da ya kunshi Shugabanni da wakilan kwamitin Amintattun kungiyar sun Kai ziyarar ne Musamman Dan kyautata alaqa tsakanin Mutanen gari da hukumar Yan sanda dan qara inganta tsaron musamman a bangarorin da suke damun Al'umma a yanayin tsaron garin Shuwarin da kewayenta.

An tattauna muhimman ba batutuwa da s**a hada da Dakile matsalar sace sacen cikin gidaje na wayoyi da Dabbobi da Kuma shawarwari Masu maana Dan kiyaye abubuwan Dake yawan faruwa a Junction din Majiyawa.

A karshe baturen Yan sandan ya Nuna Jin Dadi tareda yiwa kungiya fatan alheri da alkawarin yin aiki tare Dan tabbatar da Cigaban wannan gari da Al'umma.

Muna adduar Allah Ya qara mana zaman lafiya da Cigaba Mai anfani.

SHUDA!Kwamitin Amintattun kungiyar SHUDA karkashin jagorancin Daraktan Amintattun Mal. Ibrahim Babawuro fate Wanda Matai...
18/08/2025

SHUDA!

Kwamitin Amintattun kungiyar SHUDA karkashin jagorancin Daraktan Amintattun Mal. Ibrahim Babawuro fate Wanda Mataimakin Sa Mal. Abubakar Abba Garba Mai Abuja da dafawar Alhaji Tela Isah, Alhaji Isyaku Namadige, Hon. Umar Ilu da sauran Yan kwamitin sun tabbatar da Dr. Suleiman Ahmed Badayi Shugaban Jigawa State Polytechnic Dutse a matsayin sabon shugaban kungiyar Shuwarin Development Association SHUDA.

Zaben Dr. Badayi ya biyo bayan duba Cancanta da Jajircewa da ya Nuna a jagorancin Kungiyar da yayi a shekarun da s**a gabata.

Tun da farko Shugaban yayi godiya tare da nuna k**ar bazai iya cigaba da jagorancin ba duba da Yanayin ayyukan da ke kansa, Amma Masu zaben a matsayin su na Iyaye s**a jaddada masa tare da nusar dashi alfanun da hakan zaiyi ga Al'ummar mu.

A karshe ya amince tare da neman hadinkan sauran Shugabanni da Iyaye da Al'ummar gari wajen sauke wannan nauyi da aka Dora masa.

Sauran Shugabannin da aka zaba sun hada da:

Mal. Suraja Alhaji - Mataimakin Shugaba.

Muhammad Sunusi Hussaini - SECRETARY GENERAL

Sulaiman Musa - Assistant Secretary

Basiru Shuaibu (Likita) - Treasurer

Abdullahi Abubakar (Dan Gaga) - Financial Secretary

Alh. Baffa Sunusi - Monitoring and Evaluation Officer I

Ismail Shuaibu - Monitoring and Eva. II

Yahya Dahiru - Information Officer

Yusuf Mai Shayi - Information Officer-II

Nuhu Nakaka - Welfare Officer I

Yahuza Mai washi - Welfare Officer II

Allah Ya Taya ruko Ya kawo mana Cigaba Mai anfani, Ya tsare mutuncin mu da Mutuncin Garinmu.

15/08/2025

SHUDA!

Ga wata tambaya mai sauki Kuma Mai wahalar amsawa musamman a wurin Yara da basa bin Tarihi?

A wace shekara aka kirkiri kungiyar Shuwarin Development Association, (SHUDA)?

13/08/2025

SHUDA !

Ana sanar da Iyayen Yara musamman Yan aji Shida na firamare Masu rubuta jarabawar Common entrance ta kammala karatun firamare cewa yau laraba 13/08/2025 zaa gabatar da wannan jarabawa k**ar yadda aka saba duk shekara.

Don haka duk daliban da suke Shuwarin Cluster su fito Shuwarin central primary da karfe 9:00am.

08/08/2025

SHUDA!

A madadin shugabancin kungiyar SHUDA muna mika Sakon taaziyya da jaje ga Al'ummar Shuwarin, musamman iyalan marigayi Saleh Dan Maluniya bisa rasa ransa da yayi a hannun jamian NSCDC a kokarin su na k**a shi bisa zargin sa hannunsa a wajen kashe jamiin su ranar Litinin da ta gabata a kasuwar Shuwarin.

Muna Allah Wadai da faruwar wannan al'amari Kuma muna Kara kira ga jamaar gari da su kwantar da hankalinsu kada su dauki matakin daukar doka a hannu, a gefe guda Kuma SHUDA na tabbatar wa da Al'umma cewa zata yi iya Mai yiwa wajen hada Kai da Shugabanni da Iyayen gari Dan bibiyar haqqin wannan marigayi da Kuma daukar Matakan kare afkuwar irin wannan lamari a Nan gaba.

GODIYA GA MATASHI MAI KISHIN GARI DA AL'UMMA ABDUSSAMAD SANI! Amadadin shugabanni, Iyayen kungiya da daukacin Al'ummar g...
04/08/2025

GODIYA GA MATASHI MAI KISHIN GARI DA AL'UMMA ABDUSSAMAD SANI!

Amadadin shugabanni, Iyayen kungiya da daukacin Al'ummar garin Shuwarin, muna Mika saqon GODIYA da yabawa ga Matashi Abdussamad Sani bisa namijin Kokari da yake wajen shiga lamuran Al'umma.

-Taimakon Dalibai Sama da dubu Biyu da Biro na rubutu.
-Cikon kasa a wasu wurare da suke Tara ruwan Sama a lokacin damina.
-Samar da kasar ciko Dan gyaran Makabarta.

Wannan Hali da yake nunawa na dattako abin yabawa ne kwarai da gaske, muna Yaba masa Kuma muna Kara bashi kwarin gwiwa da Kuma adduar Allah Ya karfafe shi, ya Kara masa arziki Mai anfani.

Address

Shuwarin Town, Kiyawa Local Govt
Jigawa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shuwarin Development Association-SHUDA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Shuwarin Development Association-SHUDA:

Shortcuts

Share