MUKU Area youth development association

MUKU Area youth development association Munbude wanan shafine domin wayar dakan matasan yan yankinmu

15/06/2025

Har kullum mai tallah shike da riba
Ba laifi bane idan ka tallah ta hajar ka domin Sai kayi hakan ne wasu zasu gani su San mahimmancin abin tallar ka

04/04/2025

GARKI DA BABURA WA YAKAMATA MU ZAƁA

Yakamata jam'iyyun siyasar dake kananan hukumomin babura da garki su nuna mana yan takarkarun da zamu zaba domin mu tantance wa kanmu wa yakamata muzaba gudun karmu sake yin zaben tumun dare kamar dai yanda mukayi a wasu kujerun.

Kamar dai wacan na arewa da gari wanda yake wakiltarma a kantin tsofaffi wanda halin yanzu dayawan wasun mu basu ma san sunan sa ba bare kuma ayi batun wani abin kirki da ya aikata a gida Mazaɓar sa ba kokuma a shago can inda ake kai bukatar ahali,to a yanzu dai mutane suna ta Nadamar akensan wancan shago dayaje yayi zaman sa ba saƙo ba dan aike, wasu ma nacewa gwara wancan na kudu dagari bakin kogi da muka saki abaya mukace sai wannan din. Abdullahi Ajura

Haka shima wacan na yamma da kauyen mu wanda muka aikeshi domin yaje shagon da ake. kirkira da kuma kafa doka domin ya tsaya mana idan yaga za a saka mana dokar da zata cutar damu kokuma idan yaga abin da muke da bukata ya gabatarwa mutanen shagonsu su amince yazo mana da abin, to amma yanzu shima shekaru biyu kenan ba doka babu kuma dan abin hasafi wanda al'umma zasu dan amfana dashi, kaga shima yazama zaben tumun dare kenan. Abdullahi Muazu Ajura

Wanda mudai yanzu a garki ma iya cewa lamba daya shine kawai wanda wasu al'umma suke amfana da salon jagorancinsa muna yabamasa bisa kokarin dayake duk da dai dan adam tara yake shima wasu zasu ga baya kyauta musu amma dai 70% yana bakin kokarin sa kamar yanda muke gani duk da cewar shima akwai bayanai da zamu zo dasu nangaba akansa

Kusaurarin zuwan rubuta nagaba akan wannan magana ta GARKI DA BABURA WA YAKAMATA MUZABA akwai cigaba .

Abdullahi Muazu Ajura.

02/04/2025

Assalamu alaikum barka da zuwa wannan shafi mai suna MUKU AREA YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION
Kuka sannu ce da mu domin samun inganta tun bayanai daga al'umma zuwa masu mulki daga masu mulki zuwa ga al'umma

Address

Ajura Town Muku Ward
Garki

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MUKU Area youth development association posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share