Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah - Gombe - Nigeria

Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah - Gombe - Nigeria �� الاعتصام بالكتاب والسنة علىٰ منهج السلف الصالح
Adherence to the Qur’an and the Sunnah according

A yanzu babban abunda muke yi shine Makarantar Islamiyyah me suna *Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah Islamic Academy - Go...
15/10/2025

A yanzu babban abunda muke yi shine Makarantar Islamiyyah me suna *Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah Islamic Academy - Gombe - Nigeria* wacce tahaɗa da 6angare uku:
1. Ɓangaren yara (maza da mata) da,
2. Ɓangaren Maza (manya) da,
3. Ɓangaren Mata (manya).

Duk me buqata zai shiga ko zaisa wani ya QIRA wannam lambar:

+2347044574870.

11/10/2025

📢
Muna gayyatar maza da mata, matasa da tsofaffi kowa da kowa – ku zo ku shiga cikin wannantafiya mai albarka.
Mu koyi addininmu bisa Qur’ani da Sunnah – kamar yadda Annabi صلى الله عليه وسلم da Sahabbanshi s**ayi.

Ma’anar Kalmar Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah - Gombe - Nigeria:Kalmar Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah daga larabci n...
11/10/2025

Ma’anar Kalmar Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah - Gombe - Nigeria:
Kalmar Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah daga larabci ne tushenta wato والجماعة السنة أهل مركز Cibiyarilimi da tarbiyya ta Ahlus Sunnah Wal Jama'ah (wato Mabiyan hanyar Annabi Muhammad صلى الله عليه وسلم dasahabbanshi, a kan tauhidi, ibada da aƙida ingantacciya) wacce take cikin garin Gombe aqasar/jamhuriyyar Nigeria.

Ma'anonin Alamun cikin tambari (logo/symbol/badge):
Kalmar Shahada/shaidar bangaskiya لا إله إلا الله محمد رسول الله: dake sama ita ce tubalin ginin
Musulunci. Kasancewarta a cikin tambarin Markazu Ahlis Sunnah wal-Jamā‘ah na nuna cewa manufarMarkaz ɗin ta ginu gaba ɗaya ne a kan Tauhidi (riko da Allah shi kaɗai) da kuma bin Sunnah taManzon Allah Muhammad صلى الله عليه وسلم kuma itace a can sama sabida kalmar Allah Itace maɗaukakiya.

📖 Littafi mai shafuka a buɗe: yana nuni da Al-Qur’ani da sauran ilimummuka.

🌴 Itacen dabino saman littafin: alamar albarka, da yalwa da yaɗuwa da tsawon rai da rayuwa irinta Sunnah.

⚔ Takobi ƙarƙashin littafi: alamar ƙarfi, kariya ga addini da tauhidi da aqida da Sunnah da yaqarbidia.

🛡 Siffar garkuwa (shield shape): Tana nuna tsaro, da baiwa Sunnah kariya, da tsayin daka akanAqida da manhajar Salafus-Salih don kare musulunci daga shirka da bidi’a da jahilci da son zuciya dasharrin makiya.

Koren launi (Green colour): Alamar Musulunci ce, da ake danganta da aljanna, zaman lafiya, datsarkin zuciya. Yana nuni da rayuwa, ci gaba da albarka da alheri
Farin launi (White color): Yana wakiltar tsarki, gaskiya, da ilimi mai kyau. kuma yana nuna sulhuda rashin wariya da zaman lafiya. Kuma yana nuni da tsarkin aƙida da ilmantarwa bisa Littafi daSunnah.

Launin zinariya (Golden colour): a cikin wannan tambari yawanci yana nuni da: kyakkyawan
daraja da kima kuma yana wakiltar babban matakin ilimi da al’ada ta Sunnah da aiki da shi kumahakan na nuni da shiryarwa daga Al-Qur’ani da Sunnah.

Taken mu (motto) :
Riqo da Alqur'ani da Sunnah bisa tafarkin Salafus Salafus Salih.

Hangen Nesa/Hasashenmmu (Vision):
Gina al’umma mai tsarkakakkiyar aƙidah ta Assalafiyyah kyawawan dabi’u, tsoron Allah, da haɗinkai – wacce take rayuwa bisa Qur’ani da Sunnah kamar yadda Salafus-Salih s**a fahimta kuma s**aaikata – domin gyaran tarbiyya da samun nasara a duniya da lahira.”

Abin da ya bambanta Markaz (Unique Proposition):
Haɗa tsarin addini da na zamani cikin tsari guda.
Ginin karatu bisa ingantacciyar Aqidah Salafiyyah.
Malamai masu sahihan hujjoji da tsayawa akan gaskiya.
Shirye-shiryen karatu na musamman ga yara, matasa da manya.
Rashin tsada da tsawwalawa a kuɗin makaranta.

Ginshikan Aiyyuka da mukafi mayar da hankali (Strategic Focus / Pillars):
Koyar da Qur’ani da Hadisi da Sharhinsu.
Koyar da ilimin Shari’a (Fiqh, Usul, Aqidah).
Koyar da ilimin zamani mai amfani (kamar su English, Mathematics, Science, Computer).
Gina tarbiyya da ladabi cikin ɗalibai.
Wayar da kan iyaye da jama’a kan al’amuran shari’a da zamantakewa.

Manufofi da Burin Markaz (Objectives / Goals):
Gina ɗalibai masu aƙida ingantacciyar ta Salafiyyah da ilimi nagari.
Ƙarfafa haɗa ilimin addini da na zamani a tsari guda.
Samar da malamai da shugabanni masu gaskiya da aminci.
Gina al’umma mai tarbiyya da bin shari’a.
Wayar da kan iyaye da jama’a kan muhimmancin tarbiyyar ‘ya’ya.

Falsafar Asali (Philosophy):
Markazus Ahlis Sunnah Wal Jama‘ah ya ginu bisa Akidar Salafiyyah, wato riko da Qur’ani da Sunnahbisa fahimtar Sahabbai da Tabi’ai, ba tare da bidi’a ba.
Kuma Markaz ɗin ya dogara ne akan ƙa’idar cewa babu cikar Musulunci sai da haɗa limi da tarbiyya alokaci guda.

Tsarin Gudanarwan (Organizational Structure):
Shugaban Markaz / Director.
Mataimakin Shugaban Markaz.
Sashen Malamai da Karantarwa.
Sashen Gudanarwa da Tarbiyya.
Sashen Hulɗa da Jama’a.

Shirye-shiryen Karatu (Programs & Curriculum): Qur’ani: Koyarwa da haddar Qur’ani, Tafsiri.
Hadisi: fassara da sharhinsu.
Aqidah da Tauhidi na Ahlus Sunnah (Salafiyyah).
Fiqhu: Koyar da fiqh na ibada da mu’amala bisa hujja.
Lugga: Larabci da Hausa (kalmomi, nahawu, sarfu, balaga).
Ilimin usul: (kamar su musɗalah da usulul fiqh da usulut tafsir da sauran usul).
Tarbiyya da Ladabi: Ladabi, zamantakewa da ilimin halayya.
Darussa na musamman: (kamar darrussan mata, darrussan matasa da sauransu).
Ilimin zamani: English, Mathematics, Science, Computer da sauransu.

Nasarori da Ci gaba (Achievements):
Yawan ɗaliban da s**a haddace Qur’ani.
Gudanar da taron ilmantarwa a cikin al’umma.
Haɓaka malamai da masu koyarwa.
Horar da matasa wajen tarbiyya da aƙida ingantaciya ta Salafiyyah.

Tsarinmmu a gaba (Future plans) :
Faɗaɗa Markaz zuwa matakin jamia ta Ahlus Sunnah.
Faɗaɗa makarantu zuwa ƙauyuka da garuruwa.
Gina cibiyar koyon sana’o’i (skill center) da ƙirƙirar asibiti da cibiyar lafiya da media Station (kafofin sadarwa kamar gidan radio ko talabijin watau TV) da court/Chambers/Counseling Room (kotu da ɗakin shawarwari da sulhu da community Service Center (Wurin taimako) da islamic Bank and Financial Institution (Banki da gurin gudanarwan kuɗaɗe me tsarin Musulunci) da ɗakin Taro (Conference/Multipurpose Hall) da hostel (ɗakin kwanan ɗalibai) da guest rooms wato ɗakunan
karɓan baqi.


Kayan Aiki (Facilities):
Masallaci.
Library (ɗakin karatu) na addini da na zamani.
Computer Lab.
Classrooms masu tsafta.
Dormitory da Hostel (ɗakunan kwana) ga ɗalibai maza.

Shigar Makaranta da Dokoki (Admission & Rules):
Shigar makaranta na buƙatar ɗalibi ya kasance yana da tarbiyya da sha’awar neman ilimi.
Dole ne ya kiyaye dokokin makaranta kamar: girmama malamai, da girmama juna da bin dokokin karatu, nisantar bidi’a da halaye marasa kyau.
Yin rajista da cikakken bayanai.
Bin dokokin makaranta.
Rashin halartar bidi’a da taron bidi’a, ko ayyukan da s**a sabawa Sunnah.
Yin sallah tare a lokacin jama’a.
Tsabtace muhalli.
Da sauran abubuwan da aka rubuta acikin form/admission na dokokin.

Game da Mu (About Us / Who We Are / History):An kafa Markazus Ahlis Sunnah Wal Jamaah a watan Muharram, 1447 A.H. a gari...
11/10/2025

Game da Mu (About Us / Who We Are / History):
An kafa Markazus Ahlis Sunnah Wal Jamaah a watan Muharram, 1447 A.H. a garin Gombe a ƙasar Nigeria domin yada ilimi sahihi bisa Qur’ani da Sunnah, tare da tarbiyya bisa fahimtar Salafus-Salih.
Manufarmu itace ceto al’umma daga jahilci da bidi’a, ta hanyar ilmantarwa da tarbiyya. Markazu AhlisSunnah Wal Jama'ah Cibiyace ta musulunci (wato Islamic Centre) da take gudanarwan ayyukan addini
musamman karantarwa bisa tsarin Alqur'ani da Sunnah akan tafarkin Salafus Salih wanda tushentana aqidah ne, aqidar Ahlus Sunnah Wal Jama'ah (Assalafiyyah).
An qirqiri wannam cibiyar ce don ciyar da aqidar Ahlus Sunnah Wal Jama'ah (Assalafiyyah) cigabawanda muka kawo waensu ayyukan da muke gabatarwa kamar karantarwa da sauran abubuwakamar:
1. Ofisoshi (Offices): na shugabannin markazin da Ofishin gudanarwa (Management office) da Ofishinkula da al’umma (Community services office) daOfishin bada shawarma (Counseling),wanda shine abu
na farko da muke ƙoƙarin kawowa insha Allah.
2. Masallaci (Wurin salla): Domin gudanar da sallah guda biyar acikin yini da juma'a da sauranibadu wanda ya had'a sallar maza da mata da wurin tsarki (wudu area) na maza da na mata, wandashine abu na biyu da zamu kawo insha Allah a Wannanm Markazin.
3. Makaranta: Islamic School / Madrasa da kuma Makarantar Boko/Western/Secular Educationdon Koyar da Qur'ani da tajweed da koyar da Hadisi, Fiqhu, Tauhidi, da sauran fannoni na addini dadarussa na yara da manya mata da maza koyar da larabci gyaran akida da tarbiyya da sauransu Dakuma ilimin boko ko ilimin zamani, kuma wannam shine abu na uku da muke ƙoƙarin kawowa inshaAllah.
4. Library da Publication, Research & Da’awa Unit: wato ɗakin karatu da Wurin Gidauniyar Ilimida nazarin harkokin Musulunci don shirye-shiryen da’awa da yaduwar ilimi da fiitar da wallafe￾wallafe da da buga littattafan na Qur’ani da Sunnah, da sauran ilimummuka na da da na zamani das**a dace da Musulunci, kuma wannam shine abu na huɗu da muke ƙoƙarin kawowa insha Allah, sabida buqatuwarmu zuwa gareshi da muhimmancinshi kuma markazinmmu zatafi mayar da hankaliakan wannam fiye da komai insha Allah.
5. University (Jami'a): wacce ake koyar da manyan ɗalibai (advanced Students) kuma ake bayardasheda (certification) na diploma da degree da masters da Ph. D da ma Professor da sauran sheda nailimummuka akan courses na addini kamarsu Aqidah da Hadisi da Qur’ani da Fiqhu da sauranilimummuka na addini da na zamani, kuma wannam shine abu na biyar da muke ƙoƙarin kawowainsha Allah.
6. Ɗakin koyar da sana’o’i (Skills Center): don koyar sana’o’in hannu da na zamani kamar su ɗinki,tukwane, fasahar kwamfuta, koyar da kasuwanci, da sauransu da ma koyar da ilimin rayuwa (lifeskills), kuma wannam shine burinnmmu na shida insha Allah.
7. Media Station (kafofin sadarwa kamar gidan radio ko talabijin watau TV): don ƙara yaɗa
daawah da cigaban addini, birane da ƙauyuka/karkara da lunguna da saquna a faɗin duniya, kumawannam yana ma daga cikin manya manyan burukanmmu.
8. Court/Chambers/Counseling Room (kotu da dakin shawarwari da sulhu): do shwarwarida
sulhu kamar shawarwari na aure da sauran abubuwa kamar shawarwarin matasa.
9. Hospital /Clinic/Health Unit/First Aid (Asibiti da gurin jinyan marasa lafia da Wurin Tsabtace
Jiki da Ayyukan temakon lafiya na farko): don ayyukan lafiya kamar su hijama (cupping) da
taimakon lafiya ga mabuƙata da taimakon gaggawa.
10. Community Service Center (Wurin taimako): don raba abinci ga mabuƙata da taimakon marayuda zawarawa tallafi ga masu matsala da shirye-shiryen agaji da banking na zakka da tallafi dasauransu.
11. Dakin Taro (Conference/Multipurpose Hall): domin gudanar da karatu da darussa da taron iyayeda malamai da taron biki da walima da sauransu.
12. Islamic Bank and Financial Institution: (Banki da gurin gudanarwan kuɗaɗe me tsarin musulunci.
13. Tsarin samar da tsaro: don kyautata wuri da Hisbah wanda duka munada burin kawowa insha
Allah.
14. Hostel da guest rooms: wato ɗakunan ɗalibai na nesa da ɗakunan karɓan baqi.

Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah - Gombe - Nigeria:*Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah - Gombe - Nigeria*  Cibiyace ta mus...
28/09/2025

Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah - Gombe - Nigeria:
*Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah - Gombe - Nigeria* Cibiyace ta musulunci (wato Islamic Centre) ta take gudanarwan ayyukan addini musamman karantarwa bisa tsarin Alqur'ani da Sunnah akan tafarkin Salafus Salih wanda tushenta na aqidah ne, aqidar Ahlus Sunnah Wal Jama'ah (Assalafiyyah).

Mun qirqiri wannam cibiyar ce don ciyar da aqidar Ahlus Sunnah Wal Jama'ah cigaba wanda muka kawo waensu ayyukan da muke gabatarwa kamar karantarwa da sauran abubuwa kamar:

1️⃣ Ofisoshi
Ofishin Imam ko Sheikh wato Director ko Chairman na duka markazin
Da Ofishin gudanarwa (Management office).
Da Ofishin kula da al’umma (Community services office).
Da Ofishin bada shawara (Counseling),wanda shine abu na farko da zamu fara kawowa insha Allah.

2️⃣ Masallaci (Wurin salla)
Domin gudanar da sallah 5 cikin yini da juma'a da sauran ibadu wanda ya had'a sallar maza da mata da wurin tsarki (wudu area) na maza da na mata, wanda shine abu na biyu da zamu kawo insha Allah a Wannanm Markazin.

3️⃣ Makaranta (Islamic School / Madrasa da kuma Makarantar Boko/Western/Secular Education )
Koyar da Qur'ani da tajweed.
Koyar da Hadisi, Fiqhu, Tauhidi, da sauran fannoni na addini da darussa na yara da manya mata da maza koyar da larabci gyaran akida da tarbiyya da sauransu Da kuma ilimin boko ko ilimin zamani, kuma wannam shine abu na uku da zamu kawo Insha Allah.

4️⃣ Library da Publication, Research & Da’awa Unit wato d'akin karatu da Wurin Gidauniyar Ilimi da nazarin harkokin Musulunci Don shirye-shiryen da’awa da yaduwar ilimi da fiitar da wallafe-wallafe da da buga littattafan na Qur’ani da Sunnah, da sauran ilimummuka na da da na zamani da s**a dace da Musulunci, kuma wannam shine abu na hud'u da zamu kawo Insha Allah sabida buqatuwarmu zuwa gareshi da muhimmancinshi kuma markazinmmu zatafi mayar da hankali akan wannam fiye da komai insha Allah

5️⃣ University (Jami'a) wacce ake koyar da manyan d'alibai (advanced Students) kuma ake bayarda shed a (certification) na diploma da degree da masters da Ph. D da ma Professor da sauran sheda na ilimummuka akan courses na addini kamarsu Aqidah da Hadisi da Qur’ani da Fiqhu da sauran ilimummuka na addini da na zamani, kuma wannam shine abu na biyar da zamu kawo Insha Allah.

6️⃣ Dakin koyar da sana’o’i (Skills Center) don koyar sana’o’in hannu da na zamani kamar su dinki, tukwane, fasahar kwamfuta, koyar da kasuwanci, da sauransu da ma koyar da ilimin rayuwa (life skills), kuma wannam shine burinnmmu na shida insha Allah.

7️⃣ Media Station and Unit (kafofin sadarwa kamar gidan radio ko talabijin watau TV) don qara yad'a dawaa da cigaban addini, birane da qauyuka/karkara da lunguna da saquna a fad'in duniya, kuma wannam yana ma daga cikin manya manyan burukanmmu.

8️⃣ Court/Chambers/Counseling Room (kotu da dakin shawarwari da sulhu
Shawarwari na aure da sauran abubuwa kamar shawarwarin matasa.

9️⃣ Hospital /Clinic/Health Unit/First Aid (Asibiti da gurin jinyan marasa lafia da Wurin Tsabtace Jiki da Ayyukan temakon lafiya na farko)
Hijama (cupping).
Taimakon lafiya ga mabukata.

🔟 Community Service Center (Wurin taimako)
Raba abinci ga mabukata.
Taimakon marayu da zawarawa tallafi ga masu matsala da shirye-shiryen lafiya da agaji.
Banking na zakka da tallafi da sauransu.

1️⃣1️⃣ Dakin Taro (Conference/Multipurpose Hall) domin gudanar da:
Karatu da darussa
Da Taron iyaye da malamai
Da Taron biki da walima da sauransu.

1️⃣2️⃣ Islamic Bank and Financial Institution (Banki da gurin gudanarwan kud'ad'e me tsarin Musulunci).

1️⃣3️⃣ Tsarin samar da tsaro da Kyautata Wuri da Hisbah wanda duka munada burin kawowa insha Allah.

1️⃣4️⃣ Hostel da guest rooms wato d'akunan d'alibai na nesa da d'akunan kar6an baqi.

Muna waennam ayyukanne don neman sakamako me kyau me yawa da rabauta agurin Allah Ubangiji Maɗaukaki domin gina Markaz ko temakawa cigaban addini ko taimakawa wajen ƙarfafa ayyukan addini yana daga cikin ayyukan da ke da dimbin lada a duniya da lahira. Sabida

1. قال رسول الله صلى الله عليه وسلم "من سن في الإسلام سنة حسنة فله أجرها وأجر من عمل بها بعده، من غير أن ينقص من أجورهم شيء... “Duk wanda ya ƙirƙiro kyakkyawan (aiki) a Musulunci, yana da ladarsa, da kuma lada na duk wanda ya bi sawunsa har abada, ba tare da an rage ladar kowa ba.”
Muslim, Hadisi na 1017)

2. قال رسول الله ﷺ:
"من دلَّ على خيرٍ فله مثلُ أجرِ فاعلِه."
[رواه مسلم – الحديث رقم 1893]
“Wanda ya jagoranci wani alheri (ya nuna hanya ko ya kira wani zuwa alheri), yana da lada kamar na wanda ya aikata shi.”

3. قال رسول الله ﷺ:
"إذا مات الإنسان انقطع عمله إلا من ثلاثة: صدقة جارية، أو علم يُنتفع به، أو ولد صالح يدعو له."
[رواه مسلم – الحديث رقم 1631]
Manzon Allah ﷺ ya ce:
"Idan mutum ya mutu, dukkan ayyukansa sun yanke sai daga abubuwa uku:
Sadaqa me gudana,
Ko ilimi da ake amfani da shi,
Ko yaro nagari da ke yi masa addu’a."

4. قال رسول اللهﷺ: والله في عون العبد ما كان العبد في عون أخيه
Allah ya cikin temakon bawa matukqar bawa yana cikin temakon d'an uwanshi
(Bukhary da Muslim)

مَنْ كَانَ فِي حَاجَةِ أَخِيهِ، كَانَ اللَّهُ فِي حَاجَتِهِ، وَمَنْ فَرَّجَ عَنْ مُسْلِمٍ كُرْبَةً، فَرَّجَ اللَّهُ عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ، وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِمًا، سَتَرَهُ اللَّهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ
Duk wanda yake cikin biyan buƙatar ɗan'uwansa, Allah zai kasance cikin biyan buƙatarsa. Duk wanda ya rage wa musulmi wata damuwa, Allah zai rage masa damuwa daga damuwar ranar Kiyama. Duk wanda ya rufe (asirin) musulmi, Allah zai rufe asirinsa a ranar Kiyama
Bukhari da Muslim

أَحَبُّ النَّاسِ إِلَى اللَّهِ أَنْفَعُهُمْ لِلنَّاسِ
Mafi soyuwa a wajen Allah daga cikin mutane shi ne wanda yafi amfani ga mutane.
Sahih al-Bukhari (Hadisi na 6026) da Sahih Muslim

إِنَّ الصَّدَقَةَ لَتُطْفِئُ غَضَبَ الرَّبِّ
Lallai sadaka tana kashe fushin Ubangiji.
Sunan Ibn Mājah (Hadisi na 2431) – Hasan

أَحَبُّ الأَعْمَالِ إِلَى اللَّهِ سُرُورٌ تُدْخِلُهُ عَلَى مُسْلِمٍ، أَوْ تَكْشِفُ عَنْهُ كُرْبَةً، أَوْ تَقْضِي عَنْهُ دَيْنًا، أَوْ تَطْرُدُ عَنْهُ جُوعًا.
Mafi soyuwa daga ayyuka a wajen Allah shi ne farin ciki da ka sa wa musulmi, ko ka rage masa wata damuwa, ko ka biya masa bashi, ko ka kore masa yunwa.
Muslim

مَثَلُ الَّذِينَ يُنْفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أَنبَتَتْ سَبْعَ سَنَابِلَ فِي كُلِّ سُنبُلَةٍ مِّائَةُ حَبَّةٍ ۗ وَاللَّهُ يُضَاعِفُ لِمَن يَشَاءُ ۗ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ
Misalin waɗanda suke ciyar da dukiyarsu a kan hanyar Allah, kamar irin hatsi da ya tsiro da kawuna bakwai, a kowace kawanar akwai ɗari. Allah yana ninka (lambar lada) ga wanda Yake so, kuma Allah Mai yalwa ne, Masani."
Suratul Baqarah, Aya ta 261.

Sabida haka duk wanda yasamu damar ire iren waencan ayyuka kada yayi wasa da damar, ko a wane hali kake ciki tabbas kana damar aikata haka ko sashen wani abu daga ciki ko temakon masu aiwatarwa ta hanyar qarfinka ko dukiyarka ko shawarinka ko kulawarka ko iliminka don yin tarayya acikin ladan.

Allah Ya sa mu kasance cikin masu taimakawa addini da ilimi da ibada. Ameen

Address

Gombe
Gombe
760242

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Markazu Ahlis Sunnah Wal Jama'ah - Gombe - Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share