Imam Malik Charity Foundation Gololo

Imam Malik Charity Foundation Gololo A charitable organizations that touches the lives of the orphans, vulnerable and the less previlledge

Mun fara sayar da form na NURSERY AND PRIMARY SECTION karkashin Makarantar mu ta Imamu Malik College Gololo
07/05/2026

Mun fara sayar da form na NURSERY AND PRIMARY SECTION karkashin Makarantar mu ta Imamu Malik College Gololo

11/12/2025
We begin by extending our gratitude to Allah (SWT), who has taken control of this matter concerning His servant, Habiba ...
21/09/2025

We begin by extending our gratitude to Allah (SWT), who has taken control of this matter concerning His servant, Habiba Adamu, and destined her to face this trial.

As we previously informed our brothers and sisters, this servant of Allah has been battling a leg condition resulting from burns she sustained back in 2018. Although the burn initially healed, the wound later returned and worsened, eventually leading to cancer developing in one of her legs, which ultimately had to be amputated at the Teaching Hospital in Azare.

Before reaching this stage, we had sought support for her under the umbrella of our foundation. Following the doctor's bill of ₦850,000 for the surgery and medications, the community of believers contributed about ₦391,000. With that, we were able to make an advance payment, and the surgery was successfully carried out. However, we are still in need of approximately ₦462,000 to complete her treatment. Therefore, we continue to appeal for support from the general public — from anyone whom Allah has blessed with the means.

On behalf of this foundation, we express our heartfelt gratitude to the following individuals for their critical roles in saving the life of this servant of Allah: Alhaji Madaki Ahmed Gololo (Chairman of Gamawa LGA), Alhaji Adamu Tanimu, Sarki Liman Gololo, Ghali Alhaji Bello, and all others who supported with their money, advice, and prayers.

We pray that Allah, the Almighty, intervenes in our affairs and grants healing to all our sick ones.

Muna farawa da miqa godiyar mu ga Allah SWT daya shiga cikin lamarin wannan baiwar tasa Mai suna Habiba Adamu ya kuma ka...
21/09/2025

Muna farawa da miqa godiyar mu ga Allah SWT daya shiga cikin lamarin wannan baiwar tasa Mai suna Habiba Adamu ya kuma kadarta mata wannan lalurar.

Kamar yadda muka sanar da yan uwa wannan baiwar Allah ta sha fama da ciwon kafa sakamakon ƙuna data samu tun shekarar 2018, bayan warkewar ƙunar daga baya kuma ciwo ya dawo har Cancer ta shiga cikin kafarta ɗaya kuma takai ga har an yanke ƙafar a Asibitin Koyarwa dake Azare.

Kafin zuwan mu wannan matsayin, kwanakin bayan mun nemawa wannan baiwar Allah taimako karkashin wannan foundation din namu wanda yanzu haka shi yake jinyarta bayan likita ya bamu bill din ₦850, 000 na aikinta da kuma magunguna, cikin haka Al'ummar Allah sun taimaka mana da kuɗi kimanin ₦391, 000 wanda da wannan kudin muka samu damar biyan Advance har aka mata wannan aikin har yanzu haka muna neman kimanin kudin da yakai ₦462,000 don kammala wannan jinyarta ta. Da wannan muke cigaba da nema mata taimako a wajen al'umma duk wanda Allah ya h**e masa.

A madadin wannan foundation din muna miqa godiyar mu ta musamman ga wadannan bayin Allah saboda taka muhimmiyar rawa da s**ayi wajen ceto rayuwar baiwar Allah nan, Alhaji Madaki Ahmed Gololo (Chairman Gamawa LGA), Alhaji Adamu Tanimu, Sarki Liman Gololo, Ghali Alhaji Bello dama dukkan sauran bayin Allah da s**a taimaka da kudaden su, da shawarwarin su da kuma Addu'o'in su.

Allah Ubangiji muke roqo ya shiga lamarin mu ya kuma bawa marasa lafiyar mu afuwa.

DANGANE DA TAIMAKON HABIBA ADAMU MAIKOFIƘUDIN AIKIN DA AKE NEMA = ₦853, 900KUDIN DA AKASAMU = ₦269,400RAGOWAR KUDI DA YA...
17/09/2025

DANGANE DA TAIMAKON HABIBA ADAMU MAIKOFI

ƘUDIN AIKIN DA AKE NEMA = ₦853, 900
KUDIN DA AKASAMU = ₦269,400
RAGOWAR KUDI DA YA RAGE = ₦584, 500

ACCOUNT NUMBER: 0511067825
BANK: ALTERNATIVE BANK
ACCT NAME: IMAMU MALIK CHARITY FOUNDATION GOLOLO

Assalamu AlaikumYan uwa wannan foundation din namu mai Albarka yana nemawa wannan Baiwar Allah taimako mai suna Habiba A...
16/09/2025

Assalamu Alaikum

Yan uwa wannan foundation din namu mai Albarka yana nemawa wannan Baiwar Allah taimako mai suna Habiba Adamu Maikofi dake unguwar Makwalla a Gololo wanda yanzu hake take Teaching Hospital Azare.

Wannan yarinya mai kimanin Shekaru 20 ta samu wannan lalura ta ƙuna shekarun baya, bayan ta samu sauqi daga baya kuma ciwon ya dawo har Cancer ta shiga.

A matakin farko foundation ta kaita asibitin Azare wanda da farko an nuna mana yanke ƙafar za'ayi kuma Alhamdulillah a wancan lokacin munje wajen Chairman Hon Madaki Gololo mun faɗa masa inda ya bamu gudummawar ₦300, 000 sannan kuma wani bawan Allah ya taimaka mana da ₦100, 000

A Yanzu haka daga wancan lokacin zuwa yanzu sun kai Sati 5 a Asibitin Koyarwa na Azare ana gwaje-gwaje, da su karin jini, da magunguna da dressing da akeyi wannan foundation din mun kashe kusan ₦500, 000.

Bayan haka yanzu haka Likita ya bada bill din ₦850, 000 kuɗin aikin da za'a mata a sawayenta guda biyu gobe 16/09/2025. Wanda basu amince zasu mata aiki gobe ba sai da muka nemo bashin advance din kuɗin aikin da magungunan da za'a tanada don gudanar da aikin daya kai ₦340, 000 mun tura musu

Da wannan muke nema mata taimako a gurin ɗai-ɗai kun jama'a na abinda Allah ya h**e, sannan kuma don Allah idan da wanda zai iya taimakawa sai a sanar masa.

Daga karshe muna Addu'a Allah yasa a mata aiki lfy, Bayin Allah da suke bamu gudummawa Allah ya saka musu da Alkairi.

Wannan shine account din Foundation don taimakawa.

Account Number: 0511067825
Bank Name: ALTERNATIVE BANK
Account Name: IMAMU MALIK CHARITY FOUNDATION GOLOLO

Imamu Malik Charity Foundation yayin data kaiwa wani maraya dauki a wannan gari namu wanda yake fama da wannan ciwon kaf...
04/09/2025

Imamu Malik Charity Foundation yayin data kaiwa wani maraya dauki a wannan gari namu wanda yake fama da wannan ciwon kafar kwana da kwanaki.

Cikin taimakon ubangiji wannan foundation din ta hada shi da medical team dinta kuma tadau nauyin masa daily dressing har zuwa lokacin da zai samu lafiya in sha Allahu.

Yan uwa wannan foundation din yana gudanar da wannan aikin ne ta hanyar taimako da gudummawarku. Jama'a kar mu gajiya wajen bada taimakon ku ta account din foundation din

Account Number: 0511067825
Bank : Alternative Bank
Account Name: Imamu Malik charity foundation Gololo

AlhamdulillahCikin nasarar da Allah ya bamu a yau mun samu rahoton wannan almajirin daga Makarantar Malam Aminu a bakin ...
26/08/2025

Alhamdulillah
Cikin nasarar da Allah ya bamu a yau mun samu rahoton wannan almajirin daga Makarantar Malam Aminu a bakin Rafin Tano. Almajirin ya kasance yana yawon bara kwana da kwanaki da wannan kurajen a kansa.

A yau wannan foundation din namu ya dauki wannan yaron zuwa asibiti kuma anyi nasarar yi masa aiki sannan foundation ta dauki yaron ta kaishi wajen malaminsa tare kuma da masa gargadi akan kula da Almajirin.

Jama'a wannan yana daga cikin ayyukan da wannan foundation din take gudanarwa da irin taimakon da kuke tura mana. Kuma har kullum kar mu gajiya wajen bada gudummawarmu a irin wannan alkhairin.

Account Number : 0511067825
Account Namae : Imamu Malik Charity Foundation Gololo
Bank : ALTERNATIVE BANK

Address

Unguwar Malam Idi Dangombe Jakusko-Road Gololo
Gamawa
752106

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam Malik Charity Foundation Gololo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share