G O M B E C I T Y

G O M B E  C I T Y Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from G O M B E C I T Y, Community Center, Gombe.

GOMBE STATE TODAY.GOMBE GIDA. Gombawa Gombe State University, Gombe Nigeria Gombe People's Forum GOMBE SOCIAL MEDIA Gomb...
23/07/2025

GOMBE STATE TODAY.
GOMBE GIDA.
Gombawa
Gombe State University, Gombe Nigeria
Gombe People's Forum
GOMBE SOCIAL MEDIA
Gombe state social media

04/07/2025

Gwamnan jihar Gombe kuma shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewacin Najeriya, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa jihar Kano, domin ta'aziyya ga iyalan marigayi attajirin ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata.

Tawagar ta samu tarba daga babban ɗa ga marigayin kuma dattijon ƙasa, Alhaji Tajudeen Aminu Ɗantata, tare da dattijo kuma jigo na ƙasa, Alhaji Sani Zangon Daura, da sauran iyalansa.

Yayin da yake jawabi gwamna, Inuwa Yahaya, ya bayyana marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a matsayin dattijo mai daraja da ƙima, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bunƙasa kasuwanci, ilimi da harkokin jin ƙai, yana mai cewa, gudummawarsa ta bar gagarumar alama ba kawai a Arewacin Najeriya ba, har ma a faɗin ƙasar baki ɗaya.

"A madadin Ƙungiyar Gwamnonin Arewa da gwamnatin Jihar Gombe da al'ummar jihar, muna miƙa ta'aziyya da addu'o'inmu ga iyalan Ɗantata."

"Mun yi rashin ginshiƙi na gaskiya, mai aiki tuƙuru da tawali'u, rayuwarsa ta kasance cike da hidima, kyautatawa da jajircewa wajen ci gaban Najeriya," in ji Gwamna Inuwa.

An gudanar da addu'o'i na musamman a lokacin ziyarar domin roƙon gafara da rahamar Allah ga marigayin, tare da fatan Allah ya sa ya huta.

Gwamna Inuwa Yahaya ya samu rakiyar manyan jami'ai da dama ciki har da, Arch Yunusa Yakubu, Dakta Jamilu Ishiyaku Gwamna, Alhaji Musa Garba, Kwamishinan Kuɗi da Tattalin Arziƙi, Muhammad Gambo Magaji, da wasu manyan jami'an gwamnati.

08/06/2025

Wata Sabuwa: Bisa al'ada, Wazirin Adamawa Alh. Atiku Abubakar yana zuwa gida a yawancin lokuta na bukukuwa irin wannan, rahotanni daga 'Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa na cewa an jima ba a ga mai Martaba Lamido Dr Barkindo Aliyu Mustapha a irin wadan nan bukukuwa ba.

08/06/2025

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when G O M B E C I T Y posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share