11/09/2025
Inna lillahi wa'inna ilaihi raji, un
Munajin ƙuncin labarin nutsewar jirgin ruwa da ya faru a daren jiya Laraba 10/09/2025 da misalin ƙarfe 6:00pm a Gulbin da ke tsakanin Kamarawa da Shinkafi, wanda ya shafi al’ummar Kagara, dake karkashin karamar Hukumar Isa LGA, Jihar Sokoto.
Wannan hatsari ya rutsa da mata da ƙananan yara, inda jirgin ya ɗauki fiye da mutane 34, an ceto 23, sauran kuwa har yanzu ana cigaba da nema.
A madadin Isa Community and Neighboring Districts Association, muna mika sakon ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa da dukkan al’ummar yankin.
Muna roƙon Allah Madaukaki Ya jikansu, Ya gafarta musu, Ya kaihaske kabarinsu, Ya kuma baiwa iyalan da s**a rage juriyar wannan babban rashi.
Allah Ya tsare mu daga irin wannan iftila’i, Ya ba al’ummar mu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Sa hannu:
Engr. Surajo Abdullahi
Shugaban Ƙungiya