29/08/2026
Alssalamu alaikum warahmatullah, yan'uwana masu sana'ar dinki kuma yan kungiyar telolin kasuwar Funtua wadda mukasani da suna {FUNTUA CENTRAL MARKET TAILORING ASSOCIATION}, inayiwa dukkan membobin mu fatan alheri, kuma Ina mai jinjina da yabo agareku Baki daya, Alan irin kokarin ku da juriya wajen gani cigaban aikace-akacen wanna kungiya. Kuma da gaggarimin hadin Kai da goyon baya da kuke bayarwa, hakika hakan abin alfaharine da godiya matuka.
Bayan daukan wani dogon lokaci batare da yin zaman meeting ba adalilan sauyin lamura na matsi da tabarbarewar tattalin arziki, da gurguncewar harkokin kasuwanci, ya janyo tsaiko na ayyukan kungiyar, amma duk da irin wanna yanayi da muka tsinci kammu, yan'kumgiyar basuyi kasa a gyiwaba wajen dagewa Akan wasu al'amuran da zasu kawo cigaban yan'kumgiyar da sana'ar su. A bayan Nan ma kungiyar telolin kasuwar Funtua da kewayen tayi yunkurin farfado da kwamitin marayu na kungiyar, don cigaban da tallafawa marayu kamar yadda ta sabayi abaya Kuma kwamitin marayun yasami sauye-sauye tahanyar Samar masa da asusun ajiya domin fadada January Samar da kudaden da ake bukata don taimakon marayun, kamar yadda akasabayi.
Kuma tuni an kaddamar da Neman taimakon, kuma Muna da ran yan'kumgiyar bazasuyi kasa agyiwaba wajen bayar da gudunmawar su. Haka Kuma kwamitin na sanarda duk Wanda Allah ya h**e masa wadata da ya taimaka, basai telolin kadaiba, hidimace ta kowa-dakowa, acikin kasuwar da wajen kasuwar Funtua, ko wace irin sana'a kakeyi, yadace da kataimaka a wanna aikin Mai tarin lada awurin ubangiji
Muna mika sako ga dukkan membobin da su isar da sakon izuwa yan'uwan su na kusa da nesa domin taimakawa.
Kwamitin marayun yasami sauye-sauye tahanyar Samar masa da karin membobi kamar haka:-
-Yusuf Iliyasu chairman
Nasir Usman
-Usman Ibrahim
-Abubakar sani Dan baba. Muna fatan yan'kwamitin marayun zasu dage wajen ganin ansami nasara wannan aikin. Allah ya shiga cikin al'amuran mu yasa albarka acikin sana'ar mu ya kawo Mana gaggarimin cigaban acikinta, yabamu _lafiya_ da zaman lafiya. Ga lambar asusun nan kamar haka:-