24/06/2025
IBI ONEđź’–
Ibi Alwaysâś…
Zuwa ga matasa masu tasowa...
Ko kuna tunanin yadda goben ku zai kasan ba kamar irin na magabata ba.
Communities mu ya kasan cike da matasa da s**a kammala karatunsu kamar haka:- FSLC, SSCE, Certificate, DIPLOMA, NCE, HND, FIRST DEGREE DA MASTER DEGREE da ma wadda basu samu daman zuwa karatun ba.
Gashi babu aikin yi na gaunati, babu taƙamemen sana'a da zai iya riƙe matashi har ya taimaki iyayen ko ƙanninsa har ma yace zaiyi aure.
Hakan yazamu mana kalubale ga communities, domin duk wata community da matasa suke zaune kara zube babu aikin yi to tabbas wannan al'umma suna cikin barazana da tashin hankali, domin komai zai iya faru na gurɓacewa tarbiya musamman ga matasa masu tasowa.
MAFITA ga wannan matsala shine dole IYAYE, SHUWAGABANNI da kuma JAGORORIN MATASA su tashi tsaye gurin taimakawa community suga an magance wannan matsaloli domin gaunati bazata iya baiwa kowa aiki ba koda zata iya ma ayanxu bamuga halama hakan ba.
Mataki na farko iyaye dole ku tashi tsaye akan yara ta farnin karatu da kuma sana'a wadda yara zasu iya dogoro dashi idan sunkai munzali.
HANYA DA ZAMU FARA GYARA WANNAN MATSALAN KUWA SHINE:-
- Iyaye da shuwagabanni su tashi tsaye gurin tabbarwa yaransu irin jadawalin karatu wato (course of study) da zasu É—auka yayin daga sun kai SSS 1. Ma'ana shine yara dole su koyi courses da yake hakala da management da vocational skills "kamar yadda wani babban Malaminmu Sheikh Isa Ali Pantami yake fada mana cewa (SKILLS RATHER THAN JUST A DEGREE)"
Sanya yaro akan wannan tsari zai taimakawa communities da kuma kasa mai tasowa gurin iya rike kanta "Ina amfanin yawa har idan baku iya tsinana komai" kamar dai Jama'ar Gidan Badamasi🤗🤣.
Iyaye, Shuwagabanni, Jagororin Matasa ku taimaki al'umma ku domin su dogara da kansu kada mu sake maimai irin kuskuren da mukayi abaya na halin da muke ciki ayanxu, GA MASU DEGREE A KOWANI GIDA amma ba mai amfani ba saboda irin courses da muka karanta bazai amfanemu b***e mu amfanar da community mu.
Next post nawa akan wannan al'amari zai kasance shawarwari tare da mafita da kuma yadda zamu samu damasa isar da wannan sako ga iyaye wadda basu da hakala da social media.
~Abdulrazak H. Magaji our protocol chairman matasa
Youths Ambassador âś…