I K U Y O F

I K U Y O F IKUYOF Means Ikara United Youth Forum.

It's non governmental organization but public servant to grow and maintain peace, unity and progress in our dear local government.

MURYAR YANCI👌Innalillahi Wa'innah Ilaihirraji'un😭Allah ya jikan Alh. Shehu Dandukawa, da rahama ya yafe masa kura kuran ...
29/07/2026

MURYAR YANCI👌

Innalillahi Wa'innah Ilaihirraji'un😭

Allah ya jikan Alh. Shehu Dandukawa, da rahama ya yafe masa kura kuran sa yasa aljannah firdausi ce makoma agare shi amin🤲

Jana'iza yau laraba karfe 9:00am na safe

MURYAR YANCI👌Alhamdulillah, Masha Allah Alah Kulli Halin👏A mamadin al'ummar musulmin karamar hukumar Ikara da kewaye bak...
27/07/2026

MURYAR YANCI👌

Alhamdulillah, Masha Allah Alah Kulli Halin👏

A mamadin al'ummar musulmin karamar hukumar Ikara da kewaye baki daya muna qara jadda da godiyar mu ga mai girma Hon. Bashir Suleiman Zuntu [BZ] bisa kokarin sa na bada gudunmawar cigaba da gina dakin Allah wato babban Masallacin Juma'ah na Imam Malik Bin Anas GRA Ikara, na tunawa da marigayi Imam Bello Hamza Ikara, Allah ya jikan sa da rahama.

Wanda mai girma Bashir Suleiman Zuntu [BZ] ya bada naira dubu dari biyar 500.000.00 da farko yanzu kuma ya qara bada naira miliyan da dubu dari biyar 1,500.000.00 BZ Allah yasaka da alkhairi yasa a mizani amin.

MURYAR YANCI👌KULLU NAFSIN ZA'IKATUL MAUT!INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIRRAJI'UN😭 Allahu Akbar, Muna miqa sakon ta'aziyyar m...
26/07/2026

MURYAR YANCI👌

KULLU NAFSIN ZA'IKATUL MAUT!

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIRRAJI'UN😭

Allahu Akbar, Muna miqa sakon ta'aziyyar mu ga ya'ya, yan'uwa, abokan arziki dama al'ummar karamar hukumar Ikara da kewaye baki daya bisa rasuwar Mallam Hamisu Musa, tare da addu'ar Allah ya jikan shi da rahama yasa aljannah firdausi ce makoma agare shi amin.

Za'a gudanar da jana'izar shi yau lahadi da misalin karfe Tara na safe [9 : 00am]

MURYAR YANCI👌
04/07/2026

MURYAR YANCI👌

MURYAR YANCI👌Innalillahi Wa'innah Ilaihirraji'un!Kullu Nafsin Za'ikatul Maut😭Cikin jimami da alhini muke sanar da yan'uw...
03/07/2026

MURYAR YANCI👌

Innalillahi Wa'innah Ilaihirraji'un!

Kullu Nafsin Za'ikatul Maut😭

Cikin jimami da alhini muke sanar da yan'uwa da abokan arziki dama al'ummar karamar hukumar Ikara da kewaye baki daya bisa rasuwar Malam Mustapha, mahaifin Hussaini Mustapha, [Direba]

Muna miqa sakon ta'aziyyar mu ga ya'ya, yan'uwa, jikoki da abokan arziki Allah ya jikan shi da rahama yasa aljannah firdaus ce makoma agare shi amin.

Za'a gudanar da jana'izar shi da safiyar yau Juma'ah misalin karfe [8:00am] a gidan sa dake kasuwa 'yan barkono Ikara

MURYAR YANCI👌KULLU NAFSIN ZA'IKATUL MAUT😭Sakon ta'aziyyar mu ga yan'uwa, ya'ya, jikoki, abokan arziki dama al'ummar kara...
21/06/2026

MURYAR YANCI👌

KULLU NAFSIN ZA'IKATUL MAUT😭

Sakon ta'aziyyar mu ga yan'uwa, ya'ya, jikoki, abokan arziki dama al'ummar karamar hukumar Ikara bisa rasuwar dan'uwa Ayuba Dangilin, Allah yajikan shi rahama yasa aljannah firdausi ce makoma agare shi amin🤲

MURYAR YANCI👌Hasbunallahi Wani'imalwakil😭 Matashi Alhamdu Chino, yarasa ransa a sanadiyyar mamakon ruwan sama da akayi a...
15/06/2026

MURYAR YANCI👌

Hasbunallahi Wani'imalwakil😭

Matashi Alhamdu Chino, yarasa ransa a sanadiyyar mamakon ruwan sama da akayi a jiya lahadi 14/06/2026 a hanyar ruwan garin Saulawa zuwa Janmarmara, karamar hukumar Ikara.

Da haka muke mika sakon ta'aziyyar mu ga ya'uwa da abokan arziki dama al'ummar karamar hukumar Ikaran da kewaye baki daya bisa wannan rashi Allah ya bada hakuri da juriyar rashin sa amin.

◇Rokon arziki zuwa ga shugaban karamar hukumar Ikara

Bayan haka a karkashin wannan if iftila'in da yafaru muna mika kokon barar mu ga shugaban karamar hukumar Hon. Bashir Mamman Dogon-Koli, a bisa kokarin sa na yiwa al'umma talakawa musamman karkara aiyukan alkhairi irin wannan akoda yaushe muna rokon da ya duba wannan hanyar ruwa ta garin Saulawan zuwa Janmarmara ayi mata aikin gadar irin na garin Kwari muna sa ran insha Allahu gurin zai dauka.

Sabida haka mai girma shugaban karamar hukumar don Allah ayi hakuri a duba wannan lamarin duk da dai mun san halin da ake ciki da kuma irin kokarin da kakeyi Allah yasaka maka da alkhairi ya bada ikon yi yaqara jagoranci nagari amin.

Address

Ikara

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when I K U Y O F posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share