14/06/2026
📸 Ga yadda muka gudanar da ziyarar Gidan Marayu na Alheri Orphanage, dake kusa da CBN, Babayau, Jalingo.
Alhamdulillah, DARUL-UMMAH CHARITY FOUNDATION JALINGO ta samu damar kai ziyara zuwa Gidan Marayu na Alheri Orphanage domin nuna ƙauna, tausayi, da tallafi ga yaran da ke wannan cibiya.
A yayin ziyarar, mun yi mu'amala da yaran, mun yi musu nasiha da addu'o'i, tare da mika wasu tallafi gwargwadon ikonmu. Mun kuma yi kira ga al'umma da su ci gaba da tallafawa marayu da marasa galihu domin neman yardar Allah (SWT).
Manzon Allah (SAW) ya ce:
"Ni da mai kula da maraya za mu kasance a Aljanna kamar haka." Sai ya nuna yatsarsa ta manuniya da ta tsakiya. (Sahihul Bukhari)
Muna godiya ga dukkan mambobi da masu ruwa da tsaki da s**a ba da gudunmawa wajen nasarar wannan ziyara.
Allah Ya karɓi ayyukanmu, Ya albarkaci dukiyar masu taimako, Ya kuma sanya wannan aiki a ma'aunin kyawawan ayyukanmu. Ameen Ya Rabbal Alameen. 🤲
🤝 "Wa Ta'awanu 'Alal Birri Wat-Taqwa, Wa La Ta'awanu 'Alal Ithmi Wal-'Udwan."