Kampala Development Forum, Kungiyar cigaban unguwar Kampala

Kampala Development Forum, Kungiyar cigaban unguwar Kampala Chairman: Maiunguwa Ibrahim Z***r Al-kampaly

This page is meant to advocates the activities of Kampala Community and it's, Selfless Services to Humanity by Self Help Group Kampala Development Forum(KDF) Registered Community Base Organization.

*KODA KAI NE MAFI HAZAKA, IDAN KANA WURI MARA KYAU BAZA A SAN DARAJARKA BA*Mutane da yawa suna zargin kansu da rashin sa...
13/04/2026

*KODA KAI NE MAFI HAZAKA, IDAN KANA WURI MARA KYAU BAZA A SAN DARAJARKA BA*

Mutane da yawa suna zargin kansu da rashin sa'a ko rashin iya fafutuka, ba tare da sun lura cewa asalin matsalar ba daga su take ba. Koda kai ne kafi kowa kaifin basira a duniya, idan ka dasa kanka a cikin mutanen da basu san kimarka ba, wallahi a banza zaka tsufa.

Ga abubuwa guda biyar da zasu tabbatar maka cewa kana cikin mutanen da ya kamata ka gaggauta canzawa domin tsiratar da makomarka:

1. Suna Kashe Maka Kwarin Gwiwa: Idan duk lokacin da ka kawo sabon tsarin neman kudi ko wata shawarar ci gaba, sai su kawo maka dalilan da zasu nuna maka cewa abin ba zai yiwu ba. Suna amfani da tsoron dake zukatansu wajen dake maka gwiwa. Dole ka canza su kafin su mayar da kai raggo.

2. Basu Girmama Jajircewarka: Kana fita tun asuba kana zage damtse neman halas dinka, amma a wajensu abin dariya ne saboda aikin karfi ne ko sana'a ce karama. Mutumin da bai san zafin neman na kansa ba, ba zai taba girmama kwazon da kake yi ba, sai dai ya kawo maka cikas.

3. Babu Wani Ci Gaba : Ka duba shekaru biyu ko uku baya, idan har babu wani sabon ilimi, dabarar kasuwanci, ko rufin asiri da ka samu a dalilin zamanka a wannan wurin ko a cikin wadannan mutanen, to lallai kasar da ka shuka irin ka bata da taki. Fita ka nemi inda ake maganar ci gaba.

4. Suna Amfani Da Kai Ne Kawai: Darajarka tana fitowa ne a wajensu kawai idan suna da wata matsala da kake da mafitarta. Da zaran ka warware musu damuwarsu ko bukatarsu ta biya, sai su watsar da kai a gefe. Wannan ba nuna kima ba ne, zalunci ne da amfani da basirar mutum a banza.

5. Kana Rasa Natsuwar Zuciyarka: Duk wurin da zaka zauna kaji kullum kana cikin fargaba, bacin rai, ko zargin kanka cewa baka da amfani, wallahi wannan wurin ba naka ba ne. Natsuwa ita ce asalin mizanin samun kudi, a duk inda babu ita, babu arziki ko ka yi fafutuka har sai ka mutu.

Idan har zaka dauki matakin canza wurin zama ko abokan mu'amala zuwa inda ake yaba maka, zaka yi mamakin yadda kofofin nasara zasu bude maka cikin kankanin lokaci. Ka daina yi wa makafi bayanin kyan launi.

Allah ya raba mu da mutanen da zasu rage mana daraja.

Maiunguwa Ibrahim Z***r Al-kampaly Kampala

Ga yadda za kuyi Revalidation na INEC Voters Card dinku cikin sauki 👇🏻INEC REVALIDATION Duk wani dan Nigeria da yayi kat...
04/04/2026

Ga yadda za kuyi Revalidation na INEC Voters Card dinku cikin sauki 👇🏻

INEC REVALIDATION

Duk wani dan Nigeria da yayi katin zabe daga 2011 zuwa 2024 sai yayi revalidation.

Wannan kamar tantancewa ne ba sake Registration bane.

Ba dole sai kaje wajen wani ba, zaka iya yi online akan wayarka.

Idan online zakayi ka shiga wannan website din https://cvr.inecnigeria.org

1. Kayi creating account da details din ka.

2. Ka shigar da VIN number ta jikin katin zaben ka.

3. Za su nuna maka wajen da zaka dauki hoto ka tura.

4. System din zeyi processing domin tabbatar da kaine mai wannan katin zaben.

5. Idan yayi za su turo maka sako cewar revalidation din ka yayi successful.

•Wannan shine kawai revalidation ba wani babban aiki bane.

•Idan kuma physical zakayi sai kaje center mafi kusa ta INEC, ka tafi da katin zaben ka, ka basu bayanen ka, zasuyi maka hoto su tura, idan komai ya kammala za'a turo muku message a phone number ko email shikenan



*Al-kampaly Kampala*

Access the Nationwide Register of Voters, make Claims and raise Objections regarding any registration and provide feedback.

DUK MATASHIN DA BAI MALLAKI WAƊANNAN ABUBUWAN BA, BAI KAI AURE BA SABODA HAKA KU NUTSU..Idan baka mallaki wadannan abubu...
04/04/2026

DUK MATASHIN DA BAI MALLAKI WAƊANNAN ABUBUWAN BA, BAI KAI AURE BA SABODA HAKA KU NUTSU..

Idan baka mallaki wadannan abubuwan da zan lissafo ba, da sauranka inda maganar Aure ne. Aure fa ba wasan yara ba ne, ba kuma kayan yayi ba ne da zaka yi don kaga abokanka suna yi. Nauyi ne babba.

Ga abubuwan da dole sai kana da su kafin ka ce zaka kawo 'yar mutane gidanka:

1. SANA'A WATO HANYAR SAMUN KUDI: Ba ana nufin sai ka zama mai kudin gaske mai motoci ba. Amma dole ne ka kasance kana da tabbatacciyar hanyar neman halas din da zaka iya sayar mata da abinci, ka bata kudin asibiti idan bata da lafiya, da kuma sutura. Auren mace ka ajiye ta tana kwana da yunwa saboda baka da aikin yi, babbar mugunta ce da wulakanci.

2. WURIN ZAMA: Bance sai ka gina gidanka ba kafin ka yi aure, amma a kalla ka zama kana da daki ko gidan haya wanda za a rufe kofa asirinku ya rufu, kuma ta samu 'yancin gudanar da rayuwarta ba tare da takura ba.

3. HAKURI DA KAWAR DA KAI: Idan kai mai zafin zuciya ne, kullum kana cikin fada kuma baka daukar magana ko yar karama... to aurenka ba zai dade ba. Mace fa tana bukatar namiji mai hakuri, mai jan aji, kuma mai lallashi a lokacin da ta yi ba daidai ba.

4. ILIMIN ADDINI: Tunda kai ne shugaban gidan, dole ne ka san dokokin addini. Ta yaya zaka jagoranci iyalinka idan kai kanka baka san yadda ake yin sallah daidai ko hukunce-hukuncen zama da mace ba?

Aure a musulunci ibada ce mai girma kuma hanya ce ta rufe asirin juna da kiyaye kai daga sabo. Amma fa Musulunci bai ce ka auro yarinyar mutane ka takura mata ba saboda baka da halin daukar nauyinta. Shiyasa Manzon Allah (SAW) ya ce masu karfin rike aure su yi, marasa karfi kuma su yi azumi domin su kiyaye kansu.

A karshe ina son ku sani cewa, ka daina takura wa kanka ko jefa zuciyarka a damuwa saboda kaga wani abokinka yayi aure. Gina kanka tukunna, ka nemi na kanka yadda zaka tsaya da kafafunka. Idan lokaci yayi, wallahi komai zai zo maka da sauki cikin mutunci.

Allah yasa mu dace.
Chairman KDF
Maiunguwa Ibrahim Z***r Al-kampaly Kampala

A MATSAYINKA NA NAMIJI... TASHI KA NEMI KUDI DA YAWA, SANNAN KA NEMI ILIMI.A matsayinka na namiji, ka tashi ka nemi kudi...
03/04/2026

A MATSAYINKA NA NAMIJI... TASHI KA NEMI KUDI DA YAWA, SANNAN KA NEMI ILIMI.

A matsayinka na namiji, ka tashi ka nemi kudi. Ka neme su da yawa, Bayan haka, ka tashi ka nemi ilimi.

Idan baka san yadda duniyar nan take tafiya ba a yanzu, to ka rike wannan maganar:

Idan mai kudi ya yi babban laifi, a idon mutane cewa ake yi 'kuskure ne, dan adam ajizi ne.' Amma idan talaka ya yi dan karamin kuskure, cewa ake yi 'asalinsa ma dan iska ne, ku kulle shi.

Duniya bata da adalci ga mutumin da bashi da kudi a hannunsa. Talauci yasa ana yi wa mutum kallon mai laifi koda bashi da laifi.
Kudi da ilimi sune zasu kare maka mutuncinka a wannan zamanin.

Gane wannan bambancin a yau, sannan ka dauki matakin tashi ka fita ka nemi na kanka, ka nemi yancin kanka kafin a mayar da kuskurenka babban laifi a idon mutane.

Rashin kuɗi yana jawo wulakanci.....

Allah yasa mudace.
Chairman KDF
Maiunguwa Ibrahim Z***r Al-kampaly

03/04/2026

JUMA'AT MUBARAK PRAY FOR HADEJIA EMIRATE JIGAWA STATE AND NIGERIA🇳🇬

‎🤲 Ya Allah, Ka albarkaci Hadejia, jihar jigawa da Nigeria 🇳🇬, Ka tsare garinmu daga dukkan matsaloli da suke damun mu, Ka kawar da:

‎Rashin lafiya da cututtuka (ciwon koda,hanta, Cizon sauro da sauran cututtuka masu barazana ga rayuwa).

‎Rashin aikin yi da talauci, da duk abin da ke hana jama’a samun rayuwa mai dadi.

‎Rashin tsaftar muhalli, matsalolin ruwa da magudanan ruwa, da sauran abubuwan da ke hana ci gaban gari.

‎Rashin zaman lafiya, rashin tsaro, da dukkan abubuwan da ke kawo tashin hankali.

‎✨ Allah Ka albarkaci shugabanninmu na sarauta da siyasa, Ka basu hikima, adalci, da juriya wajen jagoranci, domin su kawo ci gaba mai dorewa a wannan al'karya🤲

‎🌿 Allah Ka sanya Hadejia ta zama garin da kowa zai yi alfahari da shi:

‎Garin da aka cika da ilimi da fasaha.

‎Garin da tattalin arziki ya bunkasa.

‎Garin da matasa da mata suke samun dama da cigaba.

‎Garin da al’ummar sa s**a hada kai, s**a tallafa wa juna.


‎💚 Ya Allah, Ka sa mu mu kasance masu kishin Hadejia, masu aiki tukuru, masu soyayya da garinmu. Ka albarkaci kowane ɗan Hadejia, Ka hada mu duka domin gini, bunkasa, da ci gaban garinmu.

‎🌟 Ya Allah, Ka cika burin Hadejia, Ka sa ta zama misali ga dukkan garuruwa a Najeriya da duniya baki ɗaya.

‎Hadejia People’s Union – Don al’umma, don ci gaba, don kasar Hadejia.


‎©️HADEJIA PEOPLE'S UNION✍️

‎➡️ https://t.me/HADEJIASTATE ⬅️




DA ACE KA SAN IRIN NATSUWAR DA KE CIKIN SAMUN KUƊI, WALLAHI BAZA KA TAƁA YIN WASA DA FAFUTUKARKA BA.Talauci surutu ne da...
31/03/2026

DA ACE KA SAN IRIN NATSUWAR DA KE CIKIN SAMUN KUƊI, WALLAHI BAZA KA TAƁA YIN WASA DA FAFUTUKARKA BA.

Talauci surutu ne da shi, yana kawo wulakanci, rashin mutunci, da kuma yawan fargaba. Amma kudi na halas... zallar natsuwa ne.

Da ace kasan yadda kwakwalwarka zata huta a ranar da ka mallaki naka, da baka taba wasa da sana'arka ba:

1. Natsuwar Gida: Jin cewa zaka iya biyawa mahaifiyarka, kannenka ko iyalinka bukatunsu a take ba tare da ka roki wani yayi maka gori ba, wata irin Aljannar duniya ce wacce sai wanda ya dandana yake gane ta.

2. Yancin Yin Shiru: Idan kana da kudi, baka bukatar yin dogon bayanin karya don a girmama ka. Natsuwarka kadai ta isa ta yi maka magana a ko'ina ka shiga.

3. Kyamar Kasala: Idan ka fahimci wannan sirrin, zaka daina yawan baccin asara, zaka daina kashe lokacinka a kan hirar banza ko Social Media babu fa'ida. Zaka mayar da hankali kan kasuwancinka dari-bisa-dari.

Ka Tashi ka nemi na kanka ta hanyar halas domin ka sayi natsuwarka. Kudi zai taimaka maka wajen samun Aljanna, kuɗi zai baka damar neman ilimi mai inganci.

Allah yasa mudace.
Chairman KDF
Maiunguwa Ibrahim Z***r Al-kampaly

MENENE YASA SUKE MANA HAKA? Mu matasa ne, masu nema cikin wahala da kunci, muna faɗi tashin don rufawa kanmu asiri, babu...
31/03/2026

MENENE YASA SUKE MANA HAKA?

Mu matasa ne, masu nema cikin wahala da kunci, muna faɗi tashin don rufawa kanmu asiri, babu wanda ya damu da mu babu wanda yake taimakon mu. Duk wata damuwa sai dai mu hadiye ta. Muna da buruka amma sun kasa cikuwa, rayuwa ko ta ina babu sauki. Ga iyaye, ga kanne... Wasu ma iyayen sun rasu sun bar su da dawainiyar kannen su.

Amma duk da haka, mutane baza su bar mu ba. Kullum sai sun nemo hanyar da zasu karya mana zuciya! Kullum sai zargi, hassada, da kuma kokarin toshe kofofin da muke gani zasu bulle mana.

Zaka ga matashi yana fafutuka, wani yana can yana matsin lambar yadda zai kammala final year project dinsa a jami'a cikin matsanancin kunci don ya canza tarihin gidansu. Wani kuma yana can yana kera karamin kasuwancinsa da guminsa don ya ciyar da kannensa marayu. Amma a maimakon mutane su taya mu da addu'a ko su karfafa mana gwiwa, sai su koma gefe suna yi mana hassada, suna yi mana bakin ciki a kan 'yar gumin da muke hadawa. Idan ka fadi su yi maka dariya, idan ka tashi su nemi rusa ka.

Ya Allah.. Ya Allah Ka dube mu da rahamarKa. Ya Allah Ka karfafa mana gwiwa a fagen dagan da muka tsinci kanmu, Ka wanke mana kuncin rayuwar nan, Ka kare mu daga sharrin masu bakin ciki da mu.

Allah yasa mudace.
Chairman KDF
Maiunguwa Ibrahim Z***r Al-kampaly Kampala

ABUBUWA 7 DA SUKE MAYAR DA SANA'O'IN MATASA BAYA.Akwai sana'o'i masu albarkar gaske, amma akwai abubuwan da suke mayar d...
30/03/2026

ABUBUWA 7 DA SUKE MAYAR DA SANA'O'IN MATASA BAYA.

Akwai sana'o'i masu albarkar gaske, amma akwai abubuwan da suke mayar da matasa baya da yawa. Kafin wasu shekaru, zaka samu sana'ar ta mutu murus ba don babu riba ba, sai don wadannan guba guda 7:

1. Masu Bashi:
Mutanenmu idan suna da kuɗi a hannu, sun fi son su wuce ka su je manyan shagunan waje su sayo waya, kaya ko wani aiki. Amma duk ranar da basu da kuɗi a hannu, gurinka zasu zo su yi maka magiya ka basu a bashi, sannan su rika wulakanta ka wajen biya. Suna lalata maka lissafin jari.

2. Hassadar Na Kusa:
Mutane basa son tallafa wa na kusa da su. Da zarar ka fara wani kasuwanci, mutane na kusa da kai gefe zasu koma suna kallonka, suna jiran ranar da zaka fadi kwai don su yi maka dariya.

3. Cinye Jari Don Burge Mutane:
Matashi yana samun 'yar riba a kasuwanci, maimakon ya juya kudin ya saro wasu kayan, sai ya je ya sayi sabuwar waya mai tsada ko tufafin alfarma don ya burge 'yan matan da ba su san lokacin da yake cin kwakwa ba. Wannan hauka ne.

4. Gasar Banza Da Masu Kudi:
Kokarin karya farashin kayanka don kawai ka kashe kasuwar wani wanda ya riga ka fita. Kana rage riba har ka fara cinye jarinka baka sani ba.

5. Raini Da Wulakanta Kwastoma:
Idan ka fara samun kudi, ka fara yi wa masu karamin karfi wulakanci a shagonka ko a wajen aikinka. Kwastoma daya da ka wulakanta, zai iya kora maka guda goma a boye.

6. Rashin Hakuri Da Juriya:
Fara kasuwanci yau, don kaga baka zama miliyoniya a wata daya ba, sai ka kulle ka fara wani daban. Babu bishiyar da take ba da 'ya'ya a ranar da aka shuka ta.

7. Rashin Tsari Da Lissafi:
Kasuwancin da babu lissafin abin da ya shigo da wanda ya fita. Kudi na shiga aljihunka kana kashewa ba tare da ka raba ribarka da asalin jarinka ba.

Saboda haka matasa na, ku zama wise, Ka tantance mutanen da suke neman ka ci gaba, da mutanen da suke kokarin karya ka.

Ka sani, mutane da yawa suna jiran su ga ranar da shagon zai gagare ka, ka rufe, ko kasuwanci ko aikin da kake ya mutu don su yi farin ciki da dariya. To amma in sha Allah, zasu yi jiran har abada, Muna nan daram✊️.

Allah yasa mudace.
Chairman KDF
Maiunguwa Ibrahim Z***r Al-kampaly Kampala

As today our able and vibrant Chairman KDF celebrate the Birthday 🎂 of 27th of March, Marks the 48 years More grease to ...
27/03/2026

As today our able and vibrant Chairman KDF celebrate the Birthday 🎂 of 27th of March, Marks the 48 years
More grease to your elbow, years with graces sir.

27/03/2026

I got over 50 reactions on my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

Address

ICT NITDA, Kampala Quarters, Mallam Madori LGA
Hadejia
730101

Telephone

+2348052327872

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kampala Development Forum, Kungiyar cigaban unguwar Kampala posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Kampala Development Forum, Kungiyar cigaban unguwar Kampala:

Share