13/08/2026
ƘUNGIYAR FUNTUA CONSULTATIVE FORUM TA ZIYARCI SABON KAMISHINAN ’YAN SANDA NA JIHAR KATSINA, TA GABATAR DA SHAWARWARI KAN INGANTA TSARO A FUNTUA
Funtua, Jihar Katsina | Alhamis, 13 ga Agusta, 2026
Ƙungiyar Funtua Consultative Forum (FCF) ta kai ziyarar girmamawa zuwa ga sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, a hedikwatar rundunar ’yan sandan jihar Katsina.
Shugaban kungiyar Funtua Consultative Forum, Dr. Zaharaddeen Idris, ne ya jagoranci tawagar ƙungiyar, wadda ta kai wannan ziyara domin maraba da sabon Kwamishinan, nuna godiya da yaba wa ƙoƙarin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro, tare da gabatar da wasu muhimman buƙatu da shawarwari da s**a shafi tsaron al’ummar Funtua.
A cikin jawabinsa, Shugaban FCF ya nuna godiya ga Kwamishinan bisa ba ƙungiyar damar ganawa da shi duk da yawan ayyukan da ke gabansa. Ya kuma yi masa maraba da zuwa Jihar Katsina, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ba shi hikima, ƙarfin hali, basira da kariya wajen gudanar da aikinsa.
Dr. Zaharaddeen Idris ya kuma yaba da ƙoƙarin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina a ci gaba da yaƙi da ’yan bindiga, ’yan daba da sauran nau’o’in aikata laifuka, yana mai bayyana cewa nasarorin da aka samu zuwa yanzu na daga cikin abubuwan da ke nuna muhimmancin ingantaccen shugabanci da jajircewa wajen tabbatar da tsaro.
BUƘATUN DA FCF TA GABATAR
A yayin ziyarar, ƙungiyar ta gabatar da wasu muhimman shawarwari domin ƙara inganta tsaro da sauƙaƙa wa al’umma samun ayyukan ’yan sanda a Funtua.
1. Mayar da Asibitin ’Yan Sanda da ke CPS Funtua zuwa police compound
FCF ta roƙi a duba yiwuwar mayar da asibitin ’yan sanda da ke CPS Funtua zuwa cikin harabar ’yan sanda da ke Funtua.
Ƙungiyar ta bayyana cewa saboda yanayin tsaro da ƙuntatawar shiga wurin da asibitin yake a yanzu, jama’a da dama ba sa samun damar yin amfani da shi yadda ya kamata. Saboda haka, mayar da shi zuwa wani wuri da ya fi sauƙin shiga zai taimaka wajen farfaɗo da ayyukan asibitin tare da bai wa jami’an ’yan sanda da sauran al’umma damar cin moriyarsa.
2. Kafa Ƙarin Rukunin ’Yan Sanda Biyu
FCF ta nemi a kafa ƙarin Rukunin ’Yan Sanda guda biyu (2) a yankunan Bagari da Maska na ƙaramar hukumar Funtua.
Ƙungiyar ta bayyana cewa waɗannan yankuna suna da yawan al’umma kuma suna da nisa daga wasu daga cikin rukunin ’yan sanda da ake da su a yanzu, wanda kan iya jinkirta kai ɗauki lokacin da aka samu matsalar tsaro ko wani lamari na gaggawa.
3. Ƙara Yawan Ofisoshin ’Yan Sanda
Haka kuma, FCF ta nemi a kafa ƙarin ofisoshin ’yan sanda a wasu muhimman wurare da ake ganin suna buƙatar ƙarin kulawar tsaro a cikin garin Funtua.
Daga cikin wuraren da aka ambata akwai Sabuwar-Abuja, Unguwar-Shanu, Maigamji, Yartafki, Unguwar-Mata, Unguwar-Dahiru da yankin GRA.
Ƙungiyar ta bayyana cewa nisan wasu daga cikin waɗannan wurare da rukunin ’yan sanda da ake da su a yanzu na iya shafar saurin kai ɗauki a lokacin da aka samu wani lamari na gaggawa.
4. Ƙara Yawan Jami’ai da Motocin Sintiri
FCF ta kuma roƙi Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina da ta ƙara yawan jami’an ’yan sanda da motocin sintiri a Funtua.
A cewar ƙungiyar, ƙarin jami’ai da motocin sintiri za su taimaka matuƙa wajen inganta saurin kai ɗauki, sintiri da kuma samar da cikakken tsaro a sassa daban-daban na garin.
FCF TA JADDADA HAƊIN KAN AL’UMMA DA JAMI’AN TSARO
Funtua Consultative Forum ta jaddada cewa waɗannan shawarwari an gabatar da su ne cikin kyakkyawar niyya da manufar haɗin gwiwa tsakanin al’umma da hukumomin tsaro, domin samar da ingantaccen tsarin tsaro mai ɗorewa.
Ƙungiyar ta sake tabbatar da shirinta na ci gaba da tallafa wa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaron rayuka da dukiyoyi, da kuma ci gaban al’umma.
FCF ta bayyana ƙwarin gwiwarta ga sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ba shi nasara a lokacin da yake jagorantar rundunar jihar.
Ƙungiyar ta kuma yi fatan sabon shugabancin zai kawo ƙarin ci gaba wajen inganta tsaro, ƙarfafa tsarin hulɗar ’yan sanda da al’umma, da ƙara dawo da amincewar jama’a ga hukumomin tsaro.
Funtua Consultative Forum ta sake jaddada cewa tana nan daram kan manufofinta na inganta ilimi, lafiya, tsaro, ci gaban al’umma da wayar da kan jama’a, tare da kasancewa wata gada ta tattaunawa tsakanin al’umma da hukumomin gwamnati.
FCF na yaba wa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya bisa sadaukarwa da ƙoƙarin da take yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Tare da haɗin gwiwar al’umma da jami’an tsaro, za mu iya gina Funtua mai zaman lafiya da ingantaccen tsaro.
Sa hannu:
Aminu Muhammad Yahuza
Jami’in Hulɗa da Jama’a (PRO)
Funtua Consultative Forum (FCF)