29/08/2026
Gidauniyar Guga Global Foundation ta gana da Shugabanninta na Ƙananan Hukumomi da Masu Kula da Shiyyoyi a Katsina.
A ranar Asabar 29 ga Agusta 2026,Gidauniyar Guga Global Foundation ta gudanar da wani muhimmin taron tattaunawa da masu kula da ayyukanta na shiyyoyi uku, da kuma shugabanninta na ƙananan hukumomi a faɗin Jihar Katsina, domin ƙara inganta ayyukan jinƙai da tallafawa marasa galihu da gidauniyar ke gudanarwa karkashin jagorancin shugaban ta Hon. Abduljabbar Surajo Guga.
Taron ya gudana a babban dakin taro na gidauniyar da ke kusa da babban filin wasa na Muhammad Dikko, a cikin birnin Katsina. Inda taron ya mayar da hankali ne kan tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi tafiyar da ayyukan gidauniyar, da kuma nada sabbin shugabanni na wucin gadi a wasu matakai, domin samun saukin gudanar da ayyukan alheri da gidauniyar ke shimfiɗawa a sassa daban-daban a Jihar Katsina.
Da yake gabatar da jawabin sa shugaban gidauniyar, Hon. Abduljabbar Surajo Guga, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa aka kafa gidauniyar shi ne, tallafa wa marayu da marasa ƙarfi, musamman wajen samun ingantaccen ilimin zamani da na addini.
Ya kara da cewa, kashi 95 cikin 100 na ayyukan gidauniyar an mayar da hankali ne kan taimaka wa marayu da marasa karfi domin su samu damar yin karatu kamar yadda suke ganin sauran yara a makarantu, yayin da sauran kashi 5 cikin 100 na tafiya ne wajen gudanar da wasu ayyukan taimakon al’umma.
Hon. Guga ya bayyana taron na wannan rana a matsayin wani ɓangare na ƙara faɗaɗa ayyukanta zuwa dukkan shiyyoyi da ƙananan hukumomin jihar.Ya ce shugabanninta na ƙananan hukumomi da masu kula da shiyyoyi za su shiga cikin al’umma domin gano marayu da marasa ƙarfi, waɗanda za su samu damar cin gajiyar wannan gidauniyar kai tsaye.
Ya kuma bada tabbacin cewa, gidauniyar za ta ɗauki nauyin karatun yara da buƙatunsu, tun daga matakin firamare har zuwa sakandare, domin tabbatar da suma ba su fuskanci wata matsala wajen ilimisu ba.
Daga karshe ya yi kira ga shugabannin gidauniyar da su ci gaba da sanya ido kan yaran da aka ɗauki nauyinsu, tare da bibiyar yadda suke karatu da halartar makarantunsu dan samun damar tattara bayanan yaran da sakamakon jarabawarsu domin a iya tantance ƙwazonsu da basirarsu, tare da taimaka musu wajen samun guraben karatu a manyan makarantu idan sun kammala matakan karatunsu na daya da na biyu.
Taron ya samu halartar masu kula da ayyukan gidauniyar daga shiyyoyi daban-daban da kuma shugabanninta na ƙananan hukumomi na Jihar Katsina.