Arewa Entrepreneurship for people with special needs

Arewa Entrepreneurship for people with special needs Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa Entrepreneurship for people with special needs, Non-Governmental Organization (NGO), Gombe.

Wish this gentleman a happy birthday please...He's your brother.
18/09/2023

Wish this gentleman a happy birthday please...

He's your brother.

Sheikh Abubakar Giro Argugu[Rayuwa tayi albarka].Wannan malamin na jima (tun ina firamare) nake jin labarin sa a wajen m...
06/09/2023

Sheikh Abubakar Giro Argugu
[Rayuwa tayi albarka].

Wannan malamin na jima (tun ina firamare) nake jin labarin sa a wajen mahaifina, kasancewar ya gina karantarwan sa akan sunnan ma'aiki (SAW).

Yanzu nake cin karo da labarin mutuwar sa, Allah ya jikansa.

NEMAN TAIMAKO!Kwanakin baya muyi rubutu a shafin nan cewar wata baiwar Allah mai suna Zuwaira Sa'idu, dake zaune a unguw...
08/05/2023

NEMAN TAIMAKO!

Kwanakin baya muyi rubutu a shafin nan cewar wata baiwar Allah mai suna Zuwaira Sa'idu, dake zaune a unguwar Alhaji Ɗan Fulani, cikin garin Kumo.
Tana neman taimako bisa rashin lafiyan Hawan jini da ya lalata sashen ƙafar ta, ga kuma ɗaki guda da take rayuwa ciki na faman lalacewa, ga kuma bayi (toilet) dake gidan ya rushe, matakin da za'a ke kallon mutum daga wajen gidan idan yana biyan bukata.
Saboda haka muka tallafa wajen tura sakon neman 'yen uwa da su taimaka gwargwadon halin su domin jinya da kuma gyara musu muhalli.
Kamar haka:

Account name: Babayo Sulaiman
Account number: 0724790825
Bank name: Access Bank

Domin karin bayani, za'a iya tuntuɓan Waɗannan lambobin:

08168820609, 09019303562, 08067326470.

ALHAMDULILLAH!

Mutane sun karbi wannan sakon da hannu biyu, saboda a yanzu haka mun samu damar gine katangar gidan tareda toshe lungunan gidan.
Wani bawan Allah ya dauki nauyin ginawa tare da rufa shaddan gida.
Wasu bayin Allah su biyu sun bamu taimakon block dari-dari su biyu.
Wani bawan Allah ya bamu taimakon block hamsin, Mun sayi block 100.
Wasu bayin Allah su biyu sun bamu taimakon block ashirin-ashirin. Jimlar block dinmu ya k**a 390.
Bayan Gina Katanga da toshe lunguna, yanzu haka mun sake samun taimako, mun fara gina mata wani daki a gefen wanda take ciki.

Har yanzu kofar taimako a bude take. Duk wanda ya taimaka da wanda yake da niyyar taimakawa, Ubangiji ya taimake mu baki daya.

Inna Llillahi Wa Inna Iaihi Raji'un 😭Wallahi kafin ta fara jinya ta kirani tace don Allah in faɗa mata yadda za tayi "De...
04/05/2023

Inna Llillahi Wa Inna Iaihi Raji'un 😭

Wallahi kafin ta fara jinya ta kirani tace don Allah in faɗa mata yadda za tayi "Deactivating Facebook account" ɗin ta , na tambaye ta lafiya tace min ita dai wallahi ta gaji da Facebook kuma yana ɗauke mata hankali ga wasu abubuwa, so take ta cigaba da Istigfari tana roƙon gafarar Allah maimakon zama Online ko da yaushe, nayi shiru sai na faɗa mata😢

Baiwar Allah ashe shirin komawa ga mahaliccin ta ne take, Allah Ubangiji ya jiƙanki da rahama Maryam alfarmar Annabi Muhammadu (SAW).

Sai mun zo 😭
© Sheikh Na Fati.

NEMAN TAIMAKO!Assalamu Alaikum 'yen uwa musulmi, wannan baiwar Allah mai suna Zuwaira Sa'idu, tana zaune ne a unguwar Al...
26/04/2023

NEMAN TAIMAKO!

Assalamu Alaikum 'yen uwa musulmi, wannan baiwar Allah mai suna Zuwaira Sa'idu, tana zaune ne a unguwar Alhaji
Ɗan Fulani dake cikin garin Kumo.
Mata ce ga Mallam Ɗan Audu mai shayi
wanda ya rasu ya barta da 'ya tilo, wacce ita take kula da rashin lafiyan Hawan jini da ya lalata sashen ƙafar mahaifiyar ta ta.
Damuna ya sako kai, kuma ɗaki guda da suke rayuwa ciki na faman lalacewa, ga kuma bayi (toilet) dake gidan ya rushe, matakin da za'a ke kallon mutum daga wajen gidan idan yana biyan bukata.

Waɗannan dalilan s**a sa muke neman 'yen uwa da su taimaka gwargwadon halin su domin jinya da kuma gyara musu muhalli.

Account name: Babayo Sulaiman
Account number: 0724790825
Bank name: Access Bank

Domin karin bayani, za'a iya tuntuɓan Waɗannan lambobin:

08168820609, 09019303562, 08067326470.

Sanarwa:
Muhammad Adamu Na Kumo.

C

TAIMAKON GAGGAWAWannan wata baiwar Allah ce mai suna  Goggoji Wacce take fama da ciwon tarin FUKA da ciwon ƘODA, mazauni...
16/04/2023

TAIMAKON GAGGAWA

Wannan wata baiwar Allah ce mai suna Goggoji Wacce take fama da ciwon tarin FUKA da ciwon ƘODA, mazauniya ce a anguwan tsamiya dake garin Kumo, Mun same ta tana kwance a cikin wannan yanayi, ganin haka yasa muka kaita ASIBITIN KUMO MEDICAL CLINIC.

Zuwa yanzu ana kan gwaje gwaje don sanin adadin yadda jinƴar zata ci, Abun takaici yanzu haka ko kuɗin gwajin ma babu a hannu.
Jama'a don Allah a taimaka albarkacin wannan wata mai albarka.

Ga lambar account tare da lambar waya na ƴar'uwar ta don gudumawa ko ƙarin bayani.

Aishatu Isah Isma'il
Bank: Access
Acc: 0085722748

Phone: 08148680670

"Yau shekara ɗaya kenan daidai da rasuwar abokinmu Dr. Aliyu Najib sak**akon haɗarin mota a jihar Gombe.Watanni uku baya...
14/04/2023

"Yau shekara ɗaya kenan daidai da rasuwar abokinmu Dr. Aliyu Najib sak**akon haɗarin mota a jihar Gombe.

Watanni uku bayan rasuwar Dr., Allah Ya wa mahaifiyar shi rasuwa. Ɗan shi Ashraf kuma Allah Ya jarrabe shi da cutar zuciya. Ashraf shekarun sa 3 da haihuwa jama'a.

Kamar yadda za ku gani a takardar da aka bamu a asibiti domin yi mishi aiki, ana neman sama da naira miliyan shida (₦6,525,000).

Tun shekarar da ta gabata da muke neman taimako, Allah Ya sa mun samu ₦903,000, saura ₦5,622,000.

Al'amarin ya fi ƙarfin mu jama'a! 😔

Albarkacin wannan wata mai albarka, don Allah muna neman kuma ku sa hannun jarinku, fisabilillahi, domin mu kula da wannan yaro.🙏

Don Allah ku taimaka ku yi sharing da duk wani naku da shi ma zai iya sanya na shi gudunmawar.🙏

Za a iya sanya gudunmawar ta account ɗin mahaifin k**ar haka:

Account Number: 3195690326
Account Name: NAJIB ALIYU ALIYU
Bank: First Bank.

Mun gode kwarai."

- Misbahu El-Hamza

12/04/2023

Makafi, Guragu
Kutare, Marayu

Allah ya baku yadda zaku yi a wannan wata mai albarkan.

10/04/2023

Alfarman wannan wata mai albarkan.

Dan Allah muke taimakawa marasa galihu.

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!Mutuwar wannan baiwar Allah ya girgiza duk wani mai imani.Allah ya gafarta mata
28/03/2023

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!

Mutuwar wannan baiwar Allah ya girgiza duk wani mai imani.

Allah ya gafarta mata

CIGIYAR MOTA TOYOTA COROLLA...Jiya da daddare wajejen karfe Goma na dare, Abokina Alhaji Abba dake zaune a unguwar Zawac...
22/03/2023

CIGIYAR MOTA TOYOTA COROLLA...

Jiya da daddare wajejen karfe Goma na dare, Abokina Alhaji Abba dake zaune a unguwar Zawaciki kusa da Dry Port ya fito daga gidansa cikin wannan motar tare da iyalinsa zasu je asibiti sak**akon rashin lafiyar da Dansa keyi, bayan fitowarsa sai wani mutum cikin siffar mutanen kirki ya daga masa hannu tare da sanar dashi cewa ya taka wani abu har ya makale a tayar motar, sai ya tsaya ya sauke gilashi tare da cewa da mutumin ya temaka ya cire masa abun dake jikin tayar k**ar gaske mutumin ya tsuguna kusa da tayar yana k**ar yana cirewa, sai yake sanar da Abba abun ba zai fita ba, yazo ya saka hannu su cire tare, yana fitowa daga motar sai mutumin ya zare wukake yayi ta kokarin kashe shi inda shi mutumin yayi sauri ya fada cikin motar ya danna Security, Alhaji Abba yayi ta ihun neman dauki wanda kafin mutane su fito barawon ya Umarci matar Abba aka ta fita daga motar ko ya kashe ta, ya turota waje sannan ya gudu da motar tare da yaron dake ciki...

Mutane sun fito an bi barawon a baya amma baa sameshi ba sak**akon an kai kusan minti 20 kafin a samu mutane kasancewar unguwa sabuwa ce, an samu yaron daga baya acan wajen gadar Fanshekara inda barawon ya jefar dashi ya gudu da motar....

Tun daren jiya aka sanar da hukumomi tare da cigaba da bincike...

JAMA'A idan Allah yasa anga wannan motar Toyota Corolla mai Lamba DTF 013AM a sanar da hukumomi dake kusa, ko a sanar dani tanan shafin....

Lambar Motar DTF 013AM

Innalillahi wainna ilahi rajiun 😭Wannan wata jaririya ce da aka samu acikin unguwarmu 😭💔Ya AllahYa Allah Ya Allah 🤲😭Inna...
17/03/2023

Innalillahi wainna ilahi rajiun 😭
Wannan wata jaririya ce da aka samu acikin unguwarmu 😭💔
Ya Allah
Ya Allah
Ya Allah 🤲😭

Innalillahi wainna ilahi rajiun 😭😭😭

Address

Gombe

Telephone

+2349019303562

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Entrepreneurship for people with special needs posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share