16/08/2024
Assalamu Alaikum...
Ina mai amfani da wannan dama na mika godiya ta ga dukkan jama'ar da s**a halarci wajen rakani ganawa da jama'ar ward dinmu domin neman alfarmar kuri'arsu da addu'o'insu tare da goyon baya. Allah Ya saka da alkhairi, na gode da irin wannan kauna da aka nuna min, Allah Ya bar mu tare.
Ina mai mika godiyata ga al'ummarmu bisa irin karba da tarba ta karamci da na samu tare da addu'o'in alkhairi dan neman jagorancin Allah Madaukakin Sarki a wannan yunkuri da muka yi. Allah Ya bar mu tare Ya kuma kara mana dankon zumunci, ameen.
Ina mai jaddada niyyata tare da dukkan kokari da zan iya yi domin yi wa jama'a aiki tukuru bisa turbar wakilci na gari idan Allah Ya ba ni nasara a wannan zabe na gobe.
Allah Ya ba mu nasara, Ameen.