09/08/2026
NAFS NATIONAL BODY TA HALARCI BUKIN YAYE DALIBAN ABEE HURAIRA ACADEMY, BAGARI
Kungiyar National Association of Funtua Students (NAFS) National Body ta halarci bikin yaye dalibai na Abee Huraira Academy, Bagari, wanda ya kasance wani muhimmin lokaci na murnar kammala karatun daliban makarantar.
Taron ya samu halartar Mai Girma Shugaban Majalisar Dattawa (Senate President) na NAFS National Body, tare da Auditor General, Comrd. Ismail Mansur Funtua; Organizing Secretary, Comrd. Musa Musa Maigidaje; Welfare Director, Comrd. Aminatu Musa; P.A. ga Senate President, Comrd. Habiba Isah, da sauran manyan baki da wakilan kungiyar.
A cikin jawabinsa na maraba, Shugaban Makarantar Abee Huraira Academy, Malam Kamal Ismail, ya bayyana godiyarsa ga dukkan bakin da s**a amsa gayyata tare da halartar wannan babban biki.
Ya kuma yaba matuka da kokarin malamai da ma'aikatan makarantar bisa irin gudunmawar da s**a bayar da kuma yadda s**a tsaya tsayin daka wajen ganin makarantar ta samu ci gaba tun daga farko har zuwa wannan lokaci.
Malam Kamal ya kuma yaba da shugabancin NAFS National Body karkashin jagorancin Comrd. Ahmad Abdulkarim, wanda bai samu halartar taron ba saboda wasu dalilai na musamman.
Haka kuma, ya yi addu'a ga mahaifin Shugaban NAFS, inda ya roki Allah Ya ba shi lafiya, Ya kuma ba shi cikakkiyar lafiya cikin gaggawa.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa (Senate President) na NAFS National Body ya yaba da kokarin shugabancin makarantar da malamai wajen koyarwa da tarbiyyar dalibai.
Ya kuma yaba da irin gudunmawar da dukkan tawagar NAFS National Body ke bayarwa wajen tallafawa da kare muradun daliban Funtua a makarantu da manyan makarantu daban-daban.
Ya jaddada muhimmancin ilimi, jajircewa, ladabi da aiki tukuru wajen gina kyakkyawar makoma ga matasa.
A nasa jawabin, Auditor General, Comrd. Ismail Mansur Funtua, ya taya makarantar murnar wannan gagarumin biki.
Shi kuwa Organizing Secretary, Comrd. Musa Musa Maigidaje, ya yaba da yadda aka tsara Taron.